Motar tantan mai rikidewa zuwa wasu abubuwan

Hakkin mallakar hoto Edgar Andres Sarmiento Garcia

Motar tantan wadda za a iya sauya ta ta zama kanti ko motar asibiti da babur mai kamar jaki da kuma gadon itacen gora mai inji na sufuri a ruwa- shin wadannan su ne irin ababan hawa na kasashe masu tasowa a nan gaba?

Jon Stewart ya yi nazari

Dukkanin wadannan abubuwan sufuri ba an samu tunanin kirkiro su daga manyan fitattun makarun koyon kera abubuwa na duniya ba ne, wasu daga cikin wadanda suka yi tunanin kirkiro abubuwan dalibai ne ma.

Manyan kamfanonin kera ababan hawa ba za su iya barin wadannan sabbin fasahohi da za su iya kawo gagarumin cigaba a fannin rayuwa da dama su wuce kawai ba.

Na'urorin su ne suka yi nasara a gasar da kamfanin Michelin ya shirya kwanan nan a babban taron baje kolin motoci na duniya da ake yi a Detroit.

Kamar yadda BBC ta taba kawo rahoto a kai a baya, wannan basira da kirkire-kirkiren da wadannan dalibai suka zo da su sun bambanta da abubuwan da kamfanonin kera motoci su ke nuna mana, kuma abubuwa ne da za su iya kawo wani sauyi na daban a gaba.

A wannan shekarar daga cikin wadanda suka yi nasara sun hada da wani abin hawa a ruwa da za a iya yi da itacen gora, wanda za a iya amfani da shi idan an samu ambaliya, da tantan (motar gona) mai amfani da intanet, wadda za ta iya nemo ta idan wani bala'i ya faru da kuma wata na'ura mai amfani da hasken rana wadda za ta iya maye gurbin doki.

Taken gasar Michelin din ta bana shi ne, ''Abin hawa ga kowa- zayyanar tsarin abubuwan sufurin zamani na gaba.''

Mai shirya gasar Ben Ebel, ya ce, ''wurare kadan ne a duniya masu zayyana abubuwan sufuri su ke fitowa daga can,'' yana nufin 'yan kalilan din makarantun da ake da su na zayyana.

Hakkin mallakar hoto Rajshekhar Dass and team
Image caption Za a iya tuka motar zuwa kasuwa kuma a mayar da ita kamar shago a kasuwar

Ebel ya ce, ''wani dan karamin wuri ne kamfanonin mota da sauran abubuwan hawa suke samun masu zayyana, amma mun amanna akwai daidaikun mutane masu baiwa, wadanda ba lalle sun halarci wadannan makarantu ba, ko kuma a ce sun fito ne daga Amurka ko Biritaniya da Turai ba.''

Kamfanin Michelin ya ce gasar tasa ta kowa ce, duk wanda yake da sha'awar shiga ko a ina ya ke. Ayyukan zayyanar da suka yi nasara su 14, an zabo su ne daga cikin tarin sama da 875, da suka wakilici kasashe 68.

Me za mu iya fahimta na hasashen yadda yanayin abubuwan hawa ko sufuri za su iya kasancewa a nan gaba, daga wadannan ayyukan zayyana uku da suka yi nasara a gasar?

Motar tantan ko ta karkara wadda Rajshekhar Dass, dalibin ajin karshe na makarantar koyon zayyanar ababan hawa ta DSK ISD da ke Indiya, ya zayyana ita ce ta zo ta daya.

Burin Dass da abokan aikinsa shi ne su kera wata mota domin amfanin al'ummar yankunan karkarar Indiya da ba su da cigaba ba wadda kuma za ta saukaka musu samun fasahar zamani.

Da farko za ka ga motar ta yi kama da tantan da aka saba gani, amma idan ka tsaya ka lura za ka ga an tsara fitilarta ta gaba, yadda za a iya cire ta, a yi amfani da ita kamar fitilar titi ko ta gida.

Ana iya amfani da bodinta ko gidanta na baya ta hanyoyi daban-daban- za a iya amfani da shi wajen sufurin amfanin gona, za a iya mayar da shi kamar shagon kasuwa domin sayar da amfanin gonar. Za kuma a iya sauya shi yadda za a dauki mutane, ta yadda manomi zai iya samun karin kudi a matsasin direban tasi.

