Ƙoƙarin ƙirƙiro daimon daga gyaɗa

Hakkin mallakar hoto Getty

Fahimtar yadda daimon ke samuwa a can cikin ƙasa ka iya bayyana yadda rayuwa ta samo asali a wannan doron duniya, kamar yadda wasu masu bincike ke gani.

A don haka wasu masana kimiyya a Jamus suke ƙoƙarin gano yadda za su yi daimon daga iska mai dumi (carbon dioxide) da kuma tunkuza.

David Robson ya bi diddigin binciken

Duk bayan dan wani lokaci, Dan Frost sai ya ji wani kara a daben ofishinsa kuma ya ji yana motsi. Wannan ba wani abu ne illa abu daya: daya daga cikin gwajin aikinsa ne na kimiyya ya face.

Yawanci da ya ji hakan sai ya kama hanya ya nufi kasan benen ofishin nasa, ya je dakin gwajin kimiyyarsa, inda zai ga abokan aikinsa duk sun yi jugu-jugu.

Daga nan inda suke ayyukan binciken na kimiyya za ka ji kamar wani dan karamin bam ne ya fashe, kuma dalibansu na cike da tsoro. ''Kamar abin tsorone,'' ya ce cikin tattausan harshe. '' Amma ba abin tsoro ba ne an kare komai.''

Wannan fashewa na daga wani bangare na aikin. Masanin kimiyya a Bayerisches Geoinstitut a Jamus, Frost yana kokarin ya kwatanta abin da ke wakana a can karkashin kasa nisan dubban kilomita.

Hakan ya hada da nika duwatsu da karfin gaske, yadda kusan a ce dan adam bai taba ganin hakan ba, amma kuma hakan na tattare 'yan hadarurruka nan da can.

A cikin irin wannan aiki ne Frost ya gano wata hanya ta ban mamaki ta yadda za a iya yin dutsen daimon daga iska mai dumi (carbon dioxide), da tunkuza.

Idan muka kwatanta irin cigaban da muka samu na zuwa sararin samaniya, za mu ga cewa kusan ba mu san komai ba a kan abubuwan da ke karkashin kafafunmu (cikin kasa).

Kimiyyar kasa ta nuna cewa za a iya kasa kasa zuwa kashi-kashi, can tsakiyarta da kasanta da kuma samanta da kuma wajenta ko doronta. To amma babbar matsalar ita ce rashin sanin sinadaran da suka hadu suka yi kasar, kuma wannan shi ne babban gibi a iliminmu.

Hakkin mallakar hoto Science Photo Library
Image caption Tsakiyar dunkulen duniya

Frost ya ce, ''idan muna son sanin yadda wannan dunkulen duniya tamu ya samu, to daya daga cikin abubuwan da kake bukatar sani shi ne me da me da me suka hadu suka yi duniyya da sauran duniyoyi da ke zagaye da ita.

Masana kimiyyar karkashin kasa na ganin, ita wannan duniya tamu, ta samu ne daga abubuwa irin wadanda suka yi taurari. Sai dai matsalar ita ce, yawancin burbushin abubuwan taurari da ke fadowa doron kasa suna da sinadarin 'silicon' (wani burbushin karfe mai kyalli) fiye da yadda muke samu a wannan duniya. Saboda haka ina wannan sinadari yake zuwa?

Wasu na ganin yana nutsewa ne zuwa can kasan duniyar tamu. Domin amsa wannan tambaya Frost ya duba hanyoyi biyu ta yadda iska ke nuka sinadarai da karfi sannan kuma zafi ya dafa su. Abin da ke faruwa a nan shi ne daidai da wanda ke wakana a can karkashin kasa kusan nisan kilomita 900, ta yadda hakan ke sanya 'yan kananan sinadaran da ke wurin su dunkule su zama wasu abubuwan masu karfi.

Mataki na biyu kuma shi ne yadda wadannan sabbin abubuwa da suka samu a matakin farko za su nike ta yadda za su yi kama da sinadaran da ke can-can karkashin kasar kuma.

Hakkin mallakar hoto Thinkstock
Image caption Tunkuza mai dauke da sinadarin carbon da ke cikin daimon

Kimiyya da fasahar da Frost ya yi amfani da ita, ka iya nuna mana abubuwa hatta a kan iskar ma da muke shaka, to a nan ne maganar daimon din Frost ta zo.

Yana ganin ayyuka da dama ne ke wakana a karkashin kasa da suke jawo iska mai dumi (carbon dioxide) daga tekuna, zuwa cikin duwatsu, sanna kuma zuwa can cikin karkashin kasa, inda take zama dutsen daimon.

Ya ce babban sinadarin da zai sa hakan faruwa shi ne karfe. Iska mai karfin da ke can cikin kasar ita ke sa wanna iska mai dumi ta cikin duwatsu wadda ta ratsa sinadaran karfe, wadanda suka rabu da iska mai sanyi ta oxygen, sai su rabu da sinadarin carbon su samar da daimon.

Wannan kimiyyar kusan ita ce ka faruwa kamar yadda Frost ya gano, lokacin da ya kwatanta kimiyyar domin kirkirar daimon daga iska.

Da wuya dai Frost ya cimma wani abu na a-zo-a-gani daga wannan yunkuri nasa, domin daimon na daukar dogon lokaci kafin ya samu. Amma wannan bai hana shi gwada wasu abubuwan ba domin samar da daimon din, kamar yadda ya jarraba tunkuza (na gyada) wanda ke dauke da sinadarin carbon mai yawa.

Hakkin mallakar hoto Getty

Iskar hydrogen ta fita da yawa a wannan dabarar da ya jarraba, har ma ta watsa aikin baki daya, in ji shi, ''amma bayan an samu daimon din.'' Cibiyarsa ta kimiyya dai a yanzu ta dukufa wajen ganin ko za ta iya kirkirar daimon da sinadarai daban-daban.

A yawancin aikin dai, Frost, yana da sha'awar sanin wasu abubuwan sirri da aikinsa zai nuna mana a game da tarihin kasa, da kuma rayuwa a wasu wuraren. Frost ya ce, ''muna da sha'awar sanin yadda can cikin kasa yake mu'amulla da wajenta, kuma idan har muna neman wata duniyar da za a iya rayuwa a kanta to dole ne mu yi nazarin wadannan abubuwa da suke wakana a wannan kasa ko duniya tamu.

Muhimmin aiki da ke bukatar sadaukar da tunkuza da kuma wannan fashewa mai firgitarwa.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How to make a diamond from scratch - with peanut butter