An kirkiro motar da zuciya ke tukawa

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Za a iya tuƙa wata mota a Jamus da isharar zuciya ko tunani kaɗai. Rose Eveleth ta tambayi direban motar da ayarinsa game da irin ƙwarewar da ake buƙata mutum ya samu har ya iya sarrafa ta.

Henrik Matzke yana zaune a gaban sitiyarin wata mota, yana shirin ya yi tukin da ba a taba gani ba. Motar ta tsaya a wata mahada. Sai ya tsaya ya natsu zuwa wani dan lokaci, yana son motar ta yi kwana. Sai kawai sitiyarin ya juya, motar ta yi kwana hannun dama, ka kama tafiya.

Hannunsa yana kan cinyarsa, Matzkedai yana tuka wannan mota ne da zuciya kadai, kuma da gudun kaiwa kilomita 50 cikin sa'a daya.

Yana daga cikin ayarin kwararru ne a jami'ar Free University ta Berlin da ke Jamus, wadanda suke aiki a kan abin da suka kira kwakwalwa-direba, fasahar da suke fatan kirkirowa wadda za ta rika karantawa da kuma fassara sakon kwakwalwa ko abin da zuciyar mutum ke rayawa tana gaya wa mota da kuma gida .

Ya za a ga yadda zuciyarka za ta sarrafa mota mai nauyin tan daya da rabi?

Abin da ya haifar da tunanin kirkirar motar da za a rika tukawa da zuciya, shi ne samar da fasahar da wani nakasasshe zai iya amfani da ita ya shiga ko'ina yadda yake so.

Bayan mota, ayarin masanan ya kuma kirkiro fasahar keken guragu. Na'urar da za ta rika amfani da wannan fasaha ta tuki da zuciya za ta bai wa mai ita damar tuka ta ne ta hanyar rayawa da zuciyarsa cewa yana son ta yi hannun hagu ko dama ko kuma ta mike.

To amma tabbatar da wannan fasaha a zahiri abu ne mai wuya ba kadan ba. Adalberto Llarena, kwararre a fannin kirkirar yaro-ba-kiwa (mutum-mutumi mai kwamfuta), wanda yake cikin ayarin da ya dukufa kirkiro fasahar, ya ce, a yanzu suna fuskantar kalubale biyu ne; kirkirar kwamfutar da za ta yi aikin da kuma mutanen.

A bangaren kwamfutar ya ce, suna kokarin kirkiro wata na'ura ne da za ta rika sauraron tunanin da kwakwalwar mutum ke yi, ta fassara su zuwa sakon da na'ura za ta yi amfani da shi.

A bangaren mutum kuwa, za su kirkiro wani abu ne wanda mutane na gaske za su koyi amfani da shi.

Hakkin mallakar hoto Brain Driver project

Wannan na'ura da za a kirkira za ta kunshi abin da za a daura a ka ne wanda ke da wasu maballai 16 da za a lika a kan mutum suna lura da irin sakon da kwakwalwa ke bayarwa.

''Abin zai zama kamar za mu sanya abin magana ne (microphone) a wani wuri can kuma a wani wurin muna kokarin sauraron muryoyin mutane miliyan daya kowa na surutu.'' In ji Llarena.

Matzke ya ce, ''Ni dai a bangarena abu ne mai sauki, '' wannan magana ta sa sauran abokan aikin nasa, suka barke da dariya. Ya ce, ''Suna dariya ne saboda basu gane yadda abin yake ba.''

Kuma wannan shi ne kalubale na mutum a wannan aiki, ta yadda za ka sa abu kamar wannan ya yi aiki, wato ka horar da kwakwalwarka ta rika samar da sakonnin da na'ura za ta fassara, wanda abu ne mai wuyar gaske.

Shi kansa Matzke wanda ya fi kwarin gwiwa a cikin 'yan ayarin, ya ce sai da ya yi watanni kafin ya samu kwarin gwiwar da ya yi amfani da mota ko keken guragu masu gwajin wannan fasaha.

Ya ce, '' Na samu kwarin gwiwa kusan kashi 70 mcikin dari, amma abu ne mai wuya ka shiga mota ka ce kana da kwarin gwiwa kashi 70 cikin dari.''

Bayan da ya yi watanni yana gwaji ne ya iya shiga motar ya kewaya a wani tsohon filin jirgin sama, inda babu hadarin wani karo, ko da wani tunani na daban zai ratso zuciyarsa ( ba a yarda a yi amfani da motar ba a kan titinan gari, idan ana tuka ta da zuciya).

