Me ya sa muka tsani kashi sosai?

Gaskiya ce tsagwaronta ba wani kauce-kauce, mun tsani ganin kashi. To amma me ya sa hakan? Domin gano wannan amsa muna bukatar sanin dabbobin da su ma su ke yi wa kashi wannan kallo da kuma wadanda su sun ma fi son inda ya ke.

Jason G Goldman ya yi nazari domin gano wannan amsa.

A bisa al'ada da dabi'a mutane sun tsani kashi. Kuma kaunar da muke yi wa 'ya'yanmu ta fi tsanar da mu ke yi wa kashi da fitsari da sauran kazantar da 'ya'yan su ke fitarwa, amma duk da haka ba wanda ya ke jin dadin sauya wa dansa kunzugun da ya baci da kashi.

Wani wasa da a ke yi a Amurka, wanda ya kunshi cin kayan kwalan da makulashe a cikin kunzugun yara mai kyau wanda ba a taba amfani da shi ba, ya kan tayar wa da mutane da dama hankali, domin ba sa jin dadin hakan.

Dabbobi da dama su ma haka su ke ji a game da kashi kamar yadda mutane ba sa son ganinsa ko wani abu da ya shafe shi, to amma kuma wasu halittun su kuwa neman kashin ma suke yi.

Wannan ne ya jawo bukatar sanin ainahin menene a halittarmu da ke sa mu jin wannan tsana ta kashi.

Tsana kamar yadda Charles Darwin ya bayyana na daya daga cikin abubuwa shida a duniya da ke tayar da hankali.

Yadda a ke ganin alamarta a fuska a tsakanin al'ummomi da yawa shi ne, za a ga an gwatsane hanci da bata rai ko murtuke fuska.

Wannan yanayi da a ke gani a fili ya kuma hada da wani yanayin da can cikin jiki ma wasu abubuwan ke faruwa, kamar yanayin bugun jinin mutum (BP) ya yi kasa. Sannan karfin yadda fatar mutum ke saurin ji idan wani abu kamar lantarki ya taba ta zai ragu, kuma cikin mutum zai burkuce kamar zai yi amai.

Duk a wannan lokaci, da zarar mutum ya ga abin da ya tsana ko ya tayar masa da hankali na kazanta.

Kafin zuwan cigaban zamani inda a ke yin bandaki a cikin dakunan kwana, mu kan yi bahaya ne a cikin salga da sauran wurare can nesa da dakunanmu na kwana domin nesanta kanmu da kashin.

Wannan tsana da mu ke yi wa kashinmu har ta shafi kazantar sauran dabbobi ma, ta yadda a wasu kasashen masu karnukan da ba su kwashe kashin karnukansu a titi ba za a ci su tara mai yawa.

Ba jinsin mutum ba ne kadai ya kan dauki duk wani mataki na nesanta kansa daga duk wata kazanta kamar kashi, domin wasu dalilai masu amfani ba.

Masanin tunanin dan adam Paul Rozin na jami'ar Pennsylvania, ya ce, shi yana ganin, tsanar da mu ke yi wa kazanta na rage mana hadarin kamuwa da kwayoyin halittu masu haddasa cuta a rubabben nama da kashi da amai ko kuma jini.

Haka kuma tana iya ma kare mu daga wasu mutanen wadanda suka riga suka kamu da cutar ko kuma kwayoyin cutar suka harbe su.

A littafinsa mai suna ''How the Mind Works'', masanin tunanin dan adam na Amurka Steven Pinker, ya rubuta cewa wannan tsana da mu ke yi na iya nuna yadda a zuci muka fahimci yanayin 'yan kananan kwayoyin halitta (microbiology).

Ya ce, ''tun da kwayoyin cuta na yaduwa ne ta hanyar haduwa da jiki, saboda haka ba abin mamaki ba ne idan wani abu ya taba wata kazanta ya zama mai kazanta har abada.''

Ba mu mutane kadai ba ne mu ke gudun wurin da kashi ya ke ba, wasu dabbobin ma suna kiwo ne nesa da inda suka yi kashi.

Misali shanu ba haka kawai suke kiwo a ko'ina ba, domin saboda yadda suke kauce wa wurin da kashi ya ke, shi ya sa ba sa cin kwayoyin cutar da ke sa musu tsutsar ciki sosai.

Haka su ma tumakai, kamar yadda wasu gwaje-gwaje da masu bincike a jami'ar Aberdeen da ke Biritaniya suka yi, sun nuna yadda tumakai suka fi son yin kiwo a filayen da kashi bai bata ba fiye da wadanda suka baci da kashi.

Sai dai ba sa iya tantance wa tsakanin kashin da ya ke dauke da kwayoyin cuta da wanda ba ya dauke da kwayoyin cuta, saboda haka suka kwammace su kauce wa duk inda kashi ya ke, domin su shafa wa kansu lafiya.

Su ma dawakai su kan kaurace wa wurin da suka yi kashi, domin su yi kiwo a wurin da babu shi.

Ita ma barewa ko kanki da birai da yawa suna zabar wurin da bai gurbata da kashi ba ne su yi kiwo.

