Ka san sunayen da ke lalata kwamfuta?

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt

Wasu mutane suna da sunayen da ke rikita shafukan intanet da suke ziyarta, kuma hakan na ba su matsala da sa su damuwa a duk lokacin da suka shiga intanet. Ko menene dalilin hakan?

Ga bayanin binciken Chris Baraniuk

Mijin Jennifer Null ya gargade ta kafin su yi aure cewa idan ta sa sunansa a cikin sunanta, abin zai rika haddasa mata matsala a harkokinta na rayuwar yau da kullum.

Saboda haka ta san irin abin da za ta fuskanta, wanda wannan ne ma ya sa danginsa suke tsokanarta a kan lamarin ko da yaushe. Kuma kamar da kasa yin aurensu ke da wuya sai matsalar ta fara kunno kai.

Ta fara ganin matsalar ne a zahiri bayan da ta sauya sunanta inda ta hada da na mijin nata (Null) bayan sun yi aure, a lokacin da za ta sayi tikitin jirgin sama ta a yawancin shafukan intanet.

Ta ce, ''a wurin cike takardar sayen tikitin, idan na saka sunan mijina wato Null a gurbin inda ya kamata na sa sunan nasa, sai shafin ya ce min na bar gurbin ba suna saboda haka na sake cike wurin.

Abin ya kan ci tura sai dai ta kira kamfanin jirgin ta waya ta sayi tikitin, amma kuma duk da haka matsalar ba ta kare ba fa.

'' Kamfanonin sukan tambaye ni me ya sa sai na kira su ta waya zan sayi tikiti, idan kuma na yi kokarin yi musu bayani, sai a ce min 'ba ta yadda haka za ta faru,' in ji ta.''

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Takardun da akae cikewa ta intanet ba sa yarda da mutanen da ke da suna daya ko suna na biyu (namahaifi ko miji) mai harafi daya kawai

Ga duk wani masanin hada aikin kwanfuka, zai iya sanin dalilin abin da ya sa kalmar ''Null'' ta ke haddasa wa manhajar kwamfutoci mai rumbu ko matattarar bayanai (database) matsala.

Wannan na faruwa ne saboda kamfuta na daukar kalmar ''null'' a matsayin wurin da ba komai. Hakan ne ya sa masu tsara ayyukan kwanfuta suke kokarin gyara matsalar a kan mutanen da ke da suna ''Null'', sai dai abu ne da ba sosai yake faruwa ba kuma abin mamaki yana da wahalar magancewa.

Matsalar Madam Null, wadda uwa ce da ke zaune a kudancin Virginia a Amurka, ba ta tsaya ba ne a kan maganar sayen tikitin jirgin sama ba ne kawai, tana kuma da matsala wajen cike sunanta a takardar biyan haraji ta intanet.

Sannan lokacin da ita da mijinta suka koma wani gari, sun samu matsala wajen samar musu takardar biyan kudin wuta da ruwa da sauran abubuwa na gida.

''Null''ba shi kadai ba ne misalin sunan da kwamfuta ke da matsala da shi. Akwai wasu da dama. A wannan zamani da aka dogara da bayanai daga matattara ko runbunan bayanai na kwamfuta kafin abu ya yi aiki, matsalar mutanen da ke da wani suna mai wuyar sha'ani na kara tsananta ne kawai.

Wasu mutanen suna da suna daya ne kawai. Wasu kuwa sunansu na biyu (misali na uba ko miji) harafi daya ne kawai. An samu rahotannin irin wadannan matsalolin tun kafin yanzu.

Ka dauki misalin matsalar Janice Keihanaikukauakahihulihe' ekahaunaele, wata mata 'yar Hawaii wadda ta yi korafi cewa kamata ya yi katin shedar mutum na gwamnati ya zama yana daukar sunan mutum ta yadda zai nuna sunasa na biyu ko da ya kai nata mai harufa 36.

