Ka san cewa mutanen Japan ba sa barci?

Hakkin mallakar hoto Adrian Storey Uchujin

Mutanen Japan ba sa barci. Suna abin da suke kira 'inemuri', wanda ke nufin barci a tsaitsaye wato a lokacin aiki ko a mota ko jirgi a cikin mutane, yayin zuwa aiki ko wani wuri.

Dakta Brigitte Steger ta bayyana.

'Yan Japan ba sa barci. Wannan shi ne abin da kowa yake fada, musamman ma su Japanawan kansu. Ba shakka wannan dai magana ce kawai, amma ba gaskiya ba ne. Amma dai idan ana magana ne ta al'ada da zamantakewa, batu ne mai ban sha'awa.

Na fara ganin wannan dabi'a ta Japanawa ne a kan barci a lokacin da na fara zuwa kasar a karshen shekarun 1980. A lokacin Japan tana kan ganiyar abin da ya zama a yau tattalin arzikin da zai ba da mamaki, wanda wani yanayi ne na hasashen bunkasarsa a lokacin.

Rayuwar yau da kullum na cike da fafutuka da kalubale. Mutane ba su da wani sukuni, daga aiki sai halartar wata liyafa, kusan ba su da wani lokaci na barci.

Yanayin rayuwar lokacin ya dace da wani take da ake yi, na wani abin sha na kara kuzari, wanda ake cewa, ''za ka iya gwagwarmaya tsawon sa'o'i 24? Da kuma Dan kasuwa! Dan kasuwa! Dan kasuwar Japan!''

Yawanci suna wannan korafi: ''Mu 'yan Japan mun cika aiki ba ji ba gani.!'' To amma kuma a wannan korafi da suke yi, za ka gano cewa, suna alfahari da kasancewarsu mutane masu kwazo da gaskiya fiye da sauran al'ummar duniya.

Amma kuma duk da haka na ga mutane bila adadin suna barci a cikin jirgin kasa na karkashin kasa a kai komon da nake yi a kullum a kasar. Wasu ma suna barcin ne a tsaye, kuma sai ka ga ba ma wanda yake mamakin abin.

Hakkin mallakar hoto Adrian Storey Uchujin
Image caption Wata ma'aikaciya a Japan na barci a matattakala

Na dauki wannan al'ada sabanin abin da Japanawan ke nunawa. Al'adar mutumin da aka san gwarzon aiki ne, wanda ba ya barci da daddare, kuma ya tsani ganin ana barci da sassafe, ga alama ta hadu da dabi'ar barci a cikin mota da jirgin kasa, da kuma lokacin tarukan aiki, da lokacin darasi a aji.

Kusan mata da maza da yara ba su damu barci ya dauke su ba a duk lokaci da kuma inda suka ji barcin.

Idan za a dauki barci a kan gado ko wata katifa ta tafi-da-gidanka alamar lalaci, ko me za a dauki barci a yayin wani taro ko aiki ko kuma a aji lokacin darasi?

Menene amfanin a hana yara barci, su kai tsakar dare suna karatu, amma da safe su je aji suna barci lokacin darasi? Wadannan dabi'u ko al'ada da sabanin da nake ganin na tattare da dabi'un su suka sa na zabi na yi karatun digirina na uku a kan barci shekaru da dama a gaba.

Da farko sai da na yi gwagwarmaya ta yakar mutanen da suke ganin barci ai ba wani abu ne mai muhimmanci da ke bukatar wani nazari a kansa ba musamman digiri na uku. To amma wadannan dabi'u ne suka ja hankalina.

Za a iya kasancewa da ma'ana da manufa da yawa. Daga abin da na fahimta, abubuwa na yau da kullum da kuma na yadda rayuwar mutum take, wadanda mutane ba sa la'akari da su, wadanda kuma suke bayyana muhimman tsare-tsare da al'adar al'umma.

Hakkin mallakar hoto Adrian Storey Uchujin
Image caption Wani ma'aikaci a Japan na ƙailula a wurin aiki

Yawanci mun dauka cewa bisa al'ada kakanninmu suna kwanciya ne idan dare ya yi, sannan kuma su tashi idan gari ya waye. To amma ware lokacin barci ba abu ne mai sauki haka ba a Japan da sauran wasu wuraren.

Tun kafin a kirkiro wutar lantarki, shedar da ake da ita ta nuna cewa ana yi wa wadanda basu kwanta da daddare ba, suka yi dare suna hira da shaye-shaye da sauran abubuwa na jin dadi.

Sai dai ana ganin kima da martabar daliban wani lokaci na da a Japan din (young Samurai), idan suk katse barcinsu domin su yi karatu da daddare, duk da cew wannan al'ada ba lalle ta samu gindin zama ba sosai domin suna bukatar tanadin man da za su zuba a fitilunsu, kuma yawanci tana sa su barci a aji lokacin koyon karatu.

Ba kasfai ake maganar barci ba a tarihi, kuma kusan abu ne ma da ba a ba shi muhimmanci ba. A kan yi maganar mutum idan barci ya dauke shi a yayin wani taro ko wani abu a bainar jama'a, domin dariya.

Haka kuma mutane suna tsokanar wanda yake gyangyadi ko barci a cikin jama'a, inda za ka ga ana sa masa wani abu a jiki domin a firgita shi ko ya yi wani abu da zai sa mutane dariya.

