Kasashen da ake farfesun bera

Hakkin mallakar hoto Grant Singleton

Yayin da aka tsani bera kuma ake yin duk abin da za a iya domin a hallaka shi, wasu al'ummomin kuwa beran abinci ne na kwalan da makulashe a wurinsu.

Ga nazarin Karl Gruber

A kullum kafin ka je ka kwanta na san da wuya ba sai ka tabbatar ba wani kayan abinci da ka manta ba ka adana ba da kyau.

Idan ba haka ba karshenta wannan abincin ya fada hannun sanannen bakon nan da ba ka maraba da shi; bera, wanda na san ka san shi farin sani, ba sanin shanu ba.

Wulkitawar bera kawai a muhalli ta isa ta jawo surutu da korafi ga hukuma daga jama'a, kamar yadda a kwanan nan hukumomin New York a Amurka suka sabunta matakan magance matsalar yawan bera a birnin.

To amma Allah daya gari bamban, ba ko ina ba ne aka tsani wannan bako ba, hasali a wasu wuraren a duniya abinci ne mai dan karen dadi da kuma daraja.

A duk ranar bakwai ga watan Maris na kowa ce shekara, al'ummar kabilar Adi, a wani kauye da ke kan tsaunukan arewa maso gabashin Indiya, su kan yi wani biki (Unying-Aran) na daban, inda farfesun bera shi ne muhimmin abincin bikin.

Daya daga cikin miyar da aka fi so ma a yayin dabdalar, wadda a ke kira bule-bulak oying, ana yinta ne da kayan cikin bera, kama daga hanji da koda da marena har ma da dan tayi.

Duk wani nau'in bera daga na gida har zuwa na daji ba abin kyama ba ne a wannan gari.

An ma fi son jela da kafar beran saboda dadinsu, in ji Victor Benno Meyer-Rochow, na jami'ar Oulu ta Finland, wanda ya tattauna da wasu da yawa daga cikin 'yan kabilar ta Adi, a wani nazari da ya ke yi kwanan nan na bera a matsayin abinci.

Amsoshi da bayanan da suka yi masa sun bayyana wani matsayi na daban na yadda a ke daukar bera.

Mutanen sun gaya wa Meyer-Rochow, cewa naman bera shi ne naman da ya fi kowa ne nama dadi a saninsu.

Ya ce, ''sun gaya min cewa, 'ba wata walima, ba wata murna da za a yi idan a yayin wani taro ba farfesun bera.

Domin girmama wani babban bako, ko dan uwa ko wani taro na musamman, dole ne sai idan da bera a cikin jerin kayan abincin da za a kawo wurin.'''

Hakkin mallakar hoto MeyerRochow Megu
Image caption Ya danganta da irin tarkon da aka sa, a kan iya kama bera 30 zuwa 100 a rana daya a kauyen Indiya da a ke cinsu

Ana matukar kaunar bera, ba wai kawai a matsayin abinci ba. Malamin jami'ar ya ce, ''har garar beran (banda) dangin ango su ke kai wa gidan amarya, wadda za ta bar wa iyayenta da dangi kafin ta tafi gidan angon.''

Da safiyar ranar farko ta wannan babban biki da mutanen kauyen na Unying-Aran su ke yi duk shekara, mai suna Aman Ro, ana bai wa yara beraye bibbiyu kamar tukuici, kamar yadda a wasu wuraren a ke ba wa yara 'yan abubuwan wasa da safiyar ranar kirsimeti.

Babu cikakken bayani kan lokacin da wannan al'umma ta kabilar Adi ta faro wannan al'ada ta cin bera, amma Meyer-Rochow na ganin dadaddiya ce, kuma ba wai sun faro ta ba ne saboda rashin wasu dabbobin ba.

Akwai dabbobin dawa da yawa kamar su barewa da bauna da har ma da na gida kamar akuya da har yanzu suke dazukan kauyen.

Su dai wadannan mutane sun fi son naman beran ne. ''Sun tabbatar min cewa 'ba wani nama da ya fi na bera','' in ji shi.

Hatta shi kansa Meyer-Rochow, duk da cewa kayan ganye ya ke ci ba ya cin nama, ya dandana farfesun beran, kuma bai ji wani bambanci da sauran nama ba, in banda kanshi ko warin naman.

Ya ce ''wannan ya sa na tuna da darasin farko na dakin bincike da daliban nazarin namun daji ke yi, inda su ke fede bera domin nazarin yadda kasusuwansa su ke.''

Hakkin mallakar hoto Prof S.R. Belmain University of Greenwich
Image caption Gasassun beraye da mai da tumatur ana gab da dibar gararsu

Ba a wannan dan yankin na kasar Indiya ba ne kawai aka dauki bera amtsayin abinci mai muhimmanci ba.

Mai gabatar da shirye-shirye a tashar talabijin ta Biritaniya (British TV), Stefan Gates ya yi yawo a kasashen duniya, inda ya hadu da mutane masu abinci na daban iri-iri.

A wajen birnin Yaounde a Kamaru, ya ga wata 'yar gona da a ke kiwon wasu irin beraye, wadanda ya ce sun kai kamar karamin kare fada da mugunta.

Suna da fada amma kuma suna da dadi, domin kamar yadda ya ce farfesunsu na musamman ne saboda ya fi farfesun kaji ko na kayayyakin ganye tsada.

