Ka san illar yawan tsafta ?

Hakkin mallakar hoto Getty

Mukan dade a bandaki muna wanka da sauya tufafi kullum kuma muna wanke hannuwanmu akai-akai duk da sunan tsafta. Ko hakan yana mana illa ne fiye da amfani.

Katia Moskvitch ta yi nazari

Yaya kake tafiyar da tsarinka? Kana wanka ne kullum ko kuma kana tsallake wasu ranakun? Kana sauya zanin gadonka, ko kuma sai sun fara wari? Yaya kuma tawul dinka: Kana sauya sabo ne ko da yaushe misali duk ranar Asabar, ko kuma kana bari ne har sai ya fara yagewa?

Muna zamani ne na tsafta a yanzu. Sabulun da muke amfani da shi ma yau ya zama mai kashe kwayoyin cuta.

Kayanmu na goge-gogen gida ana ce mana masu kashe kwayoyin cuta ne kashi 99 da digo tara bisa dari.

Eh! Gaskiya ne kwayoyin cuta suna da illa, ba wata jayayya wannan haka yake.

To amma kuma yayin da duk muke wannan kokarin tsafta, wasu masana kimiyya cewa suke yawan tsaftar ma na da illa, domin hakan ya kan iya taimaka wa cutar matsalar numfashi ta asma (asthma) da ta kan-jiki su kama mutum.

To ina mafita a irin wannan yanayi na tsaka-mai-wuya, akwai yadda za mu iya zama cikin tsafta tare da kuma rayuwa da kananan kwayoyin halittu masu sanya cuta tare da mu?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ba ko'ina ya kamata mu rika wankewa a jikinmu kamar yadda muke wanke hannunmu ba

Tun a kusan karshen karni na 19 kari kuma da abin da wani likita na Jamus Robert Koch, ya gano muka san cewa wasu kwayoyin baktiriya (bacteria) suna haddasa wasu cutuka.

Tun daga wannan lokacin muka kara daukar matakan kula da lafiyarmu ta hanyar tsaftar jikinmu da ta muhalli da kuma ta abubuwan ci da shanmu.

To amma duk da haka ba dukkanin kwayoyin halittun ba ne suke da illa. Gaskiya ne cewa, akwai 'yan mitsi-mitsin halittu na bakteriya wadanda ke haddasa cutuka masu hadarin gaske, amma, wasunsu suna da amfani sosai ga lafiyarmu.

Wasu sukan samar da sinadaran gina jiki (vitamins) a cikinmu, wasu sukan yi yabe a jikin fatarmu domin kare mu daga wasu kwayoyin halittun masu cutarwa, sannan kuma suna taimaka mana wajen narkar da abinci a cikinmu yadda jiki zai yi amfani da shi.

A wajen jikinmu kuwa sukan taimaka wajen rubar da abubuwan da aka zubar, wanda hakan kuma ke samar da kusan rabin iskar duniya da muke shaka, tare kuma ta daidaita yawan iskar naiturojin (nitrogen) a cikin iska, wanda hakan ke daidaita yanayin iska da sauran sinadarai a duniya ta yadda halittu za su zauna lafiya su rayu a duniya, kamar yadda yake.

A yau masana kimiyya da yawa na cewa mutane suna tsafta da sosai fiye da yadda ya kamata su yi.

A shekarar 1989 ne, wani kwararren masanin harkar lafiyar jama'a dan Biritaniya, David Strachan ya bayyana cewa, gamuwa da kwayoyin cuta a lokacin da mutum yake dan karami, na samar da garkuwar jiki da kuma ta kanjiki ga mutum idan ya girma, (Hygiene hypothesis).

Kanjiki dai shi ne yadda garkuwar jikinmu za ta ji cewa wani abu maras cutarwa babbar barazana ce ga lafiyar jikin.