To amma kuma a lokacin bukatar gaggawa ne ma motar ta fi ban sha'awa, domin za a hada ta ne da wani abu da ke amfani da balan-balan domin samar da hanyar intanet a yankunan karkara( irin na fasahar Google Project Loon). Idan kuma matukar bukata ta taso ana iya amfani da ita a matsayin motar asibiti.

Hakkin mallakar hoto Edgar Andres Sarmiento Garcia
Image caption An tsara babur din ne ya yi aiki da shiga wurare kamar jaki

''A duk lokacin da muke duba abubuwan da aka gabatar a gasa, muna kokarin kauce wa kawo wani abu na fasahar da kawai a tunani ne za ka iya kawo ta, ba wadda za ka iya aiwatarwa ba nan da nan,'' in ji Ebel.

Wannan fasahar ba ta Google ba ce, amma alkalan sun yaba ne da ita ne ganin cewa an gina ta ne a kan wata fasahar da ake da ita, amma aka kara fadada ta zuwa gaba. Sannan kuma ta jaddada muhimmancin ganin abubuwan hawa na gaba sun kunshi hanyoyin sadarwa ko yada bayanai (intanet).

Shi ma mai zayyanar abin hawan da ya zama na biyu, ya mayar da hankali ne kan aikin gona, amma wannan karon a yankunan karkarar Argentina.

A can an bai wa aikin gona na samar da 'yan kayan amfani matukar muhimmanci ko kuma a ce noma na iyali kusan ba abin da ya fi shi matsayi.

Misali za ka ga suna noman gahawa (kofi), kamar wani dan karamin kamfani, sannan su dauko ta daga yankunasu da dokuna ko jakuna, su ratsa duwatsu da kwazazzabai zuwa wata matattara da ake sarrafa ta.

To shi wannan abin hawa (Arrierio) mai amfani da hasken rana ya yi kama da irin manyan baburan nan ne da ake tafiya da su cikin kwazazzabo da hawa duwatsu.

An bar kayan jikinsa ne tsirara, domin a samu saukin tsara shi daidai yadda ake so da kuma kula da shi a saukake, kuma wanda ya zayyana shi Edgar Andres Sarmiento Garcia naBogota, a Colombia, ya tsara shi ne domin maye gurbin jakuna, domin zai iya ma bin hanyoyi marassa kyau da jakuna ke bi.

''Wannan sauyi ne na wani abin da wani,'' in ji Ebel. ''Wannan ya kawo tambayar cewa, 'shin wannan ya fi wancan ne, ko kuma shi daban yake'?

Wannan abu ne da za a iya kerawa kuma a yi shi daidai da abin da wannan mutumin zai yi da shi, kuma wannan ya nuna zurfin tunani, wanda ni a matsayina na mai zayya na yaba da shi.''

Za a iya cewa abin hawan(Bamboo Recumbent) da ya samu matsayi na uku a gasar kusan shi ne wanda aka fi nuna basira a kansa.

Kirkira ce ta wasu 'yan Koriya ta Kudu su biyu, WooSung Lee da kuma Chan Yeop Jeong, da suka tsara domin mutanen da ke wurare kamar Navota da ke tsakiyar Phillipines.

Hakkin mallakar hoto WooSung Lee and Chan Yeop Jeong
Image caption Za a iya amfani da abin idan ambaliya ta mamaye tituna

Mutane miliyan 25 ne ke zaune a can a yanayi na rashin wadata. Wadannan mutane wadanda ba lalle su iya sayen mota ba, kuma idan an yi ambaliya suna bukatar abin sufuri.

Gurbataccen ruwan ambaliya kan iya mamaye kauyukansu da tulin sharar da ake zubarwa a yankunan. Shi wannan abin sufuri na itacen gora, kayansa na cikin akwati ne, sai dai kawai a fito da su a harhada cikin sauki, kamar wani gadon kara, amma kuma da wasu kafafuwa kamar fanka da ke sa ya yi tafiya a kan ruwa.

Bayan tafiyar a cikin ruwa gadon yana kuma tsaftace ruwan ta hanyar kore sharar da ke ciki yayin da ya ke ratsawa shi.

Duk da cewa wadannan duk fasahar ce kawai a wannan mataki, kuma ba za ka iya sayensu ba, amma abubuwan da suka fito da su fili za su iya tasiri wjen tsarin abubuwan hawa da za a bullo da su a nan gaba.

Ebel ya ce, '' yana ganin dole ne kamfanonin ababan hawa su rika fadada fasaharsu, in dai har suna so su rika samun ciniki a gaba.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. A transforming tractor and mule-like bike