Za ka iya ba baƙo hayar motarka?

Dalilan da suke sa mu sayi mota a yau, ba lalle su zama waɗanda za mu sa yi mota saboda su ba a shekaru masu zuwa. BBC ta gana da mai tsara motocin kamfanin Ford, wadda ke fafutukar hasashen yadda yanayin hawa mota zai kasance a 2050.

Ga nazarin Jack Stewart

Yawancinmu da muke da motoci, motocin sun shiga ranmu matuka. Ba za mu iya rayuwa ba tare da su ba. Amma a zahirin gaskiya, wadannan motoci da suka shiga ranmu suna shafe kashi 95 cikin dari na lokacinsu a ajiye ne a gefen titi ko kuma a dakin ajiya (gareji).

To yanzu ka yi tunanin yadda wani zai ce maka, zai mayar da motarka sabuwa fil kuma a kyauta, ba tare da ka biya ko da sisin kwabo ba. Ya za ka ji?

Da walakin goro a miya, ba shakka. Za ka yadda ka rika karba-karbar motar taka da bako, ka rika ba baki hayar motar a duk lokacin da suke so?

Wannan shi ne abin da ake gabatarwa wasu daidaikun masu mota a wasu birane. Wannan zai iya shafar yadda muke sayen motoci da yadda muke amfani da su a shekarun da ke tafe.

Hakkin mallakar hoto Ford
Image caption Me kamfanin Fodi (Ford) zai mayar da hankalinsa a kai nan gaba?

Haka kuma wannan ne irin abin da Sheryl Connelly, shugabar tsare-tsare ta kamfanin motoci na Ford take tunani kusan a kullum, ba wai maganar irin motocin da mutane za su so saye ba a shekara biyu mai zuwa, sai dai ko ma mutane za su bukaci mota ma nan da shekara 20 mai zuwa.

Tsarin ba wa bako hayar motar shi ne abin da ake dubawa a yanzu, inda aka gayyaji wasu masu mota dubu 12 na birnin Landan da kuma wasu dubu 14 daga birane bakwai a Amurka, domin su bayar da lokacin suke bukatar a bayar da hayar motocin nasu, kamar yadda ake yi a tsarin bayar da haya na Zipcar.

Hakan wani tsari ne da ake son a bullo da shi ta yadda masu motar za su samu isassun kudaden da za su biya ko kula da motocin nasu, kuma su yi amfani da motocin kyauta a duk lokacin da suke da bukatarsu.

Yawancin motoci suna ajiye ne kawai ba tare da yin wani aiki ba, kuma ga shi sun tsare wuri. Saboda haka bayar da hayarsu zai zama wani amfani, sai dai maganar ba wa wani bako ko mutumin da ba su sani ba motarsu abu ne da ba za su yarda da shi ba.

A halin da ake ciki tsarin hayar motoci na zamani kamar su 'easyCar Club' ko 'Uber' ko 'lyft' zai zama gama-gari. Kuma ga alama matasa za su zama ba su damu da mota ba sosai kamar yadda iyayenmu suka damu.

Connelly ta ce, ''idan da zan tambayi mutumin da ya wuce shekara 30 'menene ma'anar sufuri a wurinka?' zai iya cewa abin hawa.'' Sanna kuma ta ce, ''idan da zan tambayi mutumin da bai kai shekara 30 da haihuwa ba 'menene ma'anar sufuri a wurinka?' da wuya bai ce wayar salula ba.''

Hakkin mallakar hoto ford
Image caption Titunan gobe za su ga fasaha iri-iri ciki har da motoci masu magana da junansu

Aikin Connelly dai shi ne ta duba ta hangi irin kalubale da kuma inda ra'ayinmu zai karkata a shekaru masu zuwa a kan sufuri ta taimaka wa daya daga cikin manyan kamfanonin motoci na duniya (Ford) ta yadda za a ci gaba da damawa da shi a duniya.

Mun tambayi Connelly ba wai kan yadda take ganin al'amuran sufuri za su kasance ba a nan gaba, har ma yadda harkokin za su sauya.

Sai ta ce, '' muna magana akan shekara biyu, biyar, 10, 15, 25, saboda haka ni ina tunanin shekara ta 2050, wadda tana gab da zuwa, amma kuma za ta bambanta matuka da yadda duniya take a yau.

