Ka san abin da lemon tsami zai iya bayyanawa a kanka?

Hakkin mallakar hoto Getty

Shin kana haɗa yawu idan ka ga ana shan lemon tsami? Amsar hakan na iya bayyana yanayinka maimakon bayyana ɗanɗanonka na abubuwa masu tsami.

Christian Jarrett ya yi nazari

Kana jin kai mutum ne wanda ba shi da rufi ko surutu ne (extravert), ko kuma mai zurfin ciki (introvert)? Domin amsa wannan tambaya kana buƙatar ka duba ka yi tunanin yadda kake sha'awar zuwa wuraren liyafa da magana da baƙi, ko kuma ƙila tuni ma ka samu amsa daga ire-iren abubuwan kacici-kacici da ake yi ta intanet, waɗanda ke sa a san yanayin mutum (mai magana ko maras magana).

Matsalar irin waɗannan hanyoyi na sanin yanayin mutum, ita ce sun dogara ne ga bayanai na gaskiya da kuma tarin ra'ayi. Wataƙila kai mutum ne mai son zuwa liyafa misali, amma ko kusa ba ka kai babban abokinka ba, to wannan zai sa ace kai mutum ne mai haba-haba da ta'ammali da jama'a ko kuma a'a?

Wata hanya ta daban ta sanin wannan amsa, ita ce ta amfani da lemon tsami, musamman ma ruwan lemon tsamin. Wannan hanya ce ta bincike mai daɗaɗɗen tarihi wajen sanin yanayin mutum, kuma hanya ce mai sauƙi da za ka iya gwadawa a gida.

Za ka samu auduga ne ka ɗaura mata zare a tsakiya. Bayan ka yi haka, sai ka sanya ɓangare ɗaya na audugar a kan harshenka har tsawon daƙiƙa 20. Sai kuma ka kawo ruwan lemon tsamin nan ka yi ɗigo biyar a harshen naka, ka haɗiye, sannan kuma ka sa ɗaya ɓangaren audugar a kan harshen naka shi ma na tsawon daƙiƙa 20.

A ƙarshe sai ka fitar da audugar daga bakinka, ka duba ka gani ko ba wani ɓangare da zai rinjayi wani na audugar ko kuma ɓangaren da ka sanya a bakinka lokacin da ka ɗiga ruwan lemon tsamin ne zai rinjayi ɗayan saboda ya fi nauyi.

Idan ɓangaren da ka sa baki bayan ka ɗiga lemon ya rinjaya wato ya fi nauyi, hakan ya nuna cewa ruwan lemon ya sa bakinka yawu sosai, wanda wannan alama ce da ke nuna kai mutum ne mai zurfin ciki (wanda ba a sanin abin da yake ciki).

Idan kuma audugar ta kasance daidai wato wannan ɓangare bai rinjayi ɗayan ba, wannan ya nuna cewa wannan lemon tsami bai yi wani tasiri sosai a kanka ba kenan, hakan ya nuna ƙila kai maras zurfin ciki ne, wato mai surutu ko sakin jiki da jama'a.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Masu zurfin ciki sun fi nuna alama sosai ga wani abin jan hankali kamar tsamin lemo

To ya wannan abu yake? Wannan wani nau'i ne na gwaji da ɗaya daga cikin masana kimiyyar yanayin mutum na farko-farko Hans Eysenck, tare da matarsa kuma abokiyar bincikensa Sybil Eysenck, suka bayyana tun a shekarun 1960.

A ainahin gwajin da masanan biyu suka yi na farko, sun yi amfani da sikeli maras rena nauyi domin sanin yawan yawun da audugar ke tsotsa kafin da kuma bayan da aka ba mutane ruwan lemon tsamin ko kuma suka ga lemon tsamin. To amma wannan nau'in na yanzu mai sauƙi (DIY) masani Brian Little, ne ya ɓullo da shi a littafinsa na 2014 mai suna Me, Myself and Us.

