Fasahar jirgin sama ta ɗauki sabon salo

Hakkin mallakar hoto National University of Singapore

Kana son bulaguro a jirgin sama amma kana ganin tsohon yayi ne? To wasu ɗaliban Singapore sun samar maka mafita da wani ɗan karamin jirgi na kai kaɗai.

Zamanin jirgin sama maras matuki ya kankama, inda ake amfani da shi kusan a komai daga aikewa da sakonnin kaya zuwa aikin ceto.

Idan gwajin da ake yi a yanzu ya yi nasara, to jirgin sama maras matuki da ake gani a yau zai zama tsohon yayi, inda samfurin jirgin mai daukar mutum ko kuma wanda zai dauki fasinja wani mutum kuma na sarrafa shi daga kasa, zai zama abin yayi kuma.

Shi ma dai zai rika amfani da lantarki ne kamar jirgi maras matukin da aka sani, amma kuma shi ba kamar maras matukin ba ne, wani abu ne sabo daban.

Hakkin mallakar hoto Getty

Wasu dalibai a jami'ar Singapore ta kasa (National University of Singapore), sun dukufa aikin kirkirowa wannan sabon nau'in jirgi mai daukar mutum daya, mai suna 'Snowstorm' da Ingilishi.

Shi wannan sabon jirgi da ake kokarin kirkirowa ya yi kama da wani sanfuri na jirgin da aka sani maras matuki (drone). Jirgin yana da kira da kusurwowi takwas, da kuma na'urori masu juyawa 24.

Matukin jirgin yana kasa, kuma daga kasansa giyar saukar da jirgin take, sannan jirgin yana da tayoyin sauka masu kamar kwallo da ake hura wa iska, ta yadda zai iya sauka ba tare da ya girgiza ba sosai.

Ayarin dalibai takwas ne cikin shekara daya ya kirkiro jirgin wanda a yanzu zai dauki mutum daya mai nauyin kilogram 70, ya yi shawagi da shi na tsawon minti biyar.

Wannan dan takaitaccen lokaci da jirgin ke iya shawagi na nufin ba lalle ya iya kai yawancin mutane wurin aiki daga gidajensu ba, amma daliban sun ce a wannan matakin na kirarsa suna dukarsa a matsayin abin shakatawa a cikin gida, maimakon abin hawan da zai maye gurbin motoci na zirga-zirgar yau da kullum.

Farfesa Martin Henz wanda ya taimaka wajen lura da aikin kirkirar jirgin ya ce, '' muna ganin kirkirar jiragen shakatawa ta kai lokacin da za a samu sauyi inda jiragen za su rika amfani da lantarki. Muna son gnin cewa mun taka rawa a wajen samar da wannan cigaba. Kuma wannan jirgi shi ne matakinmu na farko. Wannan abu ne mai ban sha'awa.''

Wannan sabon samfurin jirgi ba wai yana sarrafa kansa ba ne gaba daya, yana amfani da wata manhaja ta kwamfuta domin sarrafa kansa da kansa.

Mutumin kuma da ke kansa shi zai rika sarrafa tafiyarsa da kuma wurin da zai nufa. Idan jirgin ya gamu da matsala, abubuwansa suka daina aiki, to akwai wata masarrafa wadda mutanen da ke kula da jirgin a doron kasa suke lura da ita, wadda ta hanyarta za su katse tafiyar jirgin su sauko da shi kasa, kuma ana sa ran a saukake.

A yanzu ayarin na shirin nuna wa jama'a irin cigaban da suka samu kawo yanzu. Lokaci na gaba da za mu ga wannan jirgi yana tashi shi ne a lokacin taron 'foundres Formu a Landan, a watan Yuni na 2016.

Henz, ya ce, ''mun samu karin tallafin kudi domin inganta wannan fasaha, wadda a yanzu muke aikinta da kuma jarrabawa.''

Hakkin mallakar hoto National University of Singapore

Ba wannan jirgin ne ba kadai ake sa ran kirkirowa da wannan fasaha. Misali kamfanin Ehang na China a kwanan nan ya dauki hankalin duniya lokacin da ya nun wani jirginsa maras matuki, wanda yake iya daukar mutum.

Jirgin mai suna Ehang 184 an tsara shi ta yadda zai iya daukar mutum zuwa nisan kilomita 16 ko tsawon minti 23, kuma shi yake sarrafa kansa da kansa.

Har yanzu akwai wasu matsaloli ko kalubalan da za a magance kafin jirgin na China, ya zama an kammala shi, yadda za a iya sa shi a kasuwa.

Henzu ya ce a watan Mayu muke shirin gudanar da gagaruin gwaji na jirgin, kuma za mu horar da matukan jirgin da za a yi wa tambayoyin yadda aikin jirgin zai kasance.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Is this a totally new kind of aircraft?