Abin da ba ka sani ba game da jima'i

Hakkin mallakar hoto Thinstock

Mutane za su iya daukar wasu dabi'u na saduwa ko jima'i a matsayin abin da ya sabawa al'ada, duk da cewa akwai yuwuwar wasu dabbobi na irin wadannan dabi'u.

Jason Goldman ya yi mana nazari

Dangantaka da alakar kauna da soyayya na da wuyar sha'ani da fahimta kamar dai yadda saduwa ko jima'i yake.

Soyayya za ta iya kasancewa da matsaloli da suka shafi rashin fahimta ko kuma rashin kyakkyawar sadarwa tsakanin juna a wasu lokutan.

A dangane da haka ka duba yadda za ka ji idan ka gaya wa matarka (ko mijinki) karara cewa kana da wata dabi'a ko hali na jima'i na daban, da ya sabawa al'adarku.

To amma ga wani sirri. A game da duk wata al'ada ko dabi'a tsakanin ma'abota soyayya ko ma'aurata, wadda ake ganin kamar ta saba wa al'ada ko hankali, to ka tabbata cewa akwai wasu halittun da ba mutane ba, wadanda a wurinsu wannan dabi'a ce da suka saba da ita.

Ba shakka akwai misalai da yawa na dabi'un da wasu za su yi koyi da su, kamar cin abinci a dakin kwanciya ko saduwa a wasu wuraren da ba a saba yi ba, to amma ko da ka kai ga yin abin da ba a saba yin ba, akwai yuwuwar cewa za ka ga wannan dabi'a a tsakanin wasu dabbobi.

Dauki misalin rakumin dawa. Namiji da ake kira da suna kamar na sa (bull), ya kan kai ziyara lokaci zuwa lokaci a garke-garke domin neman mata (cow), wadda za so saduwa da shi.

Domin zabar wadda za ta sadu da shi, rakumin zai rika shinshina fitsarin matan.

Matan za su ba shi hadin kai a wannan sansane da yake yi, kamar yadda masu bincike David M. Pratt da Virginia H. Anderson suka bayyana.

Masanan suka ce, ''idan har ya shinshina bayanta dole ne ta yi fitsari ko da kadan ne, wanda shi kuma zai dandana wani da bakinsa.''

Idan rakuma (ta dajin) ta yi sha'awar wani rakumi (na dajin), za ta iya yin fitsari a lokacin da ya ke gittawa ta kusa da ita, ba tare da wata kwarkwasa ba.

Wannan dabi'a ta yin fitsari domin kulla alakar saduwa a tsakanin rakuman na dawa, ba kirkira ba ce ta mutum., ga alama.

Yayin da fitsari ke zaman abin da ke kulla soyayya tsakanin mace da namiji a jinsin rakumin dawa, ita kuwa dorina (hippopotamus) tana dogaro ne a kan kashi.

Dalili da kuma amfani da warwatsa kashin da dirina ke yi abu ne da har yanzu ba a fahimta ba sosai, kamar yadda masanin ilimin halittu Richard Despard Estes ya sanar.

Abin da ya fito fili shi ne mazan da suke da karfi da iko a cikin garke ko a wurin da tarin dorina take, sukan warwatsa kashinsu a harabar da suke a matsayin wata dabara tayin iyakar yankin filinsu.

Masana kimiyya na jami'ar Alberta EL Karstad da RJ Hudson sun bayyana yadda wani namijin dorina mai ji da kai ya rika warwatsa kashi da jelarsa a wani wuri a gabar teku.

To amma akwai wani dalilin na wannan dabi'a ta warwatsa kashi da namijin dorinar ke yi, ba kawai killace harabar yankinsa ba.

Idan namijin ya tunkari mace da irin wannan dabi'a, idan tana sha'awarsa sai ita ma ta karba, ta yi kasa da kanta, ta daga bayanta, tana, ita ma ta shiga warwatsa kashin.

Idan hakan ta tabbata matar ta nuna alamar cewa ta yarda da namijin kenan.

Kwarkwasar samun kusanci tsakanin namiji da mace ba ta tsaya ga amfani da fitsari da kashi ba.

Wasu mutanen sukan yi dan gumurzu kafin su kai ga tabbatar da wannan kusanci.