Sai dai ba dukkanin jinsin dabbobi ba ne su ke kaurace wa wurin da ya gurbata da kashi ba, hasali ma wasu sun fi zama a inda kashin ya ke.

Patrick Walsh da Amy Pederson daga jami'ar Edinburgh, a Biritaniya, tare da Erin McCreless daga jami'ar California, a Santa Cruz ta Amurka, sun lura cewa wasu nau'ukan beraye biyu masu dangantaka da juna, wadanda suke da farin gashi daga kasansu har kafafunsu (white-footed mouse, deer mouse) suna kama ramin da wasu beraye suka zauna ne kuma wadanda suke da abinci da kashi.

Masu binciken sun gudanar da wasu gwaje-gwaje daban har guda uku domin su ga ko lalle wadannan beraye sun fi son wurin da y ke da kashin ne.

Bincikensu na farko ya gano cewa, berayen kamar tumakai ba sa iya bambancewa tsakanin kashin beran da ya ke dauke da kwayoyin cuta da kuma wanda ya ke lafiya kalau.

Amma kuma gwaji na biyu ya bayar da mamaki sosai domin, sun ga cewa berayen sun fi son zama a ramin da kashi ya ke maimakon ramin da ba kashi.

A fannin shirya wurin kwanciya ma, idan har suna da zabi tsakanin amfani da audugar da wasu berayen suka yi amfani da ita a baya da wadda ta ke sabuwa maras datti ko kashi, sun fi son amfani da wadda aka taba amfani da ita.

Wato dai watakila za a iya cewa berayen sun fi son amfani da audugar da ke dauke da kwayoyin cuta maimakon mai tsafta.

Wannan dabi'a ta berayen haka kuma ta ke a fannin kiwonsu ko kuma cin abincinsu.

Saboda za su fi son cin abincin da ya ke kusa da kashi ko ya harbu da kwayoyin cutar ko bai harbu ba maimakon su ci abincin da ya ke da tsafta.

Ta wata hanya za a iya cewa beraye kusan kishiyoyin tumakai ne.

Duk da cewa dukkanin dabbobin biyu ba sa iya tantancewa tsakanin kashin da ba ya dauke da kwayoyin cuta da wanda ya ke dauke da kwayoyin cuta, amma su tumakai suna kaurace wa duk wanda ya ke da kashi, amma su kuwa beraye sai su yi kasada su ci na wurin kashin.

Muhimmin abin tambayar a nan shi ne me ya sa hakan? Da farko za a ga abin da berayen ke yi na cin abincin da ke da kashin ko na wurin da kashi ya ke abu ne maras kyau, idan aka yi la'akari da illar da cuta za ta iya haifarwa.

Abin lura da sha'awa a nan shi ne cewa dabbobi irin su berayen da aka rena domin amfani da su a dakin gwaji na kimiyya da kuma na sha'awa a gida suna kaurace wa abin da ya ke da kashi.

To tun da wadancan nau'ukan beraye biyu (wadanda suke a daji) da muka ambata a baya masu farin gashi a kasansu da kuma kafa su ma suna kaurace wa abin da ya ke da kashi, maganar cewa renon bera ne a gida ko dakin kimiyya, ke sa ya kaurace wa abin da ya ke da kashi, ba shi ne dalili ba kenan, to menene dalili?

Ga fahimtar Walsh da abokan bincikensa, su suna ganin su wadancan berayen daji, kasancewar kashin wasu berayen 'yan uwansu a kusa da abinci ko inda za su zauna na nuna cewa wurin ba shi da hadarin gamuwa da wata babbar dabba da za ta kama su ta cinye.

Saboda haka da a ce sun je inda za su fada bakin wata dabba da za ta cinye su, sun gwammace su yi kasadar kamuwa da cuta daga kashi.

Dabbobin da su ke dakin gwaji na kimiyya gaba dayansu ba sa cikin hadari sosai na gamuwa da manyan dabbobi da za su cinye su kamar takwarorinsu da ke daji, saboda haka suna da damar zabar abincin da za su ji da wurin da za su yi gida.

Masu binciken suka ce kowace dabba dole ne ta yi lissafi tsakanin kauce wa halittun da za su cutar da ita da kuma tsira da rai.

Saboda haka idan ka yi nazari da wannan bayani za ka ga cewa gudu ko kauce wa kashi da mu ke yi wata dama ce ta jin dadin.

Watakila kasancewar jinsinmu na dan adam, ba ya fuskantar wata barazana daga wata dabba (wadda mutum ne ita kuma abincinta) a kusa da shi, wannan shi ya sa ya yi sa'a har ya ke tsanar ganin kashi da sauran abubuwa na kazanta.

Sanin wannan shi zai iya sa watakila nan gaba ka fahimci irin martaninka sosai idan ka ga kunzugun yaro da ya baci da kashi ko kuma ka ga kashin kare a takalminka.

Ina ganin dai da wuya ka ji su suna kanshin furanni (kunzugun ko takalmin).

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Why do humans hate poo so much?