Ka san yadda ake yada jahilci da gangan?

Hakkin mallakar hoto Alamy

Ta yaya ne kamfanoni da mutanen da suke da wata manufa ta amfanin kansu suke yada jahilci da rikitar da ilimi? Georgina Kenyon ta gano cewa wannan abu ne da ake da shi a cikin shi kansa ilimin.

A shekarar 1979 aka gano wata wasikar sirri da kamfanonin taba suka rubuta, wadda aka bayyana wa jama'a. Wasikar (Smoking and Health Proposal), wadda kamfanin taba na Brown & Williamson, ya rubuta shekaru goma baya, ta bayyana dabaru da yawa da manyan kamfanonin taba suka yi amfani da su domin kalubalantar masu yaki da shan taba.

A daya daga cikin sassan takardar, masu dauke da bayanai masu muhimmanci, an tsara yadda za a iya tallata taba ga jama'a.

A bayanin, an ce, ''sanya shakku a kayanmu, tun da shakku hanya ce da ta fi dacewa ta yakar gaskiyar da mutane suka runguma. Haka kuma hanya ce ta haifar da rudani.''

Wannan bayani da aka gano, ya ja hankalin Robert Proctor, masanin tarihin kimiyya daga jami'ar Stanford, wanda ya fara tsunduma cikin bincike kan abubuwan da kamfanonin taba suke yi, da yadda suka yada rudani cikin maganar cewa ko taba tana sa cutar daji ko kuma ba ta yin hakan.

Hakkin mallakar hoto Alamy

Proctor ya gano cewa kamfanonin taba ba sa so masu shan taba su san illarta, saboda haka suka kashe makudan kudade (biliyoyin dala) domin boye gaskiyar illar da taba ke yi wa lafiya.

Wannan bincike ne ya sa har ya kai ga kirkirar wata kalma ta nazarin yadda ake yada jahilci da gangan a harshen Ingilishi, wannan kalma ita ce, ''Agnotology''.

Kalmar dai na nufin, wani fagen ilimi ne da ya kunshi nazarin yadda ake yada rudani da yaudara, musamman domin sayar da wani kaya ko samun goyon baya.

Kuma mai binciken ya kirkiro ta ne ta hanyar hada kalmomin Girkawa na zamanin da, ''agnosis'' wadda ke nufin rashin sani da kuma ''Ontology'' wadda ke nufin wani fage na ilimi na yadda halitta take.

Masanin ya ce,''ina duba yadda manyan ma'aikatu za su iya yada jahilci domin sayar da kayansu. Jahilci ma karfi ne, kuma wannan fagge na ilimi (agnotogy) ya kunshi kirkirar jahilci ne da gangan.

''Ina duba wannan fanni na karatu (agnotolgy), sai na gano sirrin kimiyyar sirri, na ga cewa ya kamata masana tarihi su nazarce shi.

Proctor ya ce, wannan takarda ta 1969 da kuma dabarun da kamfanonin taba suke amfani da su sun zama kyakkyawan misali na yada jahilci domin cimma wata manufa.

''Jahilci ba wai kawai abin da ba ka sani ba ne kadai, dabara ce ta siyasa, wadda wasu (manyan wakilai) manya ke kirkira, wadanda ba sa son ka sani.'' In ji masanin.

Domin ya taimaka masa a binciken da yake yi, Proctor ya gayyato masanin ilimin harshe na jami'ar California (UC Berkeley) Iain Boal, inda suka kirkiro wannan fagen nazari.

Wannan fagen ilimi yana da muhimmaci a yau kamar yadda yake da amfani a lokacin da Proctor, ya yi bincike a kan kutungwilar manyan kamfanonin taba ta boye gaskiyar cewa taba na haddasa cutar daji.

Idan muka duba, misali a yau, abokan hamayya sun dasa shakku bisa dalilai na siyasa a kan kasar Shugaba Barack Obama, tsawon wata da watanni har sai da ya fito da takardar shedarsa ta haihuwa a 2011.

Haka kuma a wani misalin, wasu masu fashin bakin siyasa a Australiya sun yi kokarin sanya tsoro a zukatan mutane, ta hanyar kwatanta matsayin bashin kasar da na Girka, duk da bayanan da hukumomin tantance basuka suka fitar tun a baya cewa akwai bambanci sosai a tsakanin tattalin arzikin kasashen biyu.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Har a yau din nan ana yada jahilci da gangan, ba sai a lokacin da Proctor ya kirkiro wa tsarin suna ba

Proctor ya bayyana cewa wani lokaci za a iya yada jahilci (ta dabara ko a boye) bisa manufar daidaitacciyar muhawara. Misali yadda aka saba cewa wai duk wani ra'ayi ko matsaya akwai kishiyarta, ba a ko da yaushe ne ya ke tabbatar da magana ta hankali da gaskiya ba.

Ta wannan hanya kamfanonin taba suka yi amfani da kimiyya suka sa ake ganin kayansu (taba) ba shi da illa, kuma wannan shi ne abin da masu adawa da sauyin yanayi suke musu da shi a kan shedar kimiyya da ke tabbatar da dumamar yanayi.

Proctor ya ce, ''wannan magana ko ra'ayi na daidaito, ya sa masu yin taba da masu musun matsalar sauyin yanayi a yau, su na ikirarin cewa, duk wani labari yana da fuska biyu, (inda suka fake da haka, suna cewa, 'ai kwararru sun samu sabani, wato kan cewa taba na da illa da kuma cewa yanayi na dumama), da haka suka jirgita gaskiya, saboda haka suka haifar da jahilci.''