Dorothy Matthew, masaniyar ilimin halittu a kwalejin Russell Sage da ke Troy a New York, ta ce, jikinmu zai iya daukar wani mataki na yakar kananan halittu masu amfani, saboda garkuwar jikinmu ta manta yadda za ta rayu tare da su.

A bisa wannan dalili ne ya kamata mu fahimci yadda 'yan kananan halittu da ke cikin jikinmu da wadanda suke kan jikin za su iya taimakonmu.

''Abu ne mai muhimmanci mu yada wadannan kwayoyin halitta 'yan mitsi-mitsi marassa cutarwa a cikinmu da fatarmu da sauran sassan jikinmu kuma muna da bukatar mu'amulla da irin wadannan halittu da ke muhallinmu,'' in ji Graham Rook, masanin harkar lafiyar jama'a a jami'ar Landan.

Cire kwayoyin halittu masu cuta

Dauki misalin irin robar tsotson nan ta jarirai da ta fadi kasa. Ya fi dacewa uwar jariri ta dauke ta ta wanke ta sake ba shi maimakon ta jefar da ita, ta dauko wata sabuwa mai tsafta ta ba jaririn, in ji likitan, domin kamar yadda bincike ya nuna hakan zai sa jikinsa ya yi saurin samar da kwayoyin halittar garkuwar jikinsa tare kuma da rage kanjiki.

Wani zai iya bayyana wannan da hanya ta matakin sabawa jikin jariri da kwayoyin cuta, wanda ya fara da abinci.

Likitan ya ce, ''ka ci abinci mai hade-hade iri-iri, musamman mai kayan gona.''

Sannan ya ce ya fi kyau ka motsa jiki a fili maimakon a cikin daki ko gidan motsa jiki.

Kuma yadda za mu iya daukar karnuka cewa suna da kazanta ko datti, ta da hakan suna taimaka mana wajen kara samun kwayoyin halittun kwarin da muke bukata na gina garkuwar jikinmu da kuma rage kanjiki.

Ta wata hanyar ita garkuwar jiki kamar manomi ta ke. Tana tababbatar da cewa jikinmu ya samu kananan halittun da ke da amfani ga bunkasar jikinmu, aikinsa ciki da waje, har da kwakwalwa da kuma kawar da tarin halittun (ciyayi) da ke cutarwa.

Wannan shi ya sa idan ya kasance jiki ba ya dauke da wadannan kwayoyin halitta iri-daban-daban sai ka ga wannan jikin yana gamuwa da wasu cutuka masu yawa iri-iri.

To amma wannan ba yana nufin rashin wata 'yar kwayar halittar a jikin mutum na nufin zai kamu da wata cuta ba ne, domin babu wata sheda da ta tabbatar da hakan.

''Ko da ya ke za a iya samun hakan nan gaba,'' in ji Rook, ''amma matsalar tana da sarkakiya ta fannoni biyu, na kwarewa da kuma kididdiga.''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasu masana kimiyya sun yi amanna rashin haduwarmu da kwayoyin halitta na bakteriya ne sanadin karuwar cutar asma da kanjiki

Wasu sun yarda. ''Ana danganta wadannan kananan kwayoyin halittu ga garkuwar jiki da da cutar galhanga da kanjiki da yanayin da mutum kan shiga da kuma bunkasar cibiyar tafiyar da sadarwa da motsin jikinmu baki daya (central nervous system),'' in ji Mary Ruebush, ta Becker Professional Education.

Wannan mataki na sabawa jiki da kwayoyin halitta na cuta ya fara ne tun daga lokacin da aka haife mu.

A nan, yaran da aka haifa ta ka'ida (farji) matsalar da suke da ita ta kanjiki kadan ce, idan aka kwatanta da ta wadanda aka yi tiyata ( carsarean ko cs)aka fitar da su, ana ganin saboda haduwar da yaran suka fara yi da 'yan kananan halittu da ke farjin. Kamar yadda masaniyar ta yi bayani.

