Gaskiya ne akwai bakar rana a shekara?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Ita ce ranar da aka fi bakin ciki da damuwa (Blue Monday) kamar yadda ake fada a wasu garuruwa da kasashe, to amma ina gaskiyar hakan, akwai wasu bayanai da suka tabbatar da ita, ko dai almara ce kawai?

Idan ba ka taba ji ba, to ka sani yanzu, Litinin ta uku a watan Janairun kowace shekara, ita ce shudiyar Litinin (Blue Monday), abin da ke nufin bakar rana ce da aka fi damuwa da kuma zama cikin bakin ciki a shekara.

A 'yan shekarun da suka gabata kamfanoni sukan samu hanyoyin da za su danganta ranar da kayansu domin tallatawa don a san kayan.

Su kuwa kafofin yada labarai yayin da kamfanonin ke haka, suna tattaunawa ne, yadda aka yi wannan rana ta yi wannan kaurin suna, har ma za ka ga yawanci a kan sanya hotunan mutane cikin damuwa da bakin ciki a cikin ruwan sama.

To shin a zahirin gaskiya Litinin din ta uku ta watan Janairu ita ce ranar da mutane suka fi ganin kunci da damuwa a shekara?

Wannan lamari ya samo asali ne a lokacin da wani kamfanin zirga-zirga ya bayar da wata sanarwa ta kafafen yada labarai a shekara ta 2005, inda yake sanar da cewa, wani masanin tunanin dan adam mai suna Dakta Cliff Arnall, ya gano wata hanyar lisssafi da ke nuna rana mafi muni a shekara.

Hanyar da ya kirkiro ta lissafin ta yi la'akari ne da yanayi, da yawan bashin da mutum ya ci bayan Kirsimeti da kuma damar da mutum yake da ita ta biyan bashin ranar albashi, da lokacin da ya wuce tun Kirsimetin da da irin kwarin gwiwar da yake da shi da kuma bukatar daukar matakin da ya dace, da kuma tsawon lokacin da mutane suka karya alkawarinsu na wani kudurinsu na sabuwar shekara.

Ba a dai fayyace kasashen da ake da wannan al'ada ta daukar Litinin din ta uku ta watan Janairu a matsayin bakar rana ko shudiyar Litinin ba.

Babu dai wasu alkaluma da aka taba wallafa wa wadanda suka tabbatar da abin da mai binciken ya ayyana, a gaskiya ma hatta shi kansa Arnal ya yarda cewa lissafin ba shi wani tasiri.

Rashin wasu bayanai ko alkaluma da aka taba wallafa wa ba abin mamaki ba ne idan ka duba yawan aikin da za a yi a bincike irin wannan.

Bincike ne da za ka hada tarin mutane ka auna dukkanin wadannan abubuwa a kowace rana ta shekarar. Sannan kuma ka ana bukatar ka duba irin gudummawar da kowane abu a cikin lissafin zai iya samar wa na jin rashin dadin na mutum.

Hanyar lissafi na da kyau amma duk wani masanin tunanin dan adam da zai yi bincike zai gaya maka cewa abin takaicin shi ne ba za a iya hasashen damuwa ko farin cikin mutum ba haka ma dabi'arsa ta wata hanyar lissafi.

Amma wanan ba yana nufin ba mu da bayanai a kan sauyin da ake samu a wani lokaci na shekara ba, da sauyin yanayin mutum das kuma abin da yake haifarwa ba.

Bincike a kan yadda mutane ke kashe kansu ya nuna lokacin da mutane suka fi kashe kansu a shekara, ko da yake ba cikin watannin sanyi ba ne da ke haifar da damuwar da ake dangantawa da dalilin kashe kai.

Binciken da aka yi a kasashe 20 ya gano cewa lokacin shekara da mutane suka fi kashe kansu, shi ne lokaci mafi dadi na damuna da farkon bazara.

Wani binciken da shi ma ya bi diddigin yadda mutane ke kashe kansu a Amurka a tsakanin 1971 da 2000 ya samu iran wannan sakamako ne.

Yawanci mutane suna mamakinn wannan, domin lokaci ne da mutane suka fara jin dadi da kyakkyawan fata a game da rayuwa a daidai wanna lokaci da yanayin ya fara zama mai dumi, ga furanni sun fara haskaka wuri, tsuntsaye na kuka mai dadi (waka) da yamma.

