Shan jinin mutane matsala ce ko tsafi?

Hakkin mallakar hoto olivia howitt

A yawancin manyan biranen duniya akwai wasu mutane da suka kunshi ma'aikata a kusan kowane fanni kama daga asibiti da kamfanoni da otal-otal, wadanda suke shan jinin mutane akai akai. Me ya sa suke sha?

David Robson ya bincika

A dadaddiyar unguwar nan ta birnin New Orleans (french Quater) da ke Amurka, John Edgar Browning, na shirin shiga abin da suke kira kalaci (shan jini).

Wanda zai sha jinin nasa ya fara ne da goge wurin da zai zuki jinin a bayansa kamar yadda likitoci ke yi idan za su yi wa mutum allura.

Daga nan sai ya tsaga wurin ya rika matsawa har sai da jini ya fara kwararowa. Sai ya tara bakinsa yana shan jinin.

Brown ya ce, ''ya sha jinin ne na dan lokaci sai ya goge wurin da ya huda min jiki ya sa min bandeji.''

Mista Brown ya ji mamakin yadda mutumin da ya sha jinin nasa ya ce, '' jinina wai ba shi da dadi sosai kamar yadda ya yi tsammani.''

Yana ganin yanayin abincin da mutum yake ci da yawan ruwan jikinsa da kuma rukunin jinin nasa su ne ke sa jinin mutum ya yi dandano mai dadi.

Abin da ya faru kenan a kan Browning wanda mai bincike ne a jami'ar jihar Louisiana, a lokacin da ya fara gudanar da bincike kan mutanen da ke shan jinin mutane, inda ya hadu da wani daga cikin mutanen, wanda ya jarraba abin a kansa.

Hakkin mallakar hoto olivia howitt
Image caption Wasu na cewa idan suka sha jinin yana musu maganin tsananin gajiya da ciwon kai da ciwon ciki

To ita wannan dabi'a ta shan jinin mutane, addini ne ko tsafi ko kuma dai mene ne? Kafin Brown ya hadu da ainahin mutanen da suke wannan dabi'a ya dauka mutane ne da suka sauya sakamakon yawan karance-karance na littattafai (Anne Rice) na labaran ban tsoro na masu shan jinin mutane.

A lokacin da ya fara gudanar da binciken sai tunaninsa ya sauya, bayan da ya fara haduwa da irin wadannan mutane na zahiri.

Ya gano cewa mutane ne da ba su da wata alamar tabin hankali ko ma masaniya sosai kan fina-finan Dracula. Maimakon haka suna ikirarin cewa suna fama ne da wata larura ta rashin lafiya ne ta daban, da ta kunshi gajiya da ciwon kai da ciwon ciki, abin da suka yi amanna ta hanyar shan jinin mutane ne za su samu lafiya.

A wurin mutane da dama, shan jinin mutane wani abu ne da ya saba wa al'ada, hasali ma a shekaru da dama ana danganta al'adar da kisan kai na tsabar rashin imani.

Hakkin mallakar hoto olivia howitt
Image caption Ana samun wadannan mutane masu shan jini da suka bayyana kansu a dukkanin fannin rayuwa. Yawanci ma suna da iyali da ayyuka har ma ibada suna yi

A duk lokacin da aka gano masu shan jinin mutane, a yawancin lokaci wannan tunani yakan zo wa mutane rai shi ne kisan gilla, in ji DJ Williams, masani kan zamantakewar dan adam a jami'ar jihar Idaho ta Amurka.

Ya ce, ''saboda haka ne wadannan mutane ba sa bayyana kansu kuma suke dari-dari da sauran jama'a.''

Sakamakon wannan tsangwama, masu wannan al'ada ta shan jinin mutanen da na hadu da su, sun nemi da in sakaya sunansu a wannan rubutun.

To ida dai wannan al'ada a wani lokaci na tarihi ta sha bamban da yadda ake dauka a yanzu, domin akwai lokacin da ake daukar jinin mutum a matsayin wani magani.