Haduwar jikinmu da kananan halittu masu kyau tun muna 'yan kanana abu ne mai amfani sosai ga lafiyarmu kamar yadda Rook ya ce.

Misali, idan wadanna 'yan halittu suka shiga cikinmu tun muna 'yan kanana, sukan tayar da wasu kwayoyin halitta na garkuwar jikinmu su fara aiki tun daga lokacin, ta yadda idan muka girma, wadannan kwayoyin garkuwa ba za su wuce gona da iri ba a kan kananan halittun da za su gamu da su a cikin a lokacin ( har su je suna hallaka masu amfani).

Dakta Rook ya kira wadannan 'yan halittu da sunan tsoffin abokanmu. Wadanda muke kewar abokantaka da su, saboda tsananin tsaftar da muke yi yanzu ta sa ba ma haduwa da su kamar yadda kakanninmu suka yi.

Wannan kamar wani yanayi ne mai wuyar gaske ga mutanen suke son tafiyar da rayuwarsu cikin koshin lafiya.

Ta yaya za mu kauce wa kamuwa da cuta daga kwayoyin halitta na baktiriya masu cuta, a yayin da muke kokarin habaka marassa cutarwa a jikinmu?

Ba shakka Rook ba zai bayar da shawarar kauce wa yin abin ya zama wajibi ba, kamar wanke hannu.

Masana kimiyya suna daukar hannu mai dauda a matsayin hanyar da suke ganin muna yada cuta a tsakaninmu.

Maganar wanke tsaftace hannunka, ba ta tsaya ba ne kan tsawon lokacin da za ka dauka kana wankewar ba, magana ce ta yadda ka wanke shi da kyau.

Dole ne ka sanya sabulu da ruwa, ka murtsuka ko'ina kusan tsawon dakika 15 akalla, sannan ka dauraye da ruwa ka busar da hannuwan, in ji masana.

Cudawar da za ka yi da sabulu ta hana ne kwayoyin cutar ke rabuwa da fatar hannun, yayin da daurayewar ke raba su da hannun baki daya.

Amma ba dukkanin jikinmu ba ne ke bukatar wankewa sosai da sosai.

Yawan wanke jiki yana kawo cikas ga kananan halittun da suke sa jikinka ya zauna lafiya ta hanyar gogayya da takwarorinsu masu cutarwa, in ji Ruebush.

Ta ce, amfani da jikinmu a yanayi na amfani da magungunan kashe kwayoyin cuta, kamar hana kwakwalwa motsi ne (sakon da take samu na yin aiki).

Wanda idan haka ya sami kwakwalwar sai ta haukace, wannan shi ne kwatankwacin jikin mutumin da yake kokarin kare jikinsa daga dukkanin wani abu na muhallinsa, sai ya kasance ya gamu da karin kanjiki da raunin garkuwar jiki, masaniyar ta ce.

Dadewa kana wanka a kullum ba abu ne mai amfani ba domin, yana fitar da 'yan kananan halittu masu amfani daga jikin fatarmu.

Abin daza ka tabbatar ka yi akullum din shi ne ka wanke wurin farjinka, da duk inda kake zufa sosai, sanna kuma ta sauya duras da singiletinka (da rigar nono ga mata) kullum.

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Wasu daga cikin halittun bakteriya masu amfani suna kare mu daga mitsi-mitsin halittu masu cutarwa

A gida harabar gidan kuwa hanyar yaki da kananan halittu masu yada cuta kuwa, ba yawan shara ba ne, illa yin sharar daga lokaci zuwa lokaci.

Ba shara ko goge-goge sau daya a mako ba ne ke tabbatar da tsafta ba.

Abu ne da ya kamata a rika yi a rayuwarmu ta kullum, inda za mu rika la'akari da duk wuri da lokacin da ya wajaba mu tsaftace, in ji Sally Bloomfield ta makarantar koyon tsafta ta Landan ( London School of Hygiene and Tropical Medicine), kuma shugabar kungiyar masana kimiyyar tsaftar gida ta duniya.