To amma wannan fata da sa rai da samun kyakkyawar rayuwa da mutane ke yi a wannan lokaci zai iya sa su su ma ji damuwarsu ta kara tsanani, idan har daman ba sa jin dadin rayuwar, ba su da wani kyakkyawan fata a game da rayuwar.

Ka yi tunani ka ga cewa komai na tafiya daidai a inda kake amma kuma a can cikin ranka ba ka jin dadi. Wasu ma na ganin cewa hasken rana zai iya sa mutum ya ji bukatar hallaka kansa.

Ko kuma ma yanayin da ya inganta zai iya ba wa mutum karfin da yake bukata ya shirya yadda zai kashe kan nasa.

Gaya min dalilin da ba na son ranar Litinin

To kashe kai dai ba abu ne da aka fi yawan yi a watan Janairu ba, haka kuma taruwar abubuwa da dama ne ke haifar da damuwa, wanda kuma ba lalle ba ne mutane su gamu da su a lokaci daya, ballantana ma a ce a rana daya.

Sannan a maganganunmu na yau da kullum, mukan yawaita amfani da kalmar damuwa domin mu nuna cewa muna tare da wata 'yar damuwa, abin da yake daban da damuwa ta tunani, ba ma wadda za ta kai mutum ga kashe kansa ba, wadda duk wanda ya taba gamuwa da damuwa zai iya gaya maka.

Bincike da dama ya nuna cewa idan ka tamabayi mutane yadda suka ji a baya, galibi sukan ce ranar Litinin ita ce rana mafi muni.

Sai dai dogaro a kan abin da mutum zai tuna ya fada maka yawanci ba abu ne da ya fi dacewa a yi amfani da shi ba, a wajen sanin ainahin abin da yake faruwa a zahiri, saboda hakan zai iya sauya cikin sauki bisa tunanin ga yadda mutum yake ganin ya kamata a ce ya ji a wancan lokacin, wanda kila ya manta.

Muna da wata al'ada mai karfin gaske ta kin jinin ranar Litinin, kuma wani nazari da aka yi a kasar Australiya a 2008 ya tabbatar da hakan.

Idan mutane suka duba yanayinsu a baya ranar Litinin ita ce wadda ta fi samun maki kadan (wato ba sa jin dadi a ranar), amma kuma idan a duk rana ake musu tambayar, sai a ga ranar Laraba ce ta fi samun maki kadan.

Wani nazari da aka wallafa a shekara ta 2012 a wata mujalla ta tunanin dan adam (Journal of Positive Psychology), shi ma ya nuna babu wani abu maras kyau a game da ranar Litinin.

Mutane 340,000 ne suka shiga wani bincike na kira ta waya, amma ko da ya ke mutane sun bayyana cewa sun fi jin dadi a ranakun Juma'a, babu wani bambanci da sauran ranakun mako.

Nazarin ya dogara ne a kan mutanen da suke iya tuna ainahin yadda ranar da ta gabata ta kasance a wurinsu, amma binciken ya gano cewa ranar Alhamis din da ta zo musu da wata matsala za ka iya kasance kamar duk wata Litinin da ita ma ta zo musu da wata damuwa, wato babu bambanci, kowace rana ma za ta iya kasancewa da wata matsala.

Saboda haka maganar wata ranar Litininin da ake kira shudiya (ko bakar rana) almara ce kawai, ba ita kadai ba ma hatta batun da ake yi cewa wai ba ma son Litinin (wai ko nasara na tsoronki) magana ce kawai maras tushe. Amma kuma duk da haka ba shakka za mu sake ganin wannan kanun labaran da ake sanya wa a jaridu na wannan Shudiyar Litinin (bakar rana).

Ina jira in ga har zuwa shekara nawa za a ci gaba da yin hakan. Ko ba komai dai kamr yadda wasu suka nuna akalla ta sa mutane na magana a kan damuwa, amma ni dai ban gamsu cewa tana sa mu tattauna a kan lafiyar kwakwalwarmu (tunaninmu), ko wana irin taimako ne ke tattare da hakan ba.

Ina ganin ba abin da take sa mu illa mu yi tunanin cewa watan Janairu ba shi da alheri, alhali kuwa ba abin da ya dame mu, kalau muke.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Does 'Blue Monday' really exist?