Ba abin da ya dame shi game da kwarewa, domin cewa ya yi, ''Ba wani abu ne na daban ba, saboda tuni mun riga mun kirkiro mota maras direba, mai tuka kanta.

Saboda haka idan kana zaune a cikin motar da take tuka kanta, ba zai zama wani bakon abu ba a ce ka tuka motar da zuciyarka .''

A yanzu akwai kalubale, domin ba a kai ga yadda za a fassara sakonnin da kwakwalwa ko zuciya ke fitarwa ba, ba ta yadda za ka dan yi kwana dama kadan ko hagu kadan, babu kuma yadda za ka sa ta, ta yi tafiya gaba daidai da gudun da kake so.

Haka kuma kana bukatar ka natsu sosai sannan ka saki jikinka yayin da kake tuka ta.

Hakkin mallakar hoto Brain Driver
Image caption A wannan tsohon filin jirgin saman aka jarraba tuƙa motar

Irin wannan kalubalen tuni ya harzuka masu amfani da hannayen roba da ke aiki da zuciya kamar wannan fasahar da ake son a kirkiro ta mota, domin mutum na bukatar watanni na amfani da su kafin ya saba, su kuma mutanen suna ganin ba za su iya jure wa hakan ba, suna jin sun gaji, saboda haka suka ajiye hannayen robar.

Llaren na kokarin kauce wa irin kalubalen saboda haka ya ke kokarin saukaka abin a akan wannan mota da suke son kirkirowa da za a rika tukawa da zuciya. Ba za ta dogara sosai a kan karbar umarni daga kwakwalwa ba kacokan, za ta rika barin kwakwalwa ta zabi wuri, sai kuma ita motar ko kujera (mai wannan fasaha ) ta yi sauran aikin tafiyar.

Saboda haka maimakon mutum ya rika sarrafa motar ko kujerar (a cikin gida), a kowace kusurwa ko kwana, mutun zai yi tunanin zuwa dakin girki ne ko bandaki kawai sai ita kujerar ta shiga aikin kai shi wurin kawai, haka ita ma motar.

Wani kwararre kan yadda kwakwalwa ke karbar sakonni, wanda ke aiki a Llarena, Omar Mendoza, ya ce, dasa 'yan mitsi-mitsin na'urori a kwakwalwa zai iya sa a samu saukin sarrafa motar ko kujerar.

Sai dai ya ce, ko da yake hatta mutane masu nakasa sosai ba lalle ba ne su yarda a yi musu aikin sanya wadannan 'yan na'urori a kwakwalwa ba.

Hakkin mallakar hoto USAFAl Bright
Image caption Sam Schmidt na tuka motar tserensa ne da motsin kai da ciza hakora kawai

Llarena da ayarinsa ba su kadai ba ne ke kokarin kirkiro motoci da kujeru domin amfanin mutanen da ba za su iya tuka su ba da jiki sai da tunani ba, domin a 'yan shekarun da suka gabata, kamfanin Toyota ya yi aiki a kan wannan fasaha.

Haka kuma a kwanan nan wasu kwararrun sun kirkirowa wani tsohon dan wasan tseren motoci da ya nakasa a hannuwansa da kafofinsa gaba daya, ba ya iya tuki, wata fasaha da a yanzu yake iya tuka mota da ita ta hanyar karkata kansa da kuma ciza hakoransa, maimakon amfani da tunani, kamar na wannan sabuwar da ake son kirkirowa.

A yanzu dai ba wanda yake da shirin barin motar da ke aiki da tunanin mutum hawa titi, ko sakin kujerar da zuciya za ta rika sarrafa ta a cikin. Kafin a kai ga hakan, ana bukatar fasaha mai sauki da za a yi hakan, da kuma fasahar da za ta sarrafa su, da zarar wani abu ya dauke wa direba hankali ko kuma ya rude.

A bangare daya muna da wannan tsari, a daya bangaren kuma muna mutanen da ke bukatar wadannan abubuwa, amma kuma a tsakiya muna da matsalar, wannan shi ne gibin da ba shakka muke bukatar cikewa a nan gaba, kafin ka ga mota da tunanin mutum ke tuka ta, ta zo ta sha gabanka a titi.

Kawo yanzu a duniyan nan Matzke ne daya daga cikin 'yan mutanen da suka hau titi da zuciyarsu kadai (suka jarraba mota mai wannan fasaha).

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Mind-control: 'I drove a car with my thoughts'