Misali a karshen karni na 15 an ce likitan Paparoma Innocent na takwas ya zuke jinin wasu samari uku gaba daya (har suka mutu), ya dura wa mai gidan nasa da ke halin rai kwakwai-mutu-kwakwai da zummar karsashin samartakar tasu zai sa ya farfado.

A wani lokaci kuma an rika amfani da jinin wajen maganin farfadiya, inda ake sa masu fama da larurar su taru inda za a rataye masu laifi, su rika tarar jinin mutanen mai dimi suna sha.

Hakkin mallakar hoto olivia howitt
Image caption Wasu masu shan jinin suna da alakar soyayya da masu ba su jinin

Richard Sugg na jami'ar Durham da ke Ingila, wanda a baya-bayan nan ya rubuta littafi a kan abin da ya kira ''maganin gawa'', wanda kuma a yanzu yake rubuta littafi a kan al'adar ta shan jinin mutane, ya ce, ''jini wata hanya ce tsakanin jiki da ruhi,''

Ya ce, idan ka sha jinin matashi mai koshin lafiya, kana dibar ruhinsa ne kana maganin duk wata cuta da ta damu ruhinka.

An yi watsi da wannan hanya ta magani sakamakon wayar da kai da aka rika yi a karni na 18 da kuma na 19.

Duk da haka al'adar ta ci gaba a tsakanin wasu 'yan kalilan din mutane, wadanda kafin zuwan intanet yawanci a ware suke daga sauran jama'a, wato ba a bayyane suke ba a fili, amma yanzu akwai shafukan intanet da suke amfani da su wajen sanin juna da tafiyar da al'adar tasu a boye.

DJ Willliams ya ce, ''daga abin da muka fahimta a yawancin manyan biranen duniya akwai kungiyoyin wadannan mutane masu shan jinin mutum.''

Wannan tsoro nasu na fitowa fili a sansu ne ya sa Browning ya sha wahala a lokacin da ya fara nazari a kansu. Ya ce, ''wadannan ba fa wai mutane ne da suke son a sansu ba.''

Hakkin mallakar hoto CJ
Image caption Kayan da CJ! take amfani da su wajen shan jinin

A lokacin yana zaune a Baton Rouge a Louisiana, wanda wuri ne da cikin sa'a daya zai je birnin New Orleans a mota, birnin da shi kuma aka san shi da mutane masu al'adu na daban-daban.

A wannan lokacin ne ya yi tunanin cewa inda fa har yana son samun irin wadannan mutane masu shan jinin mutum to fa dama ta samu tun da ya shigo birnin.

Daga nan ne ya fara karade lungu da sako na birnin inda yake zuwa wuraren da yake sa ran samunsu. Ko alama ba tsoronsu a ransa domin, shi ma kato ne da yake ji da karfi.

Hasali ma su masu shan jinin yake ji wa rayuwarsu, domin za ka iya sa a gane su, kamar yadda ya ce, wanda da hakan ka jefa rayuwarsu da aikinsu cikin hadari.

A karshe dai ya samu kansa a wajen wani mai kantin sayar da bakaken tufafi wadanda ke da alaka da mutuwa da sauran abubuwa na batar da kama, wanda ya nuna masa wata mata da ke tare da 'ya'yanta biyu.

Daga nan sai Browning ya je kusa da ita ya yi mata bayani game da binciken da yake yi na masu shan jini, inda ya ce, ''a karshe dai sai ta yi dariya ta ce min 'ina jin na son wasu kadan'''

Ya kara da cewa, ''lokacin da ta yi dariya sai na ga wasu hakoranta biyu kamar fika, masu tsananin tsini.'' Ko da yake daga baya ya bar haduwa da matar, wadda aka sakaya sunanta a matsayin ''Jennifer'', amma wannan haduwa ta karfafa masa gwiwa har a karshe ya kulla kyakkyawar dangantaka da masu al'adar ta shan jinin mutane da yawa, wadanda yake tattaunawa da su sosai.

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Saboda gudun tsangwama wasu masu shan jinin ba sa bari 'yan uwansu su san suna yi

Ga alama, akwai mutane daban-daban masu ayyuka iri-iri da ba ka tsammani wadanda ke wannan dabi'a ta shan jinin mutane, kama daga masu ikirarin bin wani addini zuwa marassa addinin.

