Ko cin ɗumame na da haɗari?

Hakkin mallakar hoto iStock

Ɗumama abinci musamman na kanti abu ne da za ka ga lalle ya dace musamman idan abincin ya jima a ajiye, amma mutane da yawa sun fahimci haɗarin da ke tattare da hakan kuwa?

Kusan mutane miliyan ɗaya ne a Biritaniya suke gamuwa da matsalar gurɓatar ciki a sakamakon cin abinci mai guba a duk shekara, kuma hakan na faruwa ne saboda mutane ba sa bin wasu 'yan matakai ne masu sauƙi.

Micheal Mosley na wani shirin talabijin mai suna ''Trust Me I'm a Doctor'' ya bayyana cewa dabarar da ya kamata a yi ita ce, a tabbatar an ɗumama abinci ( a na'urar dumame ta microwave ko rusho) ya kai har zafin lamba 82 a ma'aunin celcius domin tabbatar ka kashe duk wata ƙwayar halittar bakteriya mai cutarwa.

Wannan dai abu ne da za a iya ɗauka mai sauƙi amma kuma ba haka lamarin yake ba, domin za ka ga a lokacin dumama abincin sai ka ga jikin kwanon yana tururi (ya yi zafi), amma kuma cikin abincin bai yi zafi ba, saboda haka ne ya kamata a jujjuya abincin ta yadda zafin zai ratsa ko'ina.

Kuma ko da ka bi wadannan matakan, to kada ka ɗumama abinci fiye da sau daya, domin a duk lokacin da ka bari ya huce, kana ba wa ƙwayoyin halittu masu cutarwa na bakteriya dama su ninninka.

Wannan ya ke sa da wuya ka iya kashe su gaba daya a duk lokacin da ka sake sanya abincin a cikin na'u'rar dumama abincin (microwave ko rusho).

Shinkafa musamman ita ce ta fi wannan matsala, saboda tana iya tara irin wannan halittu na bakteriya masu illa (Bacillus cereus). Ita wannan bakteriya idan ta shiga abinci, ta kan fitar da guba wadda ke haddasa amai da gudawa.

Abin takaicin wannan guba tana jure wa zafi, domin ko da ka dumama shinkafar ta yadda duk kwayoyin halittar na bakteriya za su mutu, ita gubar tana nan, kuma nan da nan za ka ga illar cin gubar.

Saboda haka idan kana son adana ragowar shinkafarka, to ka tabbatar ka fara sanyaya ta da sauri, ka sa ta a firji (fridge), sa'a daya da dafa ta, tun kafin ƙwayoyin bakteriyar su fara sanya wannan guba. Idan ba haka ba to kana kasada ne da cikinka kawai, in ji Mosley.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. This is what you need to know about reheating takeaways