Ya za ka faɗi alamar @ a harshenka?

Hakkin mallakar hoto iStock

Muna amfani da alamar @ wadda Ray Tomlinson wanda ya mutu yana da shekara 74, ya kirkiro, a wasikar email da sauran wurare. Tom Chatfield ya duba yadda duniya ke amfani da alamar wadda kowa ke kiranta da sunaye iri daban-daban masu ban sha'awa da ban haushi, da yadda ta samo asali tun shekarun 1500.

Magana a game da wannan alama ta @ za ta fi armashi da ban sha'awa idan ba da Turancin Ingilishi kake magana ba. Kundin bayanai na Wikipedia ya jera sama da sunaye 50 na alamar @ a harsuna daban-daban, waɗanda da yawa daga cikinsu fassara ce ta kamanni misali na wata dabba.

Mutanen Armenia suna kiran alamar ishnik ma'ana dan kwikwiyo ( ya tsuguna a ƙasa, ina jin). Al'ummar China na da nasu sunayen iri-iri da suka hada da xiao Iaoshu a Taiwan, ma'ana ''ɗan bera'' da quan ei a ainahin cikin ƙasar China, wanda shi kuma ke nufin ''kewayayyar A''

Su kuwa mutanen ƙasar Denmark sun zaɓi su kira ta da snabela ma'ana ''hannun giwa A'', yayin da su kuwa mutanen Jamus ke kiran alamar da klammeraffe, abin da ke nufin ''birin da ya kanannaɗe''.

Mutanen Hungary na kiranta da kukac, ma'ana ''tsutsa'', su kuwa Italiyawa sun ba ta suna chiocciola wanda ke nufin ''dodon koɗi''.

Al'ummar Kazakhstan suna ganin alamar ne a matsayin ''kunnen wata'', idan kuwa kai mutumin Girka ne kana kiranta ne da papaki, ma'ana, ''yar ƙaramar agwagwa.''

Hakkin mallakar hoto iStock

Akwai kuma wadanda suka ba alamar sunayen da ba na dabbobi ba ne a harsunansu. Misali a Bosnia ana kiranta da ludo A wato ''mahaukacin harafin A'', yayin da a Turkiyya aka ba ta sunan guzel wato ''kyakkyawar A''

Na yi rubutu dan taƙaitacce a kan tarihin wannan alama ta @ wadda ake amfani da ita a wasiƙar email a littafina mai suna ''Netymology'', amma idan ana maganar cikakken bayani ne ba inda ya fi shafin intanet na Keith Houston mai suna ''Shady Characters'', inda aka yi bayani mai ban sha'awa na tarihin yadda a 1971, ƙwararren injiniyan kwamfuta ɗan shekara 29, mai suna Ray Tomlinson, ya ƙirƙiro alamar.

Tomlinson ya mutu yana da shekara 74, a ranar biyar ga watan Maris na 2016.

Wannan alama kyakkyawan zabi ne da Tomlinson ya yi, domin ba inda aka taɓa amfani da ita a aikin kwamfuta, da kuma ganin cewa tunani da ya dace da aikawa da saƙon email zuwa wani mutum a wani sashe na daban.

Tun kafin Tomlinson ya ƙirƙiro wannan alama ana yin wasiƙar email, sai dai saƙo ne da ake yi tsakanin mutane da suke amfani a fagen kwamfuta daya, ko gida daya, maimakon daga wannan matattara zuwa waccan.

A da ana amfani da @ a Ingilishi yawanci a matsayin alama a lissafin akanta, inda take nuna kudi ko farashin kaya.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Harsuna da dama suna da yadda suke kiran wannan alama

Alamar @ ta zarta yadda Tomlinson ya yi tsammani, kamar yadda misali Houston, ya bayyana, inda misali aka yi amfani da ita a wata wasiƙa a watan Mayu na shekara ta 1536, inda wani ɗan kasuwa na Florentine wanda ake kira Francesco Lapi, ya yi amfani da ita domin nuna farashin wasu kaya.

A nan akwai alamar alaƙa ta zahiri tsakanin kalmar harshen Spaniya na zamanin nan da na Portugal, dukkaninsu na alamar @ da kuma alamar lissafin nauyi , arroba, da kuma maɗaukin da aka zuba abin da ake maganar nauyin nasa, wato amphora (kamar kwalba), wadda mutanen Girka da Rumawa na zamanin da suke amfani da ita domin sufurin abubuwa na ruwa (musamman barasa).

Dukkanin wannan dogon tarihi ya kawo mu kan maganar email da dodon-koɗi da sauransu. Ko da yake ni a wurina abin ya ƙara nuna mana tarihin yadda aka samar da wannan alama ta kan kwamfutata a gaggauce.

Abin da zan iya cewa na zamanin tarihin da ne aka ɗauko shi aka karkaɗe masa ƙura aka ba shi muhimmin wuri a wannan zamani, har ya kasance babban mabuɗin musayar sako a zamanin yau.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How do you say @ in other languages?