To kuma ya dandanonsa ya ke? ''Ban taba cin wani nama da ya kai shi dadi ba a rayuwata,'' in ji shi. ''Farfesu ne mai dadin gaske na ban mamaki.''

A jihar Bihar ta Indiya Gates ya shafe wani lokaci da al'ummar Dalit, daya daga cikin kabilu 'yan bora mafi talauci a kasar.

Mutanen da ya gana da su ana kiransu masu cin bera a yankin, suna kula wa da gonakin 'yan wata kabilar, su ma 'yan bora ne na Indiya, wadanda suka mallaki filayen noma.

Masu cin beran suna kula musu da gonakin kuma ladansu na yin hakan shi ne su rika kama berayen da suka addabi gonakin.

Hakkin mallakar hoto Grant Singleton International Rice Research Institute

Kamar yadda Gates ya ce wadannan kananan beraye suna da dadi kamar kananan kaji ko salwa.

Abin da kawai ya ke dan bata naman shi ne warin babbakar gashin, domin ana babbake shi gaba daya ne domin kada a yi asarar 'yar wata fata ko nama.

To wannan babbakewa da ake yi masa shi ya sa ya ke kaurin gashin, wanda ba shi da dadi ko alama, in ji Gates.

Ya ce, wannan kuma yana sa naman ya yi daci daga wajensa. Amma cikinsa lafiya kalau. ''Nama da fatar cikinsa na da dan karen dadi'' In ji shi.

Beraye masu dai a duniya

Sha'awarmu ta cin beraye dadaddiya ce domin ta kai daruruwan shekaru kamar yadda wani nazari na malaman jami'ar Nebraska-Lincoln ya nuna, ana cin beraye a lokacin daular Tang (618-907 AD), kuma ana kiransu a lokacin da inkiyar barewar gida.

A wannan zamani wanda a ke ci na musamman, shi ne sabbin haihuwa, inda a ke tsoma su a cikin zuma, ana ci da irin tsinken nan na cin abinci a kasar Chinan. Kamar yadda marubata nazarin suka bayyana.

Har zuwa shekara 200 da ta gabata al'ummomi da dama na yankin tsakiya da kudancin tekun Pacific ciki har da 'yan kabilar Maori na New Zealand, suna cin wani nau'in bera (kiore, Rattus exulans) kamar irin na gida na yau.

Kafin bunkasar kasashen Turai, yankin tsibirin kudu na New Zealand, wuri ne da a ke samar da wannan nau'i na bera da a ke kira Kiore sosai, wanda a ke adana shi ana cinsa da yawa galibi a lokacin sanyi. Kamar yadda Jim Williams, wani mai bincike a jami'ar Otago ta New Zealand ya bayyana.

Hakkin mallakar hoto Grant Singleton
Image caption Wata mai sayar da gasassun beraye a Thailand

Kamar yadda kundin bayanan tarihi na New Zealand ya nuna, shi wannan bera (kiore) yana da muhimmanci matuka, domin idan an yi bako a wancan zamanin farfesunsa a ke yi masa, har ma kuma ana amfani da shi a matsayin kudi, da a ke musayarsa a lokacin biki kamar na aure.

Ana cin bera sosai a Cambodia da Laos da Myanmar da wasu sassan Philippines da Indonesia da Thailand da Ghana da China da Vietnam in ji Grant Singleton, na cibiyar bincike kan noman shinkafa ta Philippines.

Singleton ya ce ya ci naman bera akalla sau shida a yankin Mekong na kasar Vietnam. Yadda dandanon ya ke?

Ya ce, ''shi beran gonar shinkafa zan iya cewa namansa ya fi kama dandanon naman daji, ya dan kusa da na zomo.''

Haka kuma Singleton ya tuna yadda ya ci naman beran a Laos da Myanmar.

A Laos ya ce manoma a arewacin kasar za su iya bambance akalla nau'in beraye biyar daga dandanonsu.

Hakkin mallakar hoto Prof S.R. Belmain University of Greenwich
Image caption Wani mutum da ke Morrumbala, a lardin Zambezia, a Mozambique yana shirin cin beransa

A Afrika wasu al'ummomi sun dade da al'adar cin bera. Misali a Najeriya, kusan dukkanin kabilun kasar na cin beran nan babba na daji, da a ke kira African giant, in ji Mojisola Oyarekua na jami'ar kimiyya da fasaha ta Ifaki-Ekiti (usti).

Malamin ya ce, ''ana daukarsa a matsayin abinci na musamman kuma namansa ya fi na saniya ko kifin da ya ke daidai da shi, kuma za a iya cinsa gasasshe ko dafaffe ko a bangarsa.

To me ya sa mutane su ke cin bera? Dole ce? Bayan da ya dandana naman bera a kasashe da dama Gates ya ce mutane suna cinsa ne kawai saboda sha'awa amma ba domin ba su da wani nama ba ne.

Ba lalle ba ne ka samu naman bera a wurin cin abinci na unguwarku ba a yanzu (a Turai) amma yayin da duniya ke kara dunkulewa wuri daya, kuma a ke samun mutanen da ke da sha'awar jarraba abincin wasu wurare, ba za a ce ba ka yi daidai ba idan ka ce wata rana naman bera zai zama kusan ko'ina a kasashen yammacin duniya.

Ka jarraba shi. Kila za ka ji dadinsa. Hasali ma wasu a wurinsu shi ne naman da ya fi kowa ne nama dadi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Turanci latsa nan. The countries where rats are on the menu