Ka san sirrin da ba a so ka sani?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

A duk fadin duniya, akwai wasu sakonni ko bayanai da alamomi a titunan birane da asibitoci da motocin haya da sauran wurare. To me ya sa a ke yinsu?

Chris Baraniuk ya duba wannan sirri

Idan wata rana a tashar jirgin kasa na Biritaniya ka ji an ce, ''Supeto Sands ka zo dakin gudanarwa ("Inspector Sands to the control room, please."), to kada hanklinka ya tashi.

Amma yana da kyau ka san cewa, wani sako ne na sirri ko saye domin gaya wa ma'aikata cewa akwai wata babbar matsala a wani wuri a cikin ginin tashar.

Dabarar ita ce domin kada a tayar da hankalin matafiya, amma kuma a sadar da sakon ga kwararrun da za su iya maganin matsalar.

An kawo maganar irin wannan tsari na amfani da kalmomi na saye a wurin wata tattaunawa da aka yi ta ma'abota shafin sadarwa da muhawara na intanet na Reddit, kuma tattaunawar ta jawo dubban misalai. To irin wadanne a ke da su a wurare?

Masu kyau da ya kamata mu fara dubawa su ne na asibiti. Yawanci wadannan ana amfani da launi ne a kansu, kuma wani asibiti a Canada ya wallafa jerin nasa a Intanet.

''Launin ja'' na nufin gobara ta tashi, ''launin fari'' na nufin akwai wani mutum mai hadari, yayin da launin baki ke nufin akwai barazanar bam a asibitin.

Wasu bayanan a kan yi sayensu ne kawai kamar zaurance, ta yadda ma'aikata ne kawai ko kuma wadanda abin ya shafa za su fahimta.

An ce wani lokaci ma'aikatan asibiti su kan kira dakin ajiye gawa da lambun furanni (Rose Cottage), domin gudun kada su tayar da hankalin dangin maras lafiyar da bai dade da mutuwa ba.

Jiragen ruwa su ma suna da tsarinsu na sirranta abubuwa ko yanayi na tashin hankali.

Daya daga wadannan ita ce kalmar ''Mr Skylight'', wadda kalma ce da kusan duk ma'aikatan jirgin ruwa ke amfani da ita idan jirgin yana cikin hadarin nitsewa.

An yi amfani da ita a lokacin hadarin jirgin ruwan nan MS Estonia a 1994, wanda ya hallaka mutane 852.

A lokacin hadarin, yayin da jirgin ya kama hanyar nitsewa aka bayar da wannan sanarwa (mr Skylight to Number One and Two), abin da ke nufin ma'aikatan jirgin su rufe duk kofofin jirgin kada ruwa ya shiga.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Jirgin ruwan MS Estonia na nitsewa ranar 19 ga watan Nuwamba na 1994, inda ake sanarwa ta sirri "Mr Skylight"

Masanin harshe a jami'ar Lancaster, Paul Baker, ya ce, ''na fahimci amfanin wannan saye da a ke yi, domin zai iya kasancewa mutane ba su da tabbacin hadarin ko matsalar lokacin da su ke sanarwar, saboda haka bai dace ba a tayar wa da jama'a gaba daya hankali.''

Ba ma'aikatu da hukumomi ba ne kadai su ke da wannan tsari na saye na sanar da wani hadari a tsakanin ma'aikatansu ba.

Yawancin wadanda suka bayar da gudummawa a taron da aka yi na ma'abota shafin sada zumunta da muhawara na Reddit, sun bayar da misalai da suka shafi rayuwarsu ta yau da kullum.

Akwai ma'aikatan kamfanonin intanet da makamantansu da suka bayyana hanyoyin saye ko zaurance da su ke sadarwa a tsakaninsu.

Da yawa dga cikinsu sun bayar da misalin kalmar ''Pebkac'', wanda suna ne da aka hada daga kalmomi, wanda kwararrun aikin intanet ke amfani da shi, domin bayyana cewa wani mutum na aiko da sakon wata matsala da ke damun kwamfutarsa.

Abin da ta ke nufi shi ne akwai matsala tsakanin madannan kwamfutar da kujera ("Problem Exists Between Keyboard and Chair").

Akwai misalai da yawa na irin wadannan a wasu wuraren. A kwanan nan BBC ta yi rahato a kan wani slo ko kalma ta musmmn da masana kimiyya su ke amfani da ita wajen rarraba kasida a tsakaninsu.

