Facebook ya zama katafariyar maƙabarta

Hakkin mallakar hoto Getty

Zuwa wani lokaci Facebook zai kasance da matattun masu amfani da shi da suka fi masu rai yawa, domin a kullum 8, 000 ne ke mutuwa, kuma ga waɗanda za su kai lokacin abin zai sauya yadda muke ɗaukar mutuwar 'yan uwanmu.

Ga binciken Brandon Ambrosino

Kwana daya da mutuwar gwaggona, na gano wani rubutu na kauna da ta yi min a bangon wani littafi na rubuce-rubucen Shakespeare da ta ba ni. Ta ce, '' na san yadda wannan rubutu yake da muhimmanci a wurinka, saboda haka wannan ita ce kyautata a gareka.'' Ta kammala rubutun da , ''Ina kaunarka kamar ko da yaushe''. Ni ce Gwagggonka Jackie.

Hakkin mallakar hoto Getty

Cikin jimami, na kunna kwamfutata ta tafi-da-gidanka na shiga shafinta na Facebook. Na dauka zan ji saukin jimamin rashinta idan na ga hotunanta, na kuma ga irin rubuce-rubucenta, in ga kamar ga ta a raye tana wadannan maganganu da salon harshen 'yan Baltimore.

A saman abubuwan shafinta na Facebook wani hoton bidiyo ne da dan uwana ya sanya na wasu giwaye biyu da suke wasa a ruwa.( Gwaggon tawa na sha'awar giwaye).

A kasan bidiyon sakonni ne na ta'aziyyar mutuwarta daga tsoffin dalibanta, da kuma ta'aziyyar da 'yar uwar mijinta ta sa a shafin. Daga nan sai na koma saman shafin.

Kamar yadda bayaninta na Facebook ya nuna, Anti Jackie ta karanci harshen Turanci a fannin koyarwa a jami'ar jihar Frostburg, tsohuwar shugabar sashen koyar da Turanci ce ta makarantun Baltimore City, kuma tana zaune ne a Baltimore, a Maryland.

Tana zaune? Na yi tunani.

Ba inda take zaune. Ta rasu.

To amma fa idan ka ga bayananta a Facebook, kuma ya kasance ba ka je can kasa ka ga wannan ta'aziyya ba, to ba za ka san ta mutu ba.

A wurinka me rai ce tana nan a wani wuri. A Facebook.

Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Yawan masu mutuwa na Facebook na karuwa sosai: sun kai miliyan 30

Na tuna da daren da ni da sauran iyalan gidanmu muka kewaye ta, duk wayoyi da na'u'rori a jikinta, muna gani ta rasu.

Ta yaya cigaba da kasancewarmu a shafukan sada zumunta na intanet ke sauya yadda muke rasuwa? Nazarin wannan lamari bakon abu ne.

Ga ta nan, wadda kake matukar kauna- ga ta kana magana da ita, kana rike da hannunta, kana gode mata kan yadda ta kula da kai, kana ganin yadda take shudewa a hankali a hankali, a karshe sai kawai ka ga ba sauranta.

A yayin da hakan ta kasance, can kuma ga wata na'ura tana nunawa cewa tana da rai: wata nau'rar rumbun bayanan kwamfuta da ke wata uwa duniya, tattare da maganganunta da rubuce-rubucenta da abokan mu'amullarta.

Duk da cewa a fili take mutane ba sa mutuwa su bar jikinsu a raye a bisa tsarin fasahohin zamani, amma suna dorewa zuwa wani lokaci a wani fannin.

Yadda mutane suke daukanka a matsayin mai rai zai iya ci gaba kuma yana ci gaba a intanet. Ta yaya cigaba da kasancewarmu a shafukan intanet ke sauya yadda muke mutuwa? Kuma me hakan ke nufi ga wadanda za su yi makokinmu bayan mun tafi?

Hakkin mallakar hoto Getty

Yawan mutanen da suka mutu a Facebook na karuwa sosai. Zuwa shekara ta 2012, shekara takwas kawai bayan kirkiro da shafin, masu amfani da shafin miliyan 30 sun mutu. Kuma tun wannan lokacin yawan ya karu, wasu alkaluman sun ce sama da masu amfani da shafin 8,000 ne ke rasuwa kullum.

Za a kai wani lokaci da matattun masu amfani da Facebook suka fi masu rai yawa. Facebook makabarta ce ta intanet da ke ci gaba da girma ba kakkautawa.

Shafukan Facebook na mutane da yawa da suka mutu suna nuna sun mutu (kasar da ake rijistar wadanda suka mutu), inda ake ganin kalmar ingilishi ta ''remembering'' (tunawa), kuma na daina ganinsu a wasu fannonin na Facebook da ke tunatarwa a game da mutum, kamar zagayowar ranar haihuwar mutum, da jerin mutanen da kila ka sani.

Sai dai ba dukkanin masu amfani da Facebook din da suka mutu ba ne ake sanin sun rasu. Daya daga cikin 'yan dakinmu a lokacin da muke makaranta, Kerry, a 'yan shekarun da suka gabata ya kashe kansa, amma kuma matarsa da 'yan uwansa da abokansa na ci gaba da aika sakonni da rubuce-rubuce a shafinsa na Facebook.

Wannan ya sa Kerry da Gwaggona Jackie suna nan da ransu a Facebook, da kuma wurin duk wanda ya gamu da wani abu daga shafinsu na Facebook, wanda bai san sun mutu ba a zahiri.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Haduwa da wanda ya mutu a Facebook kamar gargadi ne cewa kai ma lokacinka na tafe

A da wasu manya ko fitattun mutane ne kawai suke da damar barin wani abu na tarihi, ko dai saboda sun yi rubutu sun ajiye domin 'ya'ya da jikokinsu ko kuma saboda wasu masu son sanin kwakwaf sun yi bincike a kansu.

Amma yanzu fasaha ta sauya duka wannan. A yanzu kowannenmu a kowane mako yana daukar sa'o'i masu yawa sama da 12 kamar yadda wani bincike ya nuna, muna rubuta bayanan tarihin rayuwarmu a shafukan sada zumunta da muhawara da sauran kafofi na intanet.

A yanzu dai ba wata hanya ta maganin wannan matsala ta cigaba da kasancewar tarin bayanan mutanen da suka mutu, a shafin Facebook, a matsayin wadanda suke da rai har bayan gushewarsu. Fata daya kawai shi ne a ce zuwa wani lokaci kwakwalwar intanet za ta fara gushewa, ta fara manta abubuwa.

Amma Jorge Luis Borges ya ce,''gaskiyar magana ita ce, dukkanninmu muna rayuwa ne ta hanyar barin wani abu na tarihi.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Facebook is a growing and unstoppable digital graveyard