Me ya sa muke kuka?

Hakkin mallakar hoto Adam Proctor

Idan ka yi tunani a kan zubar da hawaye ko kuka za ka ga kusan wani abu ne na daban. Me ya sa muke yinsa? Kuma me ya sa ake da bambanci tsakanin yadda kukan maza yake da na mata?

Adam Rutherford ya yi bincike

Ni mutum ne me saurin kuka. Ba na jin kunyar hakan. To amma fa ina da wannan al'ada ta saurin kuka ne, idan ina kallon fim. Ban gano dalilin da ke sa ni sauri da yawan zubar da hawayen ba, amma yawanci ya shafi mu'amullar iyaye da 'ya'ya ne.

Ka duba fim din 'Field of Dreams', wanda labari ne da aka shirye mai matukar ratsa zuciya da tausayi, wanda a karshe-karshensa ya sani hawaye sharbe-sharbe.

Haka shi ma fim din 'The Force Awakens' wanda na kalla tare da 'yata 'yar shekara goma, muna rike da hannun juna dukkaninmu muna hawaye. A bisa al'ada babu dalilin da zan yi haka.

To me ya sa maza ba sa kuka sosai kamar mata? Kuma menene amfanin zubar da hawaye? Shin wani abu ne da ba a saba gani ba, cewa a matsayina na namiji ina yawan kuka?

Wannan na daya daga cikin tambayoyin da nake bincike a kansu kwanan nan. Bayan ga dalilin da ya sa maza ba sa kuka sosai kamar mata. Da neman sanin amfanin zubar da hawayen da kuma uwa-uba me ma ya sa muke yin kuka idan ana magana ta fannin halitta?

Hakkin mallakar hoto Adam Proctor
Image caption Har yanzu masu bincike ba su tabbatar da ainahin dalilin da ke sa mu yi kuka ba

Amsar tabayar ko ni daban nake da sauran mutane kai tsaye take. Kamar yadda kusan duk binciken da aka yi ya nuna, mata sun fi maza yawan kuka, kuma sakamakon haka yake kasancewa ba sauyi tun lokacin da muka fara bincike.

Binciken masanin tunanin dan adam William Frey a shekara ta 1981 ya lissafa cewa yawanci mata suna kuka sau 5.3 a wata, yayin da su kuma maza suke zubar da hawaye yawanci sau 1.3 a wata.

Haka kuma yawanci kukan mace ya kan kai minti shida, yayin da shi kuwa na namiji yake iya kaiwa na tsawon minti biyu ko uku kawai.

Idan ana maganar bincike a kan kuka ne to, mutumin da za a yi magana shi ne masanin tunanin dan adam Ad Vingerhoest dan kasar Holland, daga jami'ar Tilberg.

Masanin yana daya daga cikin 'yan kalilan din masu binciken da suka yi nazari a kan kuka, kuma sakamakonsa ya tabbatar da cewa, akwai bambanci tsakanin maza da mata a kuka, kuma hakan ya fara ne tun lokacin yarinta.

A matakin jariri babu bambancin kuka tsakanin namiji da mace kuma duk duniya jarirai suna kuka ne daidai (masana na ganin kukan jariri alama ce ta neman kulawar iyaye. Kuma ina ganin tuni iyaye sun san haka).

To menene zai bayyana bambancin da ke bayyana a kuka tsakanin namiji da mace yayin da yara suka girma? A bayyane take cewa al'ada na taka muhimmiyar rawa a nan.

Bincike-binciken da aka yi ta gudanarwa a kasashe daban-daban sun nuna cewa, mutane sun fi yawan kuka a kasashen da aka fi daukar kuka da muhimmanci a zamantakewar jama'a.

Haka kuma Vingerhoets ya gano cewa mutanen kasashe masu arziki sun fi yawan kuka, saboda yalwa ta na sa mu fi bayyana damuwa ko jin dadinmu, wanda hakan ke sa mutane su zama kamar jarirai wajen tsala kuka.

Amma kuma masanin yana ganin ba wai yanayin zamantakewa na namiji ba ne kadai yake hana maza yawan kuka, hatta kwayoyin halittarsu na maza (testosterone) suna da tasiri.

Masanin ya ce, mazan da ake yi wa maganin cutar daji ta marena da magungunan da suke rage musu yawan kwayoyin halitta na namiji, su ma suna da dabi'ar kuka da yawa, ko da yake za ka iya musun haka, da cewa, suna da raunin zuciya ne saboda suna da cutar daji.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Obama na kuka

Idan muka koma kan maganar kan yadda fina-finai ke sa mutum kuka kuwa, akwai wani wuri a fim din Terminator 2, inda Arnold Schwarzenegger ya lura cewa yaron da ke wurinsa ya yi kuka kadan, bayan da aka kashe duk wani da ya sani, ya tambaye shi, ''me ya sa kake kuka?''

Mutane ne kadai aka san suna kuka saboda wani abu da ya ratsa ransu,( ko da yake a baya akwai maganganun cewa wai kila giwaye na kukan mutuwa, amma ba shedar da ta tabbatar da hakan).

Wannan dai wani fanni ne na ilimi da ba a yi bincike a kansa ba sosai. Ba mu san me ya sa muke kuka ba idan wani abu ya ji mana rauni. Ba mu san kuma me ya sa muke kuka ba idan wani abu na tausayi ko tayar da hankali ya same mu, ko kuma a lokacin da wani abu na matukar farin ciki ya same mu ba.

A matsayinmu na halittu da ke mu'amulla da juna (zamantakewa), kuka zai iya zama wata alama ta nuna wani muhimmin yanayi (tunaninmu ko zuciya) da muke ciki. Amma dai wannan duka hasashe ne kawai.

Watakila kuma mutane suna kuka ne domin rage damuwa, saboda kamar yadda daya daga cikin nazarin da Vingerhoest ya yi, ya nemi ya tabbatar da maganar da ake yi cewa mutane sun fi jin dadi bayan sun yi kuka sosai.

A shekara ta 2015 ya nemi wasu mutane (da ya yi bincike da su) da su bayyana yadda suke ji kafin su kalli daya daga cikin fina-finai masu sa kuka. Daya shi ne 'Life is Beautiful' , dayan kuma shi ne 'Hachi: A Dog's Tale'.

Suna gama kallon fim din sai ya sa mutanen su sake bayar da bayanin yanayin da suke ji (ta hanyar cike takardar da ya ba su su cike da farko), bayan minti 20 ma ya ne su ba shi bayanin yadda suke ji, da kuma bayan sa'o'i biyu ma ya sa su rubuta yadda suke ji.

Sakamakon ya bambanta karara, domin wadanda ba su yi kuka ba a lokacin kallon fina-finan, ba su nuna wani bambanci ba a yanayinsu (hankalinsu).

Hakkin mallakar hoto Getty

Amma wadanda suka yi kuka, yanayinsu ya inganta sosai bayan kukan, wanda za a iya fassara hakan da maganar da ake yi cewa kuka na sa mutum ya ji dadi bayan ya yi shi (kamar ya sauke wani nauyi).

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. It's curious that we cry - here's what we know about why