Masanin ya kara bayani da cewa, misali da yawa daga cikin nazarin da aka yi da ke danganta sinadaran da ke haddasa cutar daji (carcinogens) a cikin taba, da farko an yi su ne a jikin beraye, to sai masu kamfanonin taba suka mayar da martani da cewa, don an yi bincike an ga cuta ta kama bera, wannan ba ya nufin mutane na cikin hadari, duk kuwa da illolin da aka gani a jikin masu shan taba da dama.

Sabon zamanin jahilci

''A yau muna rayuwa ne a duniyar da ake dora mutane kan jahilcin karfi da yaji, kuma abin mamakin shi ne, kowace irin gaskiya sai ta dage ta iya tabbatar da kanta a san ita gaskiya ce,'' in ji Proctor. Ya kuma kara da gargadi, ''duk da cewa ilimi yana da sauki, hakan ba ya nufin ana samunsa.''

Harwayau dai masanin ya kara da cewa, ''ko da ya ke a kan abubuwa da dama wannan ba wani abu ba ne mai girma, amma a kan muhimman batutuwa na siyasa da falsafa, ilimin da yawanci mutane suke da shi, suna samunsa ne daga addini, ko al'ada ko kuma farfaganda fiye da komai.''

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Idan mutane ba su fahimci wani lamari ba, sai su fada tarkon masu wata manufa ta neman haddasa rudani

Proctor ya gano cewa jahilci yana yaduwa ne da farko idan mutane ba su fahimci wani abu da ake magana a kai ba ko kuma wata gaskiya, kuma na biyu yana yaduwa ne idan wasu kungiyoyi ko mutane masu wani ra'ayi ko manufa, kamar kamfani ko kungiyar siyasa, suka yi aiki tukuru domin haifar da rudani a game da wani batu.

Misali a kan maganar jahilci game da illar taba da dumama ko sauyin yanayi, za a fi rikitar da alummar da ke da jahilcin kimiyya ta hanyar amfani da dabara ko yaudarar da masu son boye gaskiya kan batutuwan suke yi.

Dauki maganar sauyin yanayi a matsayin misali. Proctor ya ce, ''rigimar ba wai a kan akwai sauyin yanayin ba ne ko babu, magana ce a kan ko Ubangiji ya halicci duniya domin mu yi yadda muka ga dama da ita ne, da ko gwamnati na da ikon sanya ido da kula da ayyukan masana'antu (kada su wuce gona da iri), da ko za a karfafa wa masu rajin kare muhalli gwiwa da ba su iko da kuma sauran batutuwa.

Ba magana ce a kan gaskiyar cewa akwai wannan matsala ta sauyin yanayi da sauran matsaloli na tattare da ita ba, magana ce ta abin da ake tunani zai fito daga wannan lamari (gaskiya) da kuma wanda zai shiga ciki. In ji Proctor.

Yanke shawara

Wani malamin da shi ma ya ke nazarin jahilci, shi ne David Dunning daga jami'ar Cornell. Malamin ya yi gargadin cewa intanet ma na taimaka wa wajen yada jahilci.

Ya ce, wuri ne inda kowa ya ke da damar zama gwanin kansa, wanda hakan ke jefa mutum cikin hadarin gamuwa da masu son yada jahilci da niyya.

Ya kara da cewa, ''yayin da wasu mutanen masu lura za su amfana da bayanan da ke intanet din cikin sauki, za a batar da wasu da yawa ta yarda za su dauka cewa su kwararru ne yanzu, suna da ilimi, sun san komai.

Damuwata ba wai yanzu ba ma yanke shawara ko daukar matsaya ba ne kan wani abu ba, a'a, yanzu cikin sauki mu ke yin hakan. Wanda kamata ya yi a ce muna tuntubar wasu kafin mu yanke shawara.

Ba shakka, su ma wadanda za mu tuntuba din suna da irin rauni ko gazawarsu, amma yawanci ra'ayinsu zai iya taimaka mana wajen gyara namu kuren, kamar yadda kurenmu su ma zai taimaka musu gyara nasu.'' In ji Dunning kamar yadda ya ke ba da shawara ko gargadi.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Bayanan Trump na maganace matsaloli wadanda ba masu yuwuwa ba ne ko sun saba wa tsarin mulki kyakkyawan misali ne na yada jahilci da gangan domin wata manufa

Matakan mai neman takarar shugabancin Amurka na jam'iyyar Republican Donald Trump, na magance matsaloli wadanda ko dai ba masu yiwuwa ba ne ko kuma sun saba kundin tsarin mulkin Amurka misali ne na yada jahilci da gangan domin wata manufa, in ji Dunning

Dunning da Proctor sun kuma yi gargadin cewa wannan dabi'a ta yada jahilci da gangan ta mamaye yakin neman takarar shugabancin Amurka na dukkanin manyan jami'yyu biyu na kasar.

Dunning ya ce, ''Donald Trump, shi ne babban misali a Amurka, inda ya ke gabatar da hanyoyi masu sauki na magance matsaloli ga magoya baya, hanyoyin da ko dai ba masu yuwuwa ba ne ko kuma sun saba wa tsarin mulki.''

Duk da cewa wannan fagen ilimi na nazarin yada jahilci da gangan domin wata manufa (agnotology), tun a lokacin farko na bunkasar kamfanonin taba ya samo asali, har zuwa yau din nan akwai bukatar yin magana a kansa da kuma nazari a kan jahilcin dan adam matuka ainun.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The man who studies the spread of ignorance