A karshe dai shafukan kwamfuta na abubuwan da suka shafi gwamnati an gyara su ta yadda za su iya karbar wasu sunayen da ake samun matsala da su.

A tsarin aikin kwamfuta matsaloli irin wadannan ana kiransu ''edge cases'', ma'ana matsalolin da ba a tsammaninsu wadanda kuma ba a tsara kwamfuta ta yadda za ta san su ba.

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Masu sunayen da kwamfuta ba ta sani ba sai sun yi amfani da tarho wajen fayyace bayanansu

Wani masanin kwanfuta Patrick Mckenzie ya ce, ''yanzu a duk shekara ana sake tsarin kwamfutoci, kuma ana jarraba su da bayanai daban-daban, da suka hada da sunaye da ake da su da yawa a tsakanin jama'a.''

Meckenzie yana da sha'awa a kan yadda kwamfutocin da dama suke samun matsala a kan wasu sunaye. Wannan ne ya sa ya shirya jerin matsalolin da masu tsara aikin kwanfuta yawanci ba sa hange lokacin da suke tsara rumbun adana sunayen mutane.

Shi kansa Meckenzien sheda ne na yadda wannan matsala take, domin a wurin yawancin 'yan yammacin duniya, masu magana da Ingilishi, sunan ''Patrick Mckenzie'' ba sa daukar zai iya kawo matsala, amma kuma inda shi MecKenzie yake zaune, Japan, sunan ya haddasa masa matsaloli daban-daban.

Yadda kwamfuta ke mamaye ayyuka a duniya, ana muhawara sosai a tsakanin masu tsara ayyukan kwamfuta domin shigar da wasu sunayen da kwamfuta ba ta sansu ba.

Ya ce, ''suna mai harufa hudu a Japan abu ne da ba kasafai ake samu ba. MecKenzie kuwa harufa takwas ne, saboda haka a takardun da ake bugawa a kwamfuta wadanda mutane ke cikewa (forms) domin wasu abubuwa na hukuma, su MecKenzie za su rika gamuwa da matsalar cewa babu isasshen wurin rubuta sunana.''

''Ana tsara kwanfutoci yawanci tare da la'akari da irin wadannan takardu da ake cikewa, kowace shekara idan zan cike takardar biyan harajina, sai dai in sa suna a matsayin 'mckenzie P' saboda wannan shi ne iya gurbin da aka ware wa sunayen.''

MeCkenzie ya yi iya kokarinsa domin sunan nasa ya samu shiga. Har sai da ya sauya sunansa zuwa katakana (wani harafa na Japan wanda yake bayar da damar rubuta sunayen kalmomin kasashen waje), to amma lokacin da aka sabunta kwamfutocin bankinsa sai aka cire wannan tsari na wannan kalma ta katakana.

Wannan ba abu ne da zai haifar da wata matsala ga masu mu'amulla da bankuna da sauran harkokin kasuwanci na Japan ba, amma a wurin McKenzie, hakan na nufin ba zai iya amfani da shafin intanet na bankin nasa ba, na wani dan lokaci.

Hakkin mallakar hoto Olivia Howitt
Image caption Sunan Null na nufin gurbin da ba komai a shafin kwanfuta

''A karshe dai sai da suka rubuta wa sashen kula da abubuwan da suka shafi kwamfuta na shalkwatar bankin namu kafin a sa wani ya gyara tsarin sannan na iya amfani da shafin intanet na bankin,'' in ji McKenzie.

Ga mutane irin su Null ga alama za su ci gaba da karo da matsala zuwa wani lokaci mai tsawo. Wasu na za su iya cewa wadanda suke da suna ye masu matsala kila su yi tunanin sauya sunansu domin saukaka wa kansu.

To amma Null ba ta daga cikin wadannan muatnen domin tuni ita ta riga ta sauya sunanta lokacin da ta yi aure. Ta ce, '' abu ne mai ban takaici a duk lokacin da ka ci karo da shi, amma ni daman tuni na riga na saba ma da hakan yanzu.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. These unlucky people have names that break computers