Ko ka san illar sakacen kunne?

Hakkin mallakar hoto spl

Maikon da ake sakatowa daga kunne wanda aka fi sani da dauɗar kunne, aba ce da babu wata masaniya sosai a kanta. Kashe ƙwayoyin cuta ne amfaninta ko kuma me? Waɗanne irin abubuwa ne dauɗar ta ƙunsa? Ka san hadarin sakace ta daga kunne?

Babbar dabbar nan ta ruwa da ake iya kira giwar ruwa (whales a Ingilishi), ba ta goge daudar kunnenta. Duk tsawon rayuwar wannan dabba ba ta sakacen kunnenta da sunan fitar da wannan dauda, har ta taru cunkus a kunnenta, dauke da sinadarai iri daban-daban.

Wannan dauda tana taruwa a kunnuwn dabbobi masu shayarwa da yawa, har da mu mutane. Ba kamar sauran dabbobi ba, yawancinmu muna fitar da wannan daudar kunne kusan ko da yaushe.

Ita wannan dauda wasu sassan jiki na mutum kusan dubu daya zuwa dubu biyu (wadanda ke kanka, wadanda kuma ke taimaka wa gashinka da maiko) da kuma halittun da ke samar da gumi ne ke samar da ita.

Da dadewa ana ganin amfanin daudar shi ne, sa miko a kunnen, ta yadda abubuwan cikin kunnen za su fi tafiyar da aikinsu sosai (kamar yadda mai da akan diga a misali keken dinki ko wasu na'urori ke taimaka musu), wannan ne ma ya sa ake amfani da ita daudar kunnen wajen yin man lebe a da.

Haka kuma an ganin daudar na da amfani wajen kare kwari daga shiga can cikin kanka ta hanyar kunnen. Wasu masanan kuwa suna ganin tana amfani a matsayin maganin kashe kwayoyin cuta.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dauɗar kunnen wasunmu ruwa-ruwa ce wasu kuma tana da kauri

A shekarar 1980 wasu masu binciken kimiyya (NIH), Tuu-Jyi da Toby C Chai, sun tattara daudar kunnen wasu mutane 12, suka hada ta a cikin ruwan sinadarin barasa.

Daga nan kuma sai suka sanya wasu kwayoyin bakteriya da ke yada cuta, a cikin ruwan, inda sinadarin ya kashe kwayoyin bakteriyar kashi 99 cikin dari, duk da cewa dai wasu kwayoyin ba su mutu ba.

A wani nazarin da aka yi a kasar Jamus, a 2011 shi ma an samu irin wannan sakamakon, inda aka gano cewa sinadarai goma a cikin daudar suna hana wasu kwayoyin cuta na bakteriya da makamantansu girma.

Masu binciken sun ce idan garkuwar da ke cikin wannan daudar kunne ta karye shi ne kunne ke kamuwa da cuta.

Sai dai kuma a shekarar 2000, wani bincike da aka yi a jami'ar La Laguna, da ke Canary Islands (Tsiburan Kanari), an gano kishiyar hakan ne, inda masu binciken suka gano cewa daudar na karfafa bunkasar kwayoyin cuta na bakteriya, saboda irin sinadaran abincin da bakteriyar ke so.

Wannan ba shi kadai ba ne binciken da ya nuna shakku a kan maganar cewa daudar kunne na kashe kwayoyin cuta na bakteriya ba.

Akwai abu daya da zai iya bayar da haske a kan bambancin da wadannan bincike-bincike suka gabatar. Shi binciken 1980 da na 2011 sun yi amfani ne daudar kunne busasshiya.

Shi kuwa binciken na shekara ta 2000, ya mayar da hankali ne kan amfani da daudar kunne mai ruwa-ruwa.

Hakkin mallakar hoto science photo library
Image caption Wanke kunne da sinadari mai ruwa na fitar da dauɗa da yawa ba tare da illata kunnen ba.

Kasancewar daudar kunnenka busasshiya ko kuma mai ruwa, abu ne da ya dogara ga wata kwayar halitta daya, wadda ake kira ABCC11, kuma idan kana da mai harafi 'A' maimakon mai 'G', to sai taka ta zama busasshiya.

Haka kuma kanshi ko warin daudar ya bambanta tsakanin busasshiyar da kuma mai ruwan, wadda ita ce ta fi yawa.

