Me ya sa sojin ruwan Amurka ke buƙatar hatsabiban matuƙan jirgin sama?

Hakkin mallakar hoto US Navy

Wani hoton bidiyo da aka nuna na hatsabibancin da wasu matukan jiragen yaki na sojin ruwan Amurka, wadanda ake kira Blue Angels, ya taso da tambayar cewa: me ya sa matukan jiragen saman yaki suke bukatar wannan kwarewa?

Chris Baraniuk ya yi bincike

Tun a shekarun 1940 ne waɗannan matuƙan jiragen sojin ruwan Amurka da ake kira 'Blue Angels' suke irin wannan hatsabibanci na kasada da rai. Za ka so ka san yadda mutum yake a cikin ɗakin matuƙin irin wannan jirgin yaƙi wanda ke wulwulawa a sama kamar wata katantanwa.

Kamar hatsabiban matuƙan jiragen yakin sama na Burtaniya, da ake kira 'Red Arrows' ko takwarorinsu na Amurka waɗanda su kuma ake kiransu 'Thunderbirds, su waɗannan matuka suna abubuwa na kasada da ba a amfani da su a wurin yaƙi.

Su waɗannan jiragen yaƙi na Amurka za ka ga suna shawagi a kusa da kusa da juna, wanda kusancinsu bai wuce inci 18 ba, wato abin da bai wuce tsawon hannu ba. Kuma suna ɗan-karen gudu ne na cin ɗaruruwan mila-milai a cikin sa'a ɗaya.

Abin tambaya a nan, shi ne ko rundunonin sojoji suna amfana da irin matuƙan jirgin saman yaƙin da ke wannan hatsabibanci?

Amsar ita ce ''a'a'' da kuma ''e''. Yawanci hatsabibanci wani ɓangare ne na atisayen sojoji, saboda abu ne mai matuƙar muhimmanci a ce matuƙan jiragen sama sun kware wajen hatsabibanci da kasada da kuma ganganci, ta yadda za su iya laƙantar kaucewa barazana.

Sai dai ba kamar matuƙan jiragen yaƙin da ke bakin fama ba, su waɗannan matukan jiragen sojin ruwan na Amurka ba sa sanya wata riga ta musamman wadda ake kira G-suit, wadda ke kare su daga fita hayyacinsu (tana hana jini taruwa a ƙafafuwa ko ƙasan jikin mutum), a lokacin da suke wannan hatsabibanci.

A maimakon wannan riga su wadannan matuƙan suna laƙantar yadda za su kame jikinsu ne a daidai lokacin da za su yi wuntsule ko za su wulwula da jirgin, wanda hakan ne ke kare su daga fita hayyacinsu.

Hakkin mallakar hoto USA Today
Image caption Wasu daga cikin jiragen kenan suke hatsabibanci

Jiragen da waɗannan matuka suke amfani da su ( F/A-18) a wannan hatsabibancin na musamman ne saboda suna da abubuwa da yawa da ake amfani da su wajen sarrafa su, a yi wannan ganganci da su cikin sauƙi.

Baya ga wasu abubuwan, dalilin duk wani hatsabibanci ko atisaye na jirgin saman yaƙi shi ne domin nuna ƙarfin soji. Ana ɗaukar hakan a matsayin wata hanya ta jawo hankalin jama'a da kuma ƙarfafa wa matasa guiwa ta yadda za su yi sha'awar zama matuƙan jirgin sama wata rana.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Why does the US Navy need pilots who can fly like this?