Mu dauki misalin, irin dan allon katakon nan da mata suke amfani da shi wajen yanke-yanken ganye a wurin girkinsu.

Idan mace ta yanka ganyayyakinta , ba laifi ta ajiye katakon ba tare da ta wanke shi ba har sai ta sake amfani da shi a aikin girkin almuru sanna ta wanke shi.

To amma ba za ta yi haka ba idan kifi ko nama ta yayyanka a kan katakon, dole ne ki wanke shi da zarar kin gama aikin, tun da rana, ko kuma ki jefa rayuwar iyalinki cikin hadarin kamuwa da cuta.

Daman kuma ga shi an tabbatar da cewa kashi 70 cikin dari na kaji da sauran tsuntsaye da muke ci dauke suke da wata kwayar halitta ta baktiriya, wadda za ta iya gurbata abinci kuma tana iya hayayyafa a kan wannan dan katako cikin dan kankanin lokaci.

Hadarin kaya (tufafi) masu lema

Binciken asibiti ya nuna cewa zanin gado da tawul suna iya yada kananan kwayoyin halitta na cuta na bairus (virus) da sauran kwayoyin cutuka daban-daban, amma wannan ba yana nufin gidajenmu na cikin hadarin da za a kai ga samun gagarumar kwayar cutar da za ta zata iya buwayar masana ba ne a nan gaba.

Amma dai a sani cewa barin tawul da danshi ka iya zama matsala ga lafiyar mutum, wurin yada kwayoyin cuta daga kananan halittu.

''Ba wani bayani na kimiyya wanda zai iya fayyace mana lokacin da ya kamata mu rika sauya zanin gadonmu da tawul da sauransu,'' in ji Bloomfield, amma dai akwai cikakkun bayanai da ke nuna cewa za su iya kasancewa hadari a gida.

A don haka ne masaniyar ta bayar da shawarar sauya zannuwan gado da tawul kusan a duk sati, kuma ta yi gargadi sosai a kan mutum ya rika amfani da tawul din wani da sauran kayayyakin da mutum ya ke amfani da su na kashin kansa.

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Da zarar an yanka nama a kan katokon dakin girki a wanke katon da wuri

Kayayyakin (tufafi da sauran kayan tsumma) da ke da lema matattara ce ta kwayoyin halittu masu cutarwa, in ji Bloomfield.

Wannan ne ya sa dole a rika tabbatar da ana fitar da tufafi da sauran jikakkun kaya daga dakin girki da bandaki kuma a wanke su da ruwan zafi ko kuma da bilichi idan ruwan sanyi ne, ba tare da bata lokaci ba.

Idan kuma har ba za a iya wanke su ba a lokacin to a tabbatar an dauraye su da kyau bayan an yi amfani da su, sannan a shanya su, kamar yadda Bloomfield ta bayar da shawara.

Dan karamin tawul na hannu da ake goge kwanukan tangaran da shi, yana da hadarin yada kwayoyin cuta ga sauran kofuna da kwanukanku.

Ya wajaba a rika sauya kwanuka da kofunan da ake amfani da su, kusan a kullu, ma'ana idan an yi amfani da wadannan, sai a ajiye su a yi amfani da wasu sai kuma wani karon a sake amfani da wadancan.

Idan kuma aka zo maganar bandaki, ya kamata mutane su rika rufe bakin salga (ta tangaran wadda mai hade da famfo), bayan sun yi bahaya za su kunna fanfo ya tafi da ita (kashin).

Domin barin bakin salgar a bude na bayar da dama ga kwayoyin cutar da ke ciki su samu damar hayayyafa kuma su watsu.

Kayan bacci ma wata matattara ce da mutane ke ba da dama ga kwayoyin cuta su yadu.