Ana kuma iya yin hasashen asalin kaurar mutanen zamanin da ta hanyar yanayin daudar kunnen. 'yan asalin Turai ko Afrika sun fi kasancewa da dauda mai ruwa.

Su kuwa 'yan asalin gabashin Asiya, an fi samunsu da daudar kunnen busasshiya. Akwai kuma daidaito a bambaci tsakanin nau'ukan biya a mutanen yankin Pacific da tsakiyar Asiya da tsirarun kabilun Asiya da 'yan asalin Amurka da kuma mutanen Canada da Alaska.

Babban abin da ya fi damun yawancinmu a kan daudar kunne, shi ne yadda za mu fitar da ita, kuma wannan shi ne abin da ya fi damun dan adam tun lokacin karni na farko.

A littafinsa De Medicina, daya daga cikin sarkin sarakunan daular Rumawa, Cornelius Celsus, ya bayar da wasu shawarwari na yadda mutum zai fitar da wannan dauda daga kunnensa.

Ya rubuta cewa, ''idan busasshiya ce, sai a zuba mai me dumi, ko wani ruwa da ake samu a jikin jan karfe (copper), ko farin karfe (brass), ko tagulla (bronze) , a hada da zuma ko ruwan lemo a cikin zuma.'' Da zarar daudar ta narke, sai a sa ruwa a wanko ta.

Amma kuma idan daudar mai ruwa ce, ya ce, '' sai a yi amfani da ruwan sinadari da ake kira 'vinegar' wanda aka hada da wani ruwan 'ya'yan itace mai daci da ake kira 'soda' a zuba a kunnen, idan daudar ta tsinke, sai a wanko ta waje.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Har yanzu likitoci na amfani da man zaitun wurin wanke dauɗar kunne

Duka dai wadannan bayanai shawarwari ne, kuma hatta a zamanin yau likitoci za su iya amfani da man zaitun su zuba a kunnen daudar ta yi laushi kafin a wanko ta.

Wasu mutanen na gamuwa da cutukan da ke da nasaba da daudar kunne, wadanda ke bukatar daukar mataki a kai. Kamar yadda wani nazari a 2004 ya nuna, kusan mutane miliyan biyu da dubu 300 ne a Biritaniya suke zuwa wajen likita a kowace shekara saboda wadannan cutuka, kuma kunnuwa miliyan hudu ake yi wa magani a duk shekara.

Masu binciken suka ce, ita daudar da kanta ba za ta huda tantanin kunnen mutum ba, amma kuma yayin da mutum ke kokarin sakace daudar ta haka sai ya huda tantanin, wato ya yi wa kansa rauni kenan.

Saboda hadarin da ke tattare da amfani da tsinke mai auduga a nannade wajen sakatar kunne yana da yawa, hatta kwararrun ma'aikatan lafiya sai sun zuba ruwan sinadari ya sa daudar ta yi ruwa ko laushi sannan su wanko ta.

A shekara ta 2012, Anjali Vaidya da Diane J Madlon-Kay, masu bincike a makarantar koyon aikin likita a jami'ar Minnesota ta Amurka, sun ce amfani da ruwa mai sinadari wajen wankewa ko sa daudar ta yi laushi, ko kuma sauran hanyoyi na hannu na sakace daudar dukkaninsu suna aiki, kuma ba wata hanya da za a ce ta fi wata amfani ko rashin hadari.

Amma dai dukkanin wadannan hanyoyi ne da ya fi dacewa a bari kwararrun ma'aikatan lafiya su yi wa mutum, ba shi da kansa ya yi ba.

Duk da irin gargadin da ake yi wa mutane, za ka ga wasu da sun fito daga wanka sai su sa tsinke da auduga suna sakatar kunnensu, wanda hakan kuskure ne da zai iya sa mutum ya huda tantanin cikin kunnensa, ko kuma ya tura audugar cikin kunnensa.

Wasu ma don kasada ko rashin kiyayewa tsinke ko wani abu mai tsini za ka ga suna sakatar kunnen nasu da shi. Idan har mutum yana son shafa wa kansa lafiya, to ya daina wannan dabi'u, ba ma amfani da abubuwa masu tsininba hatta ma audugar.

Haka kuma kada ka sake ka yi amfani da wani tsari na gargajiya da ake bi na amfani da harshen wuta wajen karawa a kofar kunne, har wutar ta sa daudar ta narke ta rika zubowa (ear candling da Ingilishi).

Idan kunne ya ji jiki ya tsira

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The mysterious properties of the wax in your ear