A yau yawan al'ummar duniya biliyan bakwai ne, amma zuwa shekara ta 2050 ana kiyasin yawan zi kai biliyan tara

Hakkin mallakar hoto Ford
Image caption Dakin kimiyya na kamfanin Ford da ke Slicon Valley na nuna yadda fasahar kwamfuta ke da muhimmanci ga motocin zamani mai zuwa

Ta ce, ''cunkoson mutane zai karu, birane za su karu manyan birane za su karu. Zuwa shekara ta 2015 zirga-zirgar da mutum zai yia mota a Beijing matuka na sa'a biyar ne. Saboda haka idan ka kara karin biliyoyin mutane, ya za ka ga yadda abin zai baci?''

Jami'ar ta ce wannan ne ya sa dole mu duba mu sake tsarin al'amuranmu, rayuwa ba za ta cigaba da kasancewa yadda take ba yanzu.

Za a daina daukar mota a matsayin wani abin ado, ko na matsayi, za ta zama kamar wani abu ne na biyan bukata na wani lokaci kawai, kamar kayan amfanin gida irin su tsani ko abin sharar daki.

Wannan tsari na bayar da motar mutum haya a lokacin da ba shi da aikin da zai yi da ita, zai sa mutum ya rika duba hanya mafi sauki da araha ta zirga-zirgarsa, ba tare da ya gamu da cunkoson ababan hawa ba.

Zai iya kasancewa mu yi hayar keke, ko babur zuwa tashar da motar hayar take, mu dauke ta hayar tsawon sa'a daya, sanna mu dawo gida ta hanyar kiran motar mutumin da ba mu sani ba ta mahajar kwanfuta.

Wannan sauyi ne da zai shafi kamfanonin kera motoci su kansu. To wannan sauyin shi ne Connelly take fatan ganin kamfanin na Ford ya shirya wa tun kafin ya zo.

Ta ce, ''ko da mun dauki mota a matsayin wani abu na bukata daga lokaci zuwa lokaci kawai, ta yaya za mu tsara ta yadda za ta dace da sha'awarmu da tsarinmu ko ra'ayinmu, kuma yadda za ta biya mana bukata?

Wannan na nufin dukkaninmu za mu iya amfana da sauye-sauyen da ake kawowa a fannin fasahar kere-kere da kuma manyan masana'antun sufuri, amma fa sai in mun yarda cewa sauyi yana aukuwa.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cunkoso a kan titunan biranen China za su ƙara yawa

Connelly ba ta son ta bayyana takamaimai yadda za mu kai ga tsara motocinmu a nan gaba daidai da yadda za su dace da ra'ayinmu ko bukatarmu, amma wannan sauyi ne wanda shi ma ba shakka ana iya hasashensa ko da kuwa ba mu mallaki motocinmu na kanmu ba.

Motar da za a rika bayar da hayarta a bisa wancan tsarin da muka ambata za a rika yi nan gaba za ta iya kasancewa da fasahar da za ta rika sauya kanta ga yadda ra'ayin direbanta yake.

Wannan zai kasance kenan, da zarar ka bude motar sai sitiyari da kujerarta su matsa daidai da yadda kake bukata. Ita ma rediyonta sai ta koma kan tsarin tashoshin da ka tsara da dai sauran abubuwa na motar duka sai su koma yadda kai ka tsara su daidai da sha'awarka.

A can gaba kuma za a kai ga yadda hatta siffa da launin motar za su sauya, su koma daidai da yadda ka tsara ta. Wai don ba ka mallaki jar mota kirar Ferrari a 2015 ba, hakan ba yana nufin ba za ka iya sauya siffar motar da ka dauka haya ba ta juye ta zama jar Ferrarin ba.

Sauya yanayin fitulun motar na waje zai iya sa sauran masu mota a hanya su dauke ka mai kaunarsu ko kuma akasin haka.

Wadannan na daga irin abubuwan da masu sayen mota a yanzu suke la'akari da su, idan za su sayi mota, amma masu tuka motocin da za su zo a shekarun gaba za su iya sauya yadda suke son motar da za su hau ta kasance a kullum.

Maganar ita ce, shin za su so hakan?

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Would you let a stranger rent your car?