Tsuntsayen da ke hallaka kansu tare

Hakkin mallakar hoto Andy Mason

Za ka ga 'ya'yan chakwaikwaiwa suna fadawa ruwa da kansu su mutu a gungun goma ko sama da haka. Shin suna kashe kansu ne, ko kuma me?

Melissa Hogenboom ta bincika

Ruwa ba sa fadawa ruwa su mutu, amma dai idan rana ta baci su kan mutu a ciki.

Idan dan tsuntsu ya fada ruwa mai zurfi kuma fukafukinsa ya jige, da wuya ya iya fitowa.

A sama da shekara dari da ta gabata an sanya wa tsuntsaye sama da 800,000 zoben bin diddiginsu, na alamar sanin inda suke.

Daga cikinsu an gano cewa guda 2,901 ne kawai ruwa ya yi sanadiyyar mutuwarsu, wato kasa da kashi daya bisa dari kenan.

Bayan da aka samu rahotannin da ke cewa tarin 'ya'yan chakwaikwaiwa suna fadawa ruwa da kansu su mutu, fiye da sau daya, wata likitar dabbobi Becki Lawson, ta kungiyar masana harkokin dabbobin dawa ta Landan, sai ta yanke shawar gudanar da bincike kan lamarin.

Hakkin mallakar hoto Josie Latus

Bisa dogaro ga rahoton jama'a Lawson da abokan aikinta sun gano irin wannan lamari har guda 12, inda aka samu tarin 'ya'yan chakwaikwaiwar sun hallaka a ruwa a Ingila da Wales, a cikin shekara 20.

Ta ce, ''wadannan duka sun hada da inda mutane suke samun gawarwakin tsuntsayen a ruwan lambunsu, yawanci a tafkin lambu da tafkin wanka na gida da rijiya har ma da ruwan bokiti.

Dukkanin tsuntsayen dai kanana ne kuma sun mutu ne 'yan watanni bayan kyankyasarsu a watan Mayu ko Yuni.

A dukkanin wadannan mace-macen guda biyu ne kawai aka samu tarin tsuntsayen goma ko sama da haka sun fada ruwan tare sun mutu.

Yawanci idan tarin tsuntsaye suka mutu a lokaci daya, ana danganta hakan da wata cuta ko wata guba.

Amma kuma su dukkanin wadannan tsuntsayen suna cikin koshin lafiyarsu ne abin ya faru.

Saboda haka dole ne akwai abin da ya haddasa hakan. Lawson tana tunanin ko ita chakwaikwaiwa tana da wata matsala ko rauni da ke sa ruwa ya ci ta.

Tana mamakin yadda tarin tsuntsayen za su bi junansu gaba daya su fada ruwa.

Hakkin mallakar hoto Christine M Matthews
Image caption Idan karamar chakwaikwaiwa ta fada ruwa sai sauran su bi ta su fada

Ita chakwaikwaiwa a kodayaushe tana tare ni wuri daya ba sa rarrabuwa.

Ta yi suna kan yadda duk yawansu (dubbai) suke tashi tare da shawagi iri daya, kamar yadda gwanayen rawa suke rausayawa tare a lokaci daya.

Wadannan da suka mutun a ruwa tare za a iya cewa ba su kanana ne ba su mallaki hankalinsu sosai, saboda haka wannan zai iya zama dalilin mutuwar tasu.

Lawson ta ce, ''ita chakwaikwaiwa tsuntsuwa ce da ke komai tare da 'yan uwanta, tashi ne ko sahan ruwa ne ko wanka duk gaba daya suke yi.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Tarin chakwaikwaiwa na shawagi

Wannan zai iya kasancewa shi ne dalilin da ya sa idan za su fada ruwa sai su fada gaba daya.''

Su kanana ba shakka ba su da wata kwarewa. Saboda haka idan daya ta shiga ruwan da ke da hadari, a rashin sani sai sauran su bi ta.

Domin tantancewa ko lalle hakan gaskiya ne, masu binciken sun kwatanta rahotannin mutuwa a ruwan na chakwaikwaiwar da kuma wata tsuntsuwar (blackbird) mai kama da jinsinta.

Hakkin mallakar hoto Jill Pakenham

Ayarin masanan ya gano cewa, ita chakwaikwaiwa ta fi daya tsuntsuwar fadawa ruwa.

Daya daga cikin wadanda suka hada rahoton, Rob Robinson, ya ce, '' babban bambancin shi ne ita chakwaikwaiwa yawancin lokaci tana tafiya ne tare da juna, inda su 'yan kananan suke yawo a daji ko kauye kamar dai 'yan matasa.''

Robinson ya kara da cewa, a yayin da suka je wata korama shan ruwa, sai su dukansu su nufi ruwan a lokaci daya suna fadawa junansu.

''Muna ganin yanayin yadda suke tashi tare ne ke jefa su cikin wannan hadari.''

Yayin da ake ganin fadawarsu ruwan kamar wani hadari ne, to amma abin da ke haddasa fadawar ya gagara ganowa.

Duk da haka wannan lamari ya kasance jifa-jifa yake faruwa, saboda haka Lawson ta ce, ba dalilin da zai sa mutane su daina zuba wa tsuntsayensu ruwa a lambunsu.

''Abin da muke fada kawai shi ne, a lokacin watan Mayu da na Yuni, zai fi dacewa mutane su rika yin 'yar wata gangara ko wani abu da zai iya taimaka wa tsuntsayen su tsira daga ruwan idan sun fada.'' In ji Lawson.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Tarin chakwaikwaiwa

Duk da cewa chakwaikwaiwa na daya daga cikin tsuntsayen da mutane suka fi kiwo a lambunsu, yawanta ya ragu da kashi 79 cikin dari a shekaru 25 da suka wuce, kamar yadda hukuma ta bayyana.

Yanzu dai kungiyar masu kare tsuntsaye ta Biritaniya ta sanya jinsin tsuntsun a cikin wadanda suke fuskantar barazanar karewa.

Wannan lamari mai daure kai na mutuwar tsuntsayen a ruwa bai yi yawan da zai sa a ce jinsin tsuntsun na fuskantar karin barazana ba.

Amma duk da haka masanan na kira ga jama'a su aika musu rahoto duk inda suka ga hakan ta sake faruwa a Biritaniya.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Birds are drowning themselves and we don't know why