Amma wannan ba komai ba ne idan aka kwatanta da yadda wani nau'in kifin nan da ake kira shark (blacktip reef shark), wanda ake samu a tekun Indiya da na Pacific yake yi.

A wurin jinsin wanan kifi jima'i yana da wani cizo da ake yi, kafin a kai ga yin shi.

Masanin kimiyyar halittu na jami'ar Stanford Douglas J McCauley, da abokan aikinsa sun yi cikakken bayani kan dabi'ar wadannan kifaye a shekara ta 2010.

Idan tarin maza suka bi mace a hankali kusa da kusa, namijin da yake gaba sai ya cije ta a jela.

Cizon nan sai ya sa ta rage tafiya, har ta samu ta kwace, kafin ya kara cizon ta a kusa da kayar gefenta na hagu.

Idan ya damke ta da baki sai ya ja kanta zuwa karkashin tekun inda kasa take, har ya kai ta inda zai sa mata daya daga cikin 'yan dogayen halittun da ke kasansa masu kama da mazakuta a cikin farjinta, inda za su yi wannan saduwa ta tsawon dakika 68.

Masanin kimiyya a kan wannan jinsin kifi (shark), David Shiffman a kwanan nan ya bayyana cewa ga alama wannan cizo da namiji ke yi wa mace zai iya kasance wa wani mataki na dole domin wannan saduwa a irin wannan muhalli mai santsi.

''Wannan ne zai tabbatar namijin ya kasance a kusa sosai da macen sanna su sadu.''

Wannan ne kila dalilin da ya sa matan jinsin kifin (shark) iri-iri suke da fata mai kauri da karfi fiye da ta mazan.

Wata nau'in saduwar ta daban kuma ita ce ta gungu, inda a duk lokacin damuna a kudancin Manitoba da ke canada, dubun dubatar wasu jajayen micizai ne suke fitowa daga ramukansu, inda suke taro domin saduwa.

Idan mace ta fito za ta rikar fitar da wani kanshi na jan hankali wanda zai jawo hankalin daruruwan maza su biyo ta.

Kamar wannan bai isa ba, masana kimiyya sun gano cewa wasu macizan maza sukan sauya juye su zaman kamar mata, ta yadda suke fitar da irin wannan kanshi da mata ke jan hankalin maza da shi.

Wani tunani da masana kimiyya ke yi shi ne mazan macizan da suke yin irin wannan abu, dabara ce suke yi domin kawar da hankalin sauran mazaje daga kan mace.

Amma kuma masana kimiyya na Australia da Amurka suna ganin macizan maza suna zama kamar mata ne domin su yi saurin dumama jikinsu kuma su rage hadarin fada wa hannun wata halittar da za ta kama su.

Ita kuwa wata halittar ruwa da ake kira mourning cuttlefish da Ingilishi sauya launin da take yi ma ya kai wani matsayi.

Halittar wadda ake samu a tekun gabashin Australia, tana sauya launinta ne cikin sauri .

Idan namijin halittar ya so ya ja hankalin wata mata da ke kusa, sai ya rika sauya launin jikinsa.

Idan wani namijin ya nufo wurin sai ya sauya launin jikinsa ya yi kama da mace domin wancan din ya dauka duk mata ne.

Ita matar daga bangarenta kuwa tana ganin wanda yake tare da idan a matsayin namiji, wancan da ya zo kusa da wurin a nasa bangaren yana ganin mace ce sai ya kama hanya ya tafi, ya bar wannan din ya cigaba da neman matar.

Al'ummarmu za ta iya daukar wasu dabi'un na saduwa a matsayin abin da ya saba ko wanda bai dace ba ko ma hauka.

To amma kamar yadda abokanta take da wasa da ma wasan matasa, bincike wasu halittun ya taimaka mana ganin yadda wasu abubuwan suke, ko da ya ke da dan bambanci da yadda dabi'armu take.

Amma idan kuma muka dan karkatar da kanmu muka duba za mu iya hangen zaren da ya hada mu da da 'yan uwan halittarmu ta rai wadanda ba mutane ba. Ko da kuwa wannan zare na 'yan uwantaka ya saba wa al'adarmu.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The wilder side of sex