Maganar manya su kwant d yara kuw domin wi hakan na sa yaran su zama masu dogaro da kansu da kuma zama nutsattsu, idan sun girma abu ne da likitoci suka yi gum da bakinsu a kai.

Tashi daga barci da wuri, a daya hannun abu ne da ya samu karbuwa, akalla tun lokacin bullar wasu addinai. A zamanin da, wasu bayanai sun nuna yadda aka ba wa tsarin aikin ma'aikata muhimmanci, amma kuma a gaba-gaba sai ya kasance wannan al'ada ta tashi da wuri ta shafi kusan duk wani fanni na rayuwa, inda ake daukar dabi'ar jinkirin kwanciya da kuma tashi da wuri da matukar muhimmanci.

Wani bu mai ban sha'a wa kuma shi ne barci tare. A Burtaniya, galibi ana gaya wa iyaye cewa su sama wa hatta 'yan kananan 'ya'yansu dakunansu daban, domin su koyi barci su kadai, domin su iya yin tsarin lokacin barcinsu yadda suke so.

Amma kuma sabanin hakan, a Japan iyaye da likitoci ba su damu da maganar barci tare da 'ya'ya ba, har sai 'ya'yan sun kai shekarun shiga makaranta akalla, ta yarda za su iya barci da kansu da kuma koyon zama natsattsun magidanta idan sun girma.

Hakkin mallakar hoto Adrian Storey Uchujin
Image caption Wani fasinja a Japan na barci kafin mota ta zo

Watakila wannan al'ada ce ta sa Japanawa suke iya barci hatta a cikin jama'a, ko da kuwa sun girma. Yawancinsu suna cewa sun fi jin dadin barci a tare da wasu maimakon mutum shi kadai.

Za a iya ganin alamun hakan a lokacin damunar 2011, bayan da bala'in ambaliyat Tsunami ya share garuruwa da yawa na bakin ruwa. Wadanda suka tsira da aka tsugunar da su a sansanoni, za ka ga gommansu ko ma daruruwansu suna zama da barci a wuri daya.

Duk da irin matsalolin da ke tattare da zaman taren, wadanda suka tsiran sun bayyana yadda kwanansu a wuri daya ya ke sa su natsuwa da kwanciyar hankali kuma su dawo da yadda suka saba barci.

Duk da haka wannan al'ada ba ta kai yadda za a ce ta samu karbuwa ba gaba daya musamman a makarantu da wuraren aiki

Bayan bincike na wasu shekaru a kan wannn dabi'a, a karshe na gano cewa, sam-sam ba a daukar al'adar Japanawan ta yin barci a mota da cikin jirgi da sauran wurare na jam'a wadda suke kira 'inemuri' a matsayin barci ba.

Ba wai ma ana daukarta daban da barcin dare ba a kan gado, ana ma daukarta dabn ne da kailula, wato dan takaitaccen barcin rana na hutawa.

Yadda ake daukar wannan barcin na al'adar Japanawan shi ne, duk da cewa wanda ke barcin ba ya sane da abin da ke faruwa a wurin. Ma'ana hankalinsa ba ya wurin, to amma zai dawo a duk lokacin da aka bukace gudummawarsa

Hakkin mallakar hoto Adrian Storey Uchujin
Image caption Wani fasinja a Japan na barci a kan kujera

Wannan barci a wurin aiki shi ne abin da muke son dubawa. A ka'ida natsuwa d shiga a dama da kai abubuwa ne da ake so ka yi a wurin aiki, saboda haka idan ka yi barci za a dauki hakan a matsayin alamar lalaci da rashin mayar da hankali kan aikinka.

Amma kuma ana danganta hakan da gajiyar da aikin ya haifar. Saboda haka zuwanka taron kadai ana daukarsa da muhimmanci fiye da abin da aka cimma. Kamar yadda wani na Japan din ya sheda min, inda ya ce, ''Mu Japanawa muna da kishi irin na Olympics, wato shiga a dama da kai shi ne abin da ke da muhimmanci.''

Juriya wadda ake nunawa ta hanyar aiki na tsawon sa'o'i da kuma sadaukar da kai da mutum yake yi, abu ne da ake matukar daukarsa da muhimmanci a Japan.

Duk mutumin da ya yi kokarin halartar taro, duk da gajiyar da ke damunsa da bukatu, mutum ne da yake da kamala da cancanta da aikin, kuma ya canci karin girma da duk wani abu na kyautatawa.

Idan har barci ya dauke shi saboda gajiya ko mura ko wani rashin lafiya, ba za a kama shi da laifi ba, sai a dora alhakin barcin a kan abin da suke kira shedanin da ke sa barci.

Tun da ana danganta wannan takaitaccen barci a mota ko a jirgi ko a wurin taro ko aiki da gajiya, idn mutum ya yi shi ko ya yi kamar yana yin barcin, ba a dauka cewa malalaci ne.

A maimakon haka ana daukar barcin a matsayin wata al'ada ta Japanawa ta tabbatar da aiki akai akai ta hanyar samun dan gajeren hutu a lokacin aikin.

Saboda haka a bayyane take cewa, Japanawa ba sa barci. Ba sa kailula. Suna dan gajeren barci na lokacin aiki wato Inemuri. Ba dadi ba ragi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The Japanese art of (not) sleeping