Ka san haɗarin tiyatar asibiti?

Hakkin mallakar hoto Goteborg University Sweden

Ƙwararren ma'aikacinmu kan ƙididdiga David Spiegelhalter ya duba tarihin aƙubar da mutane suke sha a shekarun baya a asibiti da sunan tiyata, abin da yake kamar fawar dabba.

Abu ne mai wuya ka karanta yadda ake tiyata a asibiti a daruruwan shekarun da suka gabata ba tare da tsigar jikinka ta tashi ba, saboda irin kayan aikin da ake amfani da su na gargajiya, da rashin yin allurar kashe zafin ciwo, da ma kuma irin yadda ake tiyatar domin abu ne da ba za ka iya bambantawa da yadda ake fawa ba a yau.

Daga cikin aikin a wancan lokacin za ka ga ana cire wani sashe na kokon kai har kwakwalwa ta fito fili domin a yi maganin wani rauni na ka ko kuma maganin ciwon kai ma sakamakon jin rauni a kan.

Bincike ya nuna cewa a wancan zamanin kusan a duk kokon kai uku, guda daya an yi masa wata huda ko an cire wani bangare nashi.

A zamanin na da kai shi ne ya fi hadarin jin rauni daga abubuwa da dama har da makamai irin na da, kuma ana yin hudar ne a ka ko a cire wani bangare na kokon kan domin jini ko abin da aka kira muguwar iska su fita, yadda kwakwalwar za ta rika samun iska sosai.

Babban abin da aka gano ma shi ne da yawa daga cikin wadannan kokunan kai tsakanin kashi 50 da 90 cikin dari na mutanen da suka tsira ne bayan an yi musu aiki.

An san wannan tsarin tiyata sosai a Turai a matsayin wata hanyar maganin farfadiya da larurar kwakwalwa, har zuwa karni na 18, sannan kuma daga baya ana amfani da hanyar wajen yi wa wadanda suka ji rauni a ka.

A karni na 19 masu aikin hakar ma'adanai a Turai sukan kafe sai an yi musu irin wannan huda a kokon kai ko da kuwa ciwon da suka ji a kan kadan ne, a matsayin kan-da-garki.

Amma lokacin da asibitoci suka fara bunkasa a karni na 19, sai wannan huda a ka ta kara zama hadari. Matsalar ita ce tsafta: hadarin kamuwa da wata cuta ya karu sosai a asibitocin, abin da ya sa yawan mutuwa ya karu da kusan kashi 90 cikin dari.

Maganin kashe zafin tiyata

Abin da a wancan zamanin ake amfani da shi kawai domin kashe zafin tiyata shi ne kayan maye. Barasa da ganyen wiwi da na opium su ne muhimmai da ake amfani da su a lokacin har sai da Humphrey Davy shi da kansa ya jarraba amfani da sinadarin iskar nitrous oxide ko iskar gubar da ke sa mutum yawan dariya.

A ranar 16 ga watan Oktoba na 1846 ne William Morton ya fara amfani da maganin kashe zafi a lokacin tiyata na 'ether' a babban asibitin Massachusetts a Amurka.

Daga nan ne tsarin ya samu karbuwa bayan da Sarauniya Victoria ta Ingila ta amince da amfani da sinadarin chloroform a lokacin haihuwar Yarima Leopold a 1853, ko da yake daga baya an yi watsi da amfani da chloroform din saboda mutuwar kwatsam da yake haddasawa a tsakanin matasa masu amfani da shi a matsayin kayan maye.

A yanzu kusan abu ne da ya zama al'ada a duniya, a yi wa mutane allurar barci ko kashe zafi kafin a yi musu tiyata. Hukumar lafiya ta duniya ta ce a kowace shekara ana yin manayan tiyata kusan miliyan 230 ta amfani da allurar kashe zafi.

Duk da haka wannan allura na tattare da hadarinta, kuma yawan hadarin ya dangana ne da cigaban da ake da shi na kwarewa a harkar kula da lafiya.

To idan ka tsira daga allurar kashe zafin , yaya ita tiyatar kuwa?

Alkaluman Burtaniya sun bayyana rayuwa maimakon mutuwa a sanadin tiyata. A Amurka, mutane suna mutuwa a sanadiyyar tiyata, yayin da a Burtaniya ba sa rayuwa.

Wannan dabara ta zabar sunan illa ko hatsarin yin tiyata na nuna kyawun aiki tare da boye bambance-bambance. Bambamcin da ke tsakanin asibiti biyu daya da damar nasara kashi 98 cikin dari daya kuma da kashi 96 cikin dari na rayuwa daga tiyata, kamar yadda za a iya bayyanawa a Burtaniya, abu ne da bai taka kara ya karye ba.

Can a Amurka kuwa ana irin wannan kwatanci na tsakanin kashi biyu cikin dari da kashi hudu cikin dari na mutuwa a sanadin tiyata da cewa hakan ya ninka, kuma ya fi zama matsala sosai. Wadannan su ne irin alkaluman da kafafen yada labarai ke amfani da su.

Duk tsarin da aka zaba a yi amfani da shi wajen bayyana irin hadarin mutuwa da ke tattare da tiyata, muna iya dubawa mu yi nazarin hadarin domin samun karin bayani ko ilimi.

Misali duk asibitocin da ke jihar New York wadanda suka yi tiyatar zuciya dole ne su mika wa ma'aikatar lafiya dukkanin bayanan aikin.

A shekarar 2008 an yi tiyatar sauya wurin wata jijiyar da jini ke bi ya fita daga zuciya wadda ake kira CABG a asibitoci 40, kuma mutane 194 da aka yi wa aikin ne suka mutu a asibiti ko kuma bayan kwana 30 da yin aikin, wato mutuwar kashi 1.8 cikin dari kenan , ko kuma kamar yadda a Burtaniya za a bayyana lamarin rayuwa daga tiyatar ta kai kashi 98.2 cikin dari.

Tiyata a zuciya ta fi hadari, domin a cikin mutane 21,445 da aka yi wa aiki a jihar New York tsakanin shekara ta 2006 da 2008, mutane 1,120 sun mutu, yawan mutuwa ya kai kashi 5.2 cikin dari kenan ko kuma sama da mutum daya a cikin 20.

Duk da hadarin da ke tattare da yin tiyata ga alama hadarin rashin yin ya fi girma. Saboda haka za ka so a yi maka aikin asibiti a wannan zamanin saboda irin ci gaban da aka samu na fasaha ba kamar a shekarun baya ba.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Operations: The risks of going under the knife