Ko motsa jiki na maganin damuwa?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Tattara shedar tasirin motsa jiki a kan tunani na damuwa abu ne mai wuya fiye da yadda za ka yi tsammani. Duk da tarin nazari da bincike da wasu suka yi.

Claudia Hammond ta yi bincike

Akwai tunanin da mutane ke yi na jin cewa motsa jiki na sa ka ji dadin jikinka sosai. An gudanar da bincike na tsawon shekaru a kan batun, sannan wasu likitoci sun sa wasu marassa lafiyar da ke fama da damuwa, su rika motsa jiki bayan ba su shawara ko kuma magani.

To ko za a iya cewa rahotannin 'yan shekarun na kafafen yada labarai da ke nuna cewa wani sabon bincike ya nuna motsa jikin ba ya taimakawa wajen magance cutar damuwa na nufin a matsayar masana harkokin lafiya ba daidai take ba kenan?

Abin ba fa wai yana da sauki ba ne kamar yadda rahotannin kafafen labaran ke nuna wa ba ne, domin tattara bayanai na tasirin motsa jiki a kan cutar damuwa na da wuya fiye da yadda za ka yi tsammani.

Mafi muhimmancin tsarin bincike da ake amfani da shi, shi ne, wanda ake yi tsakanin jama'a, inda za a raba mutane kashi biyu, a bai wa kashi daya magani, sannan daya kashin a bar shi haka ba magani.

Dukkanin mutanen da ake gwajin da su, ba wanda zai san wana bangare yake. Idan gwajin sabon magani ake yi, hakan yana da sauki, inda za a ba wa wasu maganin na gaskiya, 'yan daya kashin kuma a ba su magani na bogi, wanda ba za ka iya tbambance shi da na gaskiya ba.

Irin wannan abu ne da yake da wuya a iya yi a fannin gwajin motsa jiki, domin mutanen da za a yi gwajin da su za su sani ko suna motsa jiki ko ba sa motsawa.

Haka kuma abu ne mai wuya ka tilasta wa mutane motsa jiki, saboda haka sai mutane su zabi bangaren da za su shiga, wanda hakan zai karkata sakamakon, domin mutanen da suke sha'awa da jin dadin motsa jiki za su fi amfana.

Wasu masana a wannan fanni sun gano matsaloli da dama da za su soki yadda aka gudanar da nazari ko gwajin na baya bayan nan.

Binciken dai daya ne daga cikin tarin irinsa da aka yi a baya, saboda haka domin samun cikakke mafi inganci na karkata ga wani nazarin (Cochrane collaboration), wanda bincike ne na bibiya da nazarin, gwaje-gwaje da nazari na harkokin lafiya.

Hada sakamakon nazarce-nazarcen da aka tattaro daga kasashe da yawa kamar Thailand da Denmark da Australiya, an gano cewa motsa jiki yana da amfani a kan mai cutar damuwa.

Saboda haka an fahimci cewa ga alama motsa jiki zai iya taimakawa kadan, wanda hakan ya jawo tambayar dalilin hakan.

Kuma ba shakka akwai kokarin da aka yi na gaske domin amsa wannan tambaya. Daya daga cikin bayanan shi ne cewa, motsa jiki ya kan sa jikin ya fitar da wasu sinadarai (endorphins, dopamine), wadanda za ka ji nishadi a kai.

Akwai kuma wani bayanin da ya samo asali daga yin surace, na shekarun 1970 da aka yi a kasashen Turai masu sanyi sosai (scandinavia), wanda ya nuna cewa dimin da jiki zai yi a sanadin motsa jiki yana sa fitar sanadari (endorphins) daga jikin.

Wadanda akwai gwajin da su, kashin da suka shiga cikin tururrin, sun fi jin dadi,a kan wadanda ba su shiga cikin na'urar turarin ba suka zauna a benci kawai.

Wani abin sani game da wannan bincike ko nazari kuma shi ne, an biya wadanda aka yi nazarin da su ne da barasa.

To amma motsa jiki zai iya inganta yanayinka, (damuwa), ko da jikinka bai yi dumi da gumi ba?

Masu bincike sun yi amfani da hanyoyi da dam, kama daga sanya jaruman mutane su yi tafiya a kan keke, kansu daure da dankwalin da aka sanya kankara a cikinsa, zuwa tukin keke cikin ramin da aka cika da ruwan sanyi (tafkin), sai kansu ne kawai a waje.

Yanayin wadanda suka yi tukin kleken a cikin ramin da aka cika da ruwan sanyin bai sauya ba, amma su wadanda aka sanya musu dankwali mai dauke da kankara, yanayinsu (damuwa) ya inganta.

Ko da ya ke wani zai iya cewa sun ji dadi ne kawai saboda an cire musu kankarar a ka ne da kuma, na'urar auna dumin jikinsu.

Watakila ba sanadin fitar sinadarin daga jikinsu ba ne, kila fita daga gidan, ko kasancewa cikin wasu mutane, ko jin dadin lakantar wani abu daban (hawa keken ko kara kwarewa), ko kuma ma ganin yanayin karfin jikinsu ya karu a sakamakon wannan motsa jiki, duka wadannan za su iya sa su wannan abu.

Dukkanin gwajin da aka yi a kan wadancan nazarcenazarce in ban da guda daya, ba wanda ya kunshi motsa jiki na tsari (na kwararru), yayin da shi sabon nazarin kuma ya bayar da shawarar yin kowane irin motsa jiki.

A ka'idar motsa jikin da ya kamata a ce an yi kamar yadda hukumar da ke kula da sha'anin motsa jiki ta Biritaniya ta bayar da shawara, kamar yadda maganin cutuka daban-daban yake, a kan wannan larurar ta damuwa shi ne, yin motsa jiki na tsari bisa kulawar kwararu, a cikin mutane (ba mutum ya yi shi kadai ba), kuma sau uku a mako.

A karshe Farfesa William Morgan na jami'ar Wnsconsin-Madison ta Amurka ya gabatar da wani tunanin ko dabara, wadda ya kira ta dauke hankalin mutum.

A bisa tsarin nazarin nasa, motsa jiki yana dauke wa mutum hankali daga wani abu da yake ransa ko yake damunsa.

Ya kuma gano cewa tasirin motsa jikin na kawar wa mutum damuwar, yana karewa bayan sa'o'i 24, saboda haka muna bukatar mu rika cigaba da yi.

Amma wannan nazari nasa kila zai karfafa gwiwar mutumin da ba shi da sha'awar motsa jiki ne sosai. Haka zama a kan wata tsohuwar kujera mai laushi a dakin da yake shiru, na wani tsawon lokaci ga lama shi ma yana taimakawa mutun ya ji dadi.

Abin dai lura a nan kawai shi ne, motsa jiki na ka iya taimakawa, amma dai ba maganin damuwa ba ne. Yanayin yadda abin yake shi ne duk yanayin yadda cutar damuwar take, mutane da yawa za su ji dadi bayan wata shida na motsa jiki, ko wane irin magani ko hanya suka bi ta maganin matsalar.

Motsa jiki ba zai yi maka maganin damuwa ba, amma dai abu ne da za a iya gwadawa, kuma idan a karshe aka dace ka ji sauki, to kawai ka yi shi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Does exercise really help with depression?