Alamun saye na gani da ido

Ba dukkanin hanyoyin saye ba ne a ke yi da rubutu. Wasu na gani ne, wadanda a ke tsara su ta yadda ba za a iya ganinsu da ido ba haka kawai.

Kamar yadda wani shiri na BBC a farkon shekaran nan ya gano, yawancin takardun kudi suna da wasu alamomi na musamman na boye (EuRion), da a ke sa su a jiki domin hana yin jabu ta juyar kudin (photocopy) a na'urar kwafin takardu.

An tsara yawancin na'urorin daukar hoton takardu ta yadda za su gano wadannan alamomi.

Hakkin mallakar hoto BBCW

Wasu alamomin na saye na gani da ido su kuwa ana yinsu ne a muhallanmu. Misali daya na ban mamaki shi ne na tarin irin wadannan alamomi (hoboglyps), da a ke yi domin matfiya da mutane marassa muhalli ko gida.

Wadannan alamomi sun hada da wadanda ke nuna irin kyawun ruwan wani famfo ko rafi ko rijiya da ke wuri.

Ko nuna wa mutum cewa mai wani gida mai mutunci ne ko kuma maras son jama'a ne ko ba shi da kirki ko yana da fada.

Irin kungiyoyin matasan nan 'yan ban-bakwai masu rubuce-rubuce a gango su ma suna d wannan dabi'a, inda su ke rubuta wata alama ko wani abu a kan rubutun 'yan wata kungiyar da ba sa ga-maciji da su.

Mujallar Discover ta wallafa misalin wasu daga cikinsu a shekara 2012, wadanda suka hada da ''SS'' (South Side) bangren wata kungiya a Indianapolis, da kuma zana harafin ''X'' da launin ja a kan alamar wata kungiyar wanda hakan ke nufin wani cin mutunci.

Hakkin mallakar hoto FlickrEverfallingCC BY 2.0
Image caption Alama da ke nuna inda ba 'yan sanda da kuma inda ruwa mai kyau ya ke, wadda masu kwana a titi ke yi a tsakaninsu

Abin mamaki bayan da wannan mujalla ta rubuta wannan labari, a yanzu an samar da manhjar kwamfuta da ke taimaka wa 'yan sanda gano ma'anar irin wadannan alamomi da rubuce-rubuce na saye.

Hanzu abin ya kai ma har masarrafa (apps) a ke da ita iri-iri ta wayoyin komai-da-ruwanka na gano ma'anar irin wadannan alamomi na sirri.

A karshe kuma sai irin alamomin nan da ka ke gani na fenti a gefen tituna a garuruwa da birane a dukkanin kasashen duniya, wadanda su ma'aikatan gine-gine da injiniyoyi ne ke sanin ma'anarsu.

Wani rahoto da BBC ta yi kwanan nan ya bayyana ma'anar da yawa daga cikinsu a Biritaniya, inda rahoton y nuna launi daban-daban da ya shafi wayoyi da bututai daban-daban.

Shudi na nufin bututun ruwa yayin da ruwan dorawa ko rawaya ke nufin bututun iskar gas, tsanwa ko kore kuwa na nufin wayoyin na'urar daukar hoto ta tsaro (CCTV) ko kuma wayoyin intanet.

Hakkin mallakar hoto FlickrRory HydeCC BY 2.0
Image caption A tsarin aikin gini launin ja na nufin lantarki, shudi ruwa, kore na'urar daukar hoto ta tsaro, fari kuwa na sadarwa

Dukkanin wannan saye ko sirri na da dalili, wanda ya hada da, kauce wa ta da hanklin jama'a, mika sako tsakanin wasu mutane da su ke aiki iri daya ko su ke da mu'amulla daya ko su ke kungiya daya, ko kuma bayar da bayani na aiki cikin sauki da gaggawa.

Amma da zarar ka gane su, abu ne mai wuya ka dauka cewa ba an yi su ba ne da wata manufa ta boye. Ba mamaki mutane da yawa ke son tattaunawa ta intanet a kan wadannan abubuwa.

''Mutane ba sa son sirri ko?'' In ji Baker. Ya kara da cewa, ''mutane suna da matukar sha'awar samun bayanai da jin labari, hasali ma muna zamani ne na fasahar yada bayanai.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan The secret codes you're not meant to know