Wani bincike ya nuna cewa mutane da yawa ba sa wanke kayan barcinsu sai sun ji sun fara tsami.

Masana suka ce kamata ya yi ka sauya su akalla sau daya a sati.

Gabadayan sakon da ake son yadawa a nan shi ne, ba wai ana son mutane su koma rayuwa ta tsananin kazanta ba ne, domin samun kwayoyin halitta na bakteriya masu amfani ba, abin da ake bukata shi ne mu sanya ido sosai hatta a wajen gidajenmu mu tabbatar mun kare su daga kwayoyin cuta.

Ilka Hanski masani kan ilimin halitttu a jami'ar Helsinki da ke Finland, cewa ya yi, yana kyau mutum ya fita daga gidansa ya je daji ya shakata.

''Ka je da 'ya'yanka wani wuri inda za su yi wasa da kasa da tsirrai, wadanda ke dauke da kwayoyin halittu masu amfani,'' in ji shi

Ya kara da cewa, ''idan kana da gida ka bari tsirrai su fito a harabar gidan su girma, sai ka rika yanke su sau daya ko sau biyu a shekara.''

Karfi bayan rashin lafiya

Bincike daban-daban sun nuna cewa yaran da suka girma a muhallin da ba a tsanantawa wajen tsaftace shi, ba sa yawan kamuwa da cutar daukewar numfashi ta asma da kanjiki.

Sannan kuma akwai kwayoyin bakteriya da suke kare mu sosai daga cutuka masu sanya kuraje da ma wata damuwa.

Ga alama mutum zai iya samun lafiyayyar rayuwa ne ta hanyar mu'amulla ko shiga cikin dabbobin gona da haduwa da 'yan mitsi-mitsin kwayoyin halittu marassa cutarwa amma kuma masu amfani a cikin datti da abinci da kuma ruwa.

''Haduwa da irin wadannan kwayoyin halittu na da muhimmanci wajen samarwa da bunkasa tsarin daidaita garkuwar jiki,'' in ji Thom McDade na jami'ar Northwestern da ke Evanson a Illinois.

Idan wannan tsarin na rage yawan tsananin tsaftar daidai ya ke, kila zai iya bayyana dalilin da samun hauhawar cutar asma da ta kanjiki a cikin shekara 20 da ta gabata.

Ko da ya ke akwai sauran bayanai, misali yanayin tsarin kula da lafiyar jam'a, kamar yawan amfani da ruwan sha da ake sanya wa sinadarai domin tsaftacewa da yawan amfani da kwayoyin magani da kuma sauyi a muhallinmu wanda ya danganci gurbatar muhallin.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Zama da kare ka iya karfafa garkuwar jikinka

''Za ta iya kasancewa abubuwa da yawa da suka danganci tsarin rayuwar yammacin duniya (kasashen Turawa) na da tasiri a ciki.

Kwayoyin magani za su iya damun kwayoyin halittun masu amfani da ke jikinmu, ta hakan kuma su cutar da garkuwar jikinmu,'' in ji Hanski.

Ya kuma kara da cewa, sabanin haka bincike ya nuna karara cewa magunguna rigakafi ba sa cutarwa kuma kuma ba wata rawa da suke takawa wajen kara kanjiki.

Amfanin abin kuma in ji Ruebush shi ne, ka sani cewa duk lokacin da dan rashin lafiya ya same ka, jikinka yana kara karfi kadan.

''Wannan ba sako ba ne da yawan mutane za su so su ji; a ko da yaushe mutane suka kamu da dan zazzabi ko rashin lafiya suna son shan maganin da za su samu sauki nan da nan. Amma kuma ba ka sani ba a duk lokacin da ka sha wannan maganin kana sa jikinka dan rauni ne.''

Ka tuna wannan nan gaba idan ka ji ranka na son ka yi amfani da irin ruwan sabulun nan da ke wanke jiki fes (shower gel), idan za ka yi wanka.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Can you be too clean?