Shi Eysencks da matarsa suna son su gwada wata nazariyya ce ta rashin zurfin ciki (extraversion) da zurfin ciki (introversion). A kan haka ne masanin ya ce yana ganin wannan yanayin na mutum yana da wata dangantaka da halayya ko al'adar jikin mutum, inda mutum mai zurfin ciki jikinsa ke saurin sauyawa idan ya ji wani abu na jan hankali.

A takaice jikinsu na da saurin jin wani abu sosai da sosai, wanda hakan ga alama ke sa su kauracewa ko janye jikinsu daga yin wani abu. Masanan biyu (mata da miji) suka ce wannan gwaji na lemon tsami ya tabbatar da wannan nazariyya tasu, saboda mutanen da suke samun maki mai yawa a tambayoyin da ake musu na tantance masu zurfin ciki bakinsu ya fi yin yawu idan aka ba su ruwan lemon tsami.

Duk da cewa ba shakka shi kansa wannan gwaji na yawu da lemon tsami akwai wasu abubuwan da suke haddasa wannan zurfin ciki ko rashin zurfin ciki wanda zai iya haɗawa da gadon yanayin daga iyaye, a yanzu dai mun san cewa wannan nazariyya ba kashi dari bisa dari take gaskiya ba.

Duk da cewa har yanzu wannan gwaji na lemon tsami abu ne da ake da muhawara a kansa wajen tabbatar da cewa zai iya tabbatar da zurfin cikinka daidai, to amma ko ba komai ya nuna mana wani abu mai muhimmanci a kan jikinmu, kuma za ka iya ci gaba da jarraba wannan gwaji har ka samu sakamako mai kyau.

To koma dai mene ne ba halayyar zurfin ciki ko rashinta za a iya gwadawa da wannan hanya ta amfani da lemon tsami ba kawai. Wata ƙasida da aka rubuta a 2014 ta nuna cewa za a iya amfani da wannan tsari na gwaji da lemon tsami a ga irin yadda mutum ke jin tausayin mutanen da ke wani hali mawuyaci.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hamma na da ƙarfin yaɗuwa tsakanin mutane- Waɗanda suka fi tausayi na da saurin kamuwa da ita

Domin samun gwajin da zai fi bayar da bayani na gaskiya Florence Hagenmuller, da abokan aikinta sun sa wasu mutane (waɗanda aka yi gwaji da su) sanya mulmulen auduga uku a baki domin ganin yawan yawun da za su yi, inda aka sanya musu wani hoton bidiyo na minti biyu.

Hoto ɗaya na nuna wani mutum yana yanka lemon tsami yana sha, ɗaya kuma yana nuna mutumin yana ɗauko wasu ƙwallaye daga cikin wani bokiti yana ɗora su a kan tebur.

Daga baya sai masana kimiyyar suka duba mulmulen audugar uku, kowacce suka duba yadda ta jiƙe da yawu, sai suka ga audugar da ke bakin mutanen lokacin da mutumin yake yanka lemon tsamin nan yana sha ta fi yawu da yawa.

Wannan shi ne kusan irin abin da ke faruwa idan muna kwaikwayon juna kan yanayin da muke ciki, kamar idan muna hamma ko mun ga wani yana hamma ko kuma idan mun ga wani ya ji ciwo.

Hagen Muller, da abokan nazarinta sun ce wannan hanyar ta gwaji da lemon tsami tana da muhimmanci sosai , misali wajen sanin yadda wasu mutanen ke nuna tausayi kan wasu, mutanen da ba za a iya yi musu wasu tambayoyi ba saboda suna da wata larura, kamar galhanga (dolaye-dolaye).

Kuma wannan hanya ce ta gwaji da ba ta bukatar wata fahimta ta wasu abubuwa a kan wanda za a yi gwajin da shi, illa kawai ya sa audugar nan a bakinsa kawai, ya zauna ya kalli hoton bidiyon.

To daga yanzu kana da zabi idan ka samu kanka da ledar lemon tsami a wurinka. Kana iya hada ruwan lemon tsami ka sha ko kuma ka jarraba gwajin kimiyya ta sanin wani abu na tunanin ɗan adam. Ban san abin da shawararka za ta nuna game da yanayin halayyarka ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. What can a lemon tell you about your personality?