Za ka iya rayuwa da fargabar mutuwar farat daya?

Hakkin mallakar hoto Thinkstock

Marubuciya Eva Hagberg Fisher ta yi shekaru cikin tsammanin cewa za ta iya mutuwa a kowane lokaci, sai dai ba wanda zai iya tabbatar mata, saboda likitocinta suna ta ƙoƙarin gano cutar da ke damunta.

Rose Eveleth ta tambaye ta yadda zama cikin irin wannan zullumi yake, tare da neman sanin yadda fargabar mutuwa ke iya sauya tunaninmu.

A yau Eva Hagberg Fisher daliba ce da ke karatun digirin digirgir, sannan kwararriya ce kan harkar zanen gine-gine sannan kuma marubuciya ce wadda kle zaune a Berkeley. A kwanan nan ta sayar da littafinta na biyu, wanda ya kunshi tarihi ne kan abokanta.

Kuma a cikin shekara takwas da ta wuce Hagberg Fisher ta kasance tana rayuwa cikin rashin tabbas na tsawon lokacin da za ta iya rayuwa.

A shekarar 2008 ne Hagberg Fisher tana zaune a New York, sai a hankali a hankali ta fara jin wani irin yanayi na daban a jikinta. Kusan ko da yaushe sai ta rika jin jiri, da kuma yawan kishirwa.

Wata rana a watan Janairu ta tashi daga barci ta shiga dakinta na girki, inda, ''na ji kamar daben dakin yana tasowa sama ya tarad da ni ko kuma ni ina jin kamar ina yin kasa zan tarad da daben,'' Kamar yadda ta rubuta a wani littafin intanet a game da gwagwarmayar larurarta.

Wani likita a jami'ar New York ya sa ta je a yi mata hoton cikin jikinta na asibiti (MRI), yana ganin kamar wani dan kurji ne a kusa da kunnenta yake sa mata wannan larura. Haka ta rika zuwa ana mata gashi na cutar daji sau biyu a mako, amma hakan bai yi wani tasiri ba.

Hakkin mallakar hoto iStock Olivia Howitt
Image caption Mukan yi tunanin mutuwa a zuci amma ba abin da za ka iya yi ka shirya zuwanta na zahiri

Ta yi tunanin cewa watakila yanayin zama ne a wannan birni me hayaniya ya haddasa mata wannan rashin lafiya, saboda haka a 2009 sai ta koma Portland da zama domin ta huta. Ta gaya min cewa ta rika cin 'ya'yan ita ce da motsa jiki a keke.

A lokacin da take Portland ta koma karatu a jami'a kuma a 2010 sai ta koma Berkeley ta fara karatun digiri na uku a fannin karatun tarihin zanen gine-gine.

A farkon karatun nata na digiri na uku sai ta fara gani da jin wasu alamomi na daban a jikin nata. Sai tunani ya dame ta kusan ko da yaushe tana cikin zullumi.

Wani likita a San Francisco ya rubuta mata maganin yawan tunani, domin hakan abu ne da daliban da ke karatun gaba da digirin farko kan yi fama da shi, aka ce kila yana daga abin da ke sanya mata jirin na.

Maganin ya kashe mata jiki amma kuma bai tsayar mata da matsalolin ba. A hankali a hankali sai abubuwa suka fara yi mata tsauri. Ta tashi daga barci tana ta zufa, ta yi ta fama kan abin da za ta yi.

Sai yanayinta ya rika sauyawa, kofuna na faduwa a hannunta a dakin girkinta, ta jefa wannan abu can ta sa wancan a nan, ta rika jin tana abubuwa daban da yadda ya kamata ta yi, har ma ta fara manta sunan dalibanta.

Wani lokaci suna tsakar tattaunawa har ta kai ga shidewa ta suma. Wani likita a asibitin daliban makarantar ya yi mata gwaji ya gano tana fama da wata cuta ne da ta shafi zuciya, inda sakonni ke yanke wa daga zuciyar.

Daya daga cikin hadurran ita wannan cuta kamar yadda likitoci suka gaya mata shi ne mutuwar farat daya. Washegari sai Hagberg Fisher ta tashi daga barci amma kuma ta kasa tafiya . Ta ce, ''na kasa fahimtar komai, na rude.''

A dakin kula da marassa lafiya da ke bukatar kulawar gaggawa, inda likitoci suka yi amanna cewa, ruwan jikinta ne ya kare, wata ma'aikaciyar jiyya ta nemi a kwantar da ita a asibitin.

A nan ta kwashe kwanaki shida a asibitin, yayin da likitoci ke ta kokarin gano abubuwan da ke haddasa mata wadannan matsaloli. Sun dai kawar da yuwuwar cewa ko tana dauke da cutar daji ta koda ko cutar sukari ko cuta mai karya garkuwar jiki, ko kuma tinjere (syphilis).

Wani yana ganin damuwa ce nake fama da ita, yayin da wani kuma yake tunanin wani kurji ne ke damuna. Abin mamaki, cewa kurji ne zai kashe ta da wuri haka, sai abin ya zamar mata wani sauki.

Ta ce, ''da ina ta tunanin cewa ya kamata na dage ne na rika numfashi da kyau na kuma kara himma wajen motsa jiki, sai kawai suke maganar wani kurji, mai wani suna da ban taba ji ba, wanda ni da tunanina shi ne ina bukatar jajircewa ne, saboda ina ta kokarin samawa kaina sauki da kaina amma abin ya ci tura.

Hakkin mallakar hoto Getty Olivia Howitt
Image caption Hagberg Fisher ta kan tsaya haka a ƙame domin fargabar mutuwa za ta ɗauke ta

A karshe dai ta shawo kan likitocin su yarda a dauki hoton kwakwalwarta. Bayan 'yan sa'o'i da yin hoton sai suka zo da sakamako cewa tana bukatar a yi mata wani aiki ne a kwakwalwarta saboda tana da wata 'yar larura daga wani bangarenta.

To amma a rashin saninsu wannan shi ne farkon rudanin shekaru kan wannan larura tata da kuma cigaba da rayuwa cikin zullumin mutuwa a ko wane lokaci.

Bayan shekara biyar yanayin larurar Hagberg Fisher sai ya fara zama kamar wani bangare na wani wasan kwaikwayo. Likitoci sun yi tunanin tana da cutar daji ta mahaifa ne, sannan suka ce kurji ne a kwakwalwarta, suka dawo suka sake cewa sankarar mahaifa ce ke damunta, suka zo daga baya suka ce ai tsananin gajiya ce, haka dai suka rika kawo mata cutuka iri daban-daban.

Har tiyata aka yi mata a mahaifarta bisa zaton akwai wani abu a ciki, amma ba a ga komai ba. Akwai ma lokacin da take gab da mutuwa a cikin motar daukar marassa lafiya za a tsallaka gadar Golden Gate Bridge da ita.

Ta ce, '' na tuna lokacin da nake kallo ta tagogin motar ta baya lokacin da muke tsallaka gadar, ina tunanin cewa wannan shi ne abu na karshe da zan gani a rayuwata, kuma hankalina bai tashi ba, ina cikin natsuwa. Wannan kwanciyar hankali da mutane ke magana na ji ta.

A lokacin ina ganin na natsu ne saboda na dake, amma yanzu na san cewa kwakwalwata ce kawai take shirin dena aiki. An yi mata tiyata a zuciya domin yi mata maganin wata cutar. Ta koma Arizona da zama domin tsira daga abin da take gani yanayi ne da jikinta ba ya so a inda take. Hakan bