A natsu....lokaci ne na darasi a makarantar dabbobi

Hakkin mallakar hoto Getty

Dabbobi da dama kamar wata mai kama da kurege da ake kira ''meerkat a Ingilishi suna karantar da 'ya'yansu kamar yadda mu ke yi. To amma suna koyon darasi ne kamar yadda mu mutane mu ke yi?

Jason G Goldman ya bincika wannan lamari

Barka da zuwa Makarantar ''Meerkat''. Ba a biyan kudin shiga, sannan ana bayar da abincin rana kyauta, ko da ya ke kunama ce kadai abincin.

Duk da cewa kunama tana da dadi kuma tana da abubuwa masu gina jiki, amma fa tana da hadari sosai.

Kuskure daya tak na idon da ba a horas ba, ko kuma kafar mai ci-da-zuci na iya kai wannan dabba (meerkat) da tsautsayi ya hau ga mutuwa.

Saboda haka dole ne sai 'ya'yan wannan dabba mai kama da kuregen sun halarci ajin darasin koyon cin abinci.

Ita dai koyarwa ma'anarta ita ce, sadarwa tsakanin mutane biyu ko fiye da haka, wadda kan haifar da bayar da ilimi ko wata kwarewa, kamar yadda masana tunanin dan adam 'yan kasar Hungary, Giorgy Gergely da Gergely Csibra suka bayyana.

Kafin koyarwa ta amsa sunanta, dole ne mai koyarwa ko malami ya tsara dabi'arsa ta hanyar shirya darasinsa daidai da kokarin dalibi.

Kuma ilimin da zai bayar dole ne ya kasance bayani wanda za a iya amfani da shi a kan sabbin mutane ko kayayyaki ko wurare ko kuma wasu abubuwa ko yanayi, wato dai abin da a ke kira 'bayanin da za a iya amfani da shi a kan komai'.

Kamar dai salon maganar da a ke cewa, nunawa mutum inda zai samu kifi ba koyarwa ba ce, amma koya masa yadda zai kama kifi, ita ce koyarwa.

To mu koma kan waccan makaranta da muka fara maganarta a baya, ta dabbar (meerkat) da muka ce mai kama da kurege.

A wannan makaranta manya ne masana wadanda su ke da kwarewa su ke ba wa dalibansu ('ya'yansu) matacciyar kunama, wadda aka cire mata kari (na harbi).

Da wannan matacciyar kunama ce su daliban su ke koyon yadda za su cicciri jikin kunamar da su ke ci.

Da zarar sun kware da wannan darasin, sai kuma malaman nasu wato manyan, su ba su, wata matacciyar kunamar amma wadda ba a cire mata kari ba, ita ma su ko yi yadda za su ciri abubuwan da su ke ci a jikinta.

A lura cewa, abu ne mai sauki a wurin su wadannan yara, ko matasa su koyi cire karin kunamar a jikin matacciya maimakon mai rai wadda kuma ke kazar-kazar.

A karshe ne kuma sai manyan su ba wa matasan kunama mai rai da lafiya, da karinta daidai, su nuna musu yadda za su yi mu'amulla da ita.

Ta wannan hanya matasan da ba su da ilimi na mu'amulla da kunamar, su ke koyon yadda za su yi hakan, tun daga matakin da ta ke na maras cutarwa har zuwa mai hadari, daidai da shekarunsu da kuma kwarewarsu.

Wato kenan su manyan wannan dabba suna kara matakin manhajar koyarwar da kuma dabi'arsu bisa la'akari da dabi'ar matasan.

Sai dai fa, a duk wadannan matakai uku, su manyan ba sa koya wa matasan ainahin yadda za su kashe kunamar, za a iya cewa su na ba su abubuwan yin hakan ne kawai.

Kamar mai samar da kayayyakin yin girki ne, wanda ya kawo tukwane da kwanuka da wukake da kayan miya, amma bai bayar da bayanin yadda za a yi amfani da su a yi girkin ba.

Kenan malaman waccan makaranta ta wannan dabba, ba koyarwa su ke yi ba, kamar yadda Gergely da Csibra suka bayyana ma'anar koyarwa.

Watakila wata nau'in tururuwa (da ke gudu) za ta iya kusan dacewa da ma'anar masanan ta koyarwa.

Ita dai wannan tururuwa, kamar waccan dabba mai kama da kurege, idan guda daya ta gano inda abinci ya ke, sai ta sauya yanayin dabi'arta domin 'yar uwarta da ke binta a baya ita ma ta yi koyi da hakan.

Bayan sun bar gidansu ne (raminsu) sai ita wadda ke gaba (mai koyarwa kenan) ta rage tafiya ko kuma ta rika tsayawa lokaci zuwa lokaci, domin mai bin nata ta haddace hanyar daga gidan nasu da inda abincin ya ke.

Idan har aka samu wata matsala a tafiyar, jagorar za ta tsaya ta jira mai koyon (mai bin nata) har ta dawo kafin a ci gaba da darasin (tafiyar).

Yadda abin ya ke aiki, shi ne, ita masaniyar tururuwar za ta shiga gaba, kuma mai binta tana tattaba ta, ta baya akai-akai domin ta nuna cewa tana tare da ita, ta ci gaba da tafiyar nuna mata hanya, koyarwar kenan.

Yayin da dukkaninsu halittun biyu, ita waccan dabbar mai kama da kurege da kuma tururuwar su ke kara matakin koyarwar tasu daidai da sani ko kwarewa ko kuma fahimtar daliban nasu, ita tururuwar, koyarwarta sadarwa ce tsakanin dalibi da malama a zahiri karara.

Duk da haka, wannan sadarwa ko koyarwa tsakanin tururuwar ba ta amsa ka'ida ko ma'anar koyarwa ba.

Saboda bayanin da a ke bayarwa ya tsaya ne kawai tsakanin tururuwa biyu, kuma daga wannan wurin (gidansu) zuwa inda abincin ya ke, sannan ilimi ne na yanzu ne kawai.

Maimakon nuna wa juna yadda za a iya samo abinci a ko da yaushe, bayanin da malamar ke bayarwa ya dogara ne kawai kan inda za a samu abinci a wani lokaci daya kawai.

Dabbobi da yawa su ma suna amfani da irin wannan tsari na koyarwa.

Kudan zuma yana yin shawagi iri daban-daban domin nuna inda abinci ya ke, kuma birai su kan yi kuka ko kara iri-iri domin ankarar da junansu zuwanwani mugu ko wata dabba mai hallaka su.

Birin da ya ke sanar da 'yan uwansa ta hanyar kuka cewa ga fa muguwar dabbar nan da ke kashe su tana shawagi a sama, ba zai iya sadarwa kamar cewa wannan dabba ko tsuntsun da ke kashe su yana farauta ne da rana, ko kuma wannan tsuntsu daga kusurwar arewa ya ke bullowa.

Damusa (cheetah) na nuna wa 'ya'yanta yadda za su kama dabba, wanda wannan ilimi ne na gaba daya, amma kamar yadda waccan dabba mai kama da kurege ke yi, koyarwar ba sadarwa ba ce ta fili karara.

Yunwar bayani.

A zahirin gaskiya duk wata sananniyar ganawa mai kama da koyarwa tsakanin dabbobin da ba mutane ba, ta kunshi tsarin yada bayani daya ne kawai.

Koyarwar dan adam ce kadai ta cika ka'idoji ukun da aka sani da ke tabbatar da koyarwa ta amsa sunanta na koyarwa.

Kuma abu mafi muhimmanci ma, mutane ne kawai malamai na komai. Mutane suna koyar da komai. Mutane suna koya wa duk wani abu.

Muna koyar da lissafi da yadda za a daure takalmi. Muna koyar da kimiyya da ilimin kwamfuta da aikin kafinta da kuma yadda a ke yin tukwane.

Lokacin da na ke makarantar gaba da furamare, ina koyon darasin yadda a ke rubutu na ado da kayatarwa.

Na yi shekara biyu ina jarraba kwallon kafa, shekara daya ina kokarin koyon kwallon kwando da kuma wata shekara daya da na yi fafutukar lakantar kwallon raga (volley).

Na shiga ajin koyon zane, kuma wata rana na dade ina koyon yadda a ke shirya furanni. Na kuma yi shekara biyu ina kokarin koyon yadda a ke kada jita.

Shin menene ya sa mu mutane mu ke koyarwa ta hanyar da ba wata dabba ke yi?

Gergely da Csibra cewa suka yi, su suna ganin ai ita kanta sadarwar da mutum ke yi ta musamman ce, inda suka rubuta cewa,

''Idan na nuna jiragen sama biyu, na ce maka 'jiragen sama suna tashi', abin da za ka koya, ba ya tsaya ba ne a kan wadannan jiragen saman da ka gani biyu kawai.

ko kuma a ce ilimin ya tsaya a iya wannan maganar ta lokacin kadai, amma hakan zai ba ka ilimi mai fadi game da shi jirgi ma wana irin abu ne, a wane rukuni na abubuwa ya ke, da makamantan haka...''

Abin da masanan su ke magana a takaice shi ne, girma ko fadin bayanin da suka yi maka, shi kansa yana nuna kansa a sadarwar kanta.

Suka cigaba da cewa, ''idan a zahiri ko a aikace na nuna maka yadda za ka bude katan (kwali) na madara, abin da za ka koya shi ne, yadda za ka bude duk wani katan irin wannan,'' ba wai yadda za ka bude wannan kwalin ba kawai.

Saboda haka koyon ilimi na gaba daya ko mai fadi yana kunshe ne a cikin sadarwar mutum.

Wannan sadarwa ko ana yinta ne ta harshe (yare) ko kuma ba ta harshe ba, ba ta bukatar sai lalle mai koyon ya fahimce ta ko ya gane ta.

A tsakanin dukkanin dabbobin duniyar nan, mutane ne kadai su ke gina gidaje dogaye masu hawa barkatai, su ne su ke bin ka'idar da aka shirya daki-daki ta yin wani abu kamar girki, da wasan dara da koyon kididdiga da karbar sakonnin faifan sauti na DVD ta wasika da kai butum-butumi duniyar Mars.

Irin al'ada ko rayuwa da mutane ke yi za ta iya samuwa ne kawai saboda mun kware wajen koyarwa da kuma koyo daga malamai.

Ta yawancin hanyoyi, bambancin da ke tsakanin mutum da dabbobin da ba mutane ba, na matsayi ne kawai amma ba na iri ba.

Ma'ana irinmu daya amma mun bambanta a mataki na kwarewa ko kokari.

Amma kuma akwai wani muhimmin bambanci tsakanin jinsinmu na mutum da duk wani jinsi. Mu muna koyarwa, kuma muna koyar da komai.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan Pay attention… time for lessons at animal school