Wani daga cikin masu wannan dabi'a wanda aka sauya kira da suna ''Merticus'' domin dalilai na sirri, ya ce, ''su ba wai kawai suna abubuwa da suka shafi dabi'ar tasu ba ne kawai, kamar taruwa a makabarta da haduwa wajen shan jini da wasu tarukansu ba ne kadai.

Akwai kungiyoyinmu da suke taimaka wa gidajen marassa galihu, da shiga aikin ceton dabbobi da sauran ayyukan taimakon jama'a.''

wani abu kuma da ya kamata a sani shi ne, yayin da wasu masu shan jinin ke yin hakan domin samun karfin jiki kamar yadda suke cewa, wasu kuwa suna ganin suna bukatar jinin ne domin maganin wata larura a jikinsu.

Bayan kasala wasu matsalolin da suke cewa na damunsu sun hada da tsananin ciwon kai ko ciwon ciki. Misali wata mata da aka sakaya sunanta da CJ!, kuraje ne ke fito mana a jiki, da har ta sha jinin ta ce suke bacewa.

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Jinin mutum yana da dandano daban-daban, ya danganta da rukunin jinin da irin abincin da mutum ke ci da kuma yawan ruwan da yake sha

Game da yadda suke samun jinin, CJ!, ta ce, galibi masu ba su jinin abokansu ne na kusa, wadanda suka san halin da suke ciki, misali wata mai suna Kinesia tana samun jinin ne daga mijinta bayan 'yan makwanni.

Browning ya ce, wasu sukan biya wanda za su zuki jinin a jikinsa ne, amma dai koma ya abin yake akwai yarda tsakanin mai shan da mai bayarwa.

Kusan dai babu wani hadari a tatare da wannan dabi'a ta su game da ko akwai wata illa da jinin zai iya yi musu a ciki, domin daga cikin wadanda na tattauna da su ba wanda ko kuma wadda ta ce min ga wata larura da ta same su, ko da yake dai ba za a iya kawar da yuwuwar kamuwa da wata cuta ba.

Hanyar da za a fi gane wata larura ko hadari a jikinsu, sai dai a bi ta hanyar tarihi da bayanan lafiyar mutum da ake tattara wa a asibiti.

To amma matsalar wannan kuma ita ce, yawancin masu dabi'ar na fargabar gaya wa likita ko jami'an aikin taimakon jama'a cewa ga abin da suke yi.

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Wasu masu shan jinin mutanen suna fafutukar gano dalilin dabi'ar tasu da kuma yadda za su rabu da ita

Williams wanda ya gudanar da bincike kan tsangwamar da irin mutanen ke iya fuskanta, ya ce akwai wadda ta ce, idan ta gaya wa masu aikin yi wa jama'a hidima cewa, tana da wannan dabi'a ta shan jinin mutane ta san za a kwace mata 'ya'yanta.

Duk da haka wasu daga cikinsu kamar CJ!, suna kokarin fitowa su nuna kansu kamar yadda ita ta sheda wa likitan kayan ciki da kuma na masu tabin hankali abin da take ciki, duka cewa sun karfafa mata gwiwa kan yadda za ta bar dabi'ar, amma ba wanda a cikinsu yake da wata shawara ta yadda za ta bar ta'adar.

Da yawa daga cikin wadanda na tattauna da su, sun nuna a shirye suke su bar dabi'ar, amma kuma sun ce ya zuwa yanzu likitoci ba su sama musu wata hanya da za su yi maganin larurorin da ke sa su shan jinin ba.

Browning ya ce, wannan dabi'a ta shan jini a ganinsa hanya ce da wasu mutane ke jure wa rayuwa da wani hali mai tsanani takurawa, ya yi bayanin cewa, ''abin da ke faruwa da su gaskiya ne. Ba mu fahimci abin ba, kuam su ma ba su san ko menene ba, amma suna kokarin su yi maganinsa.''

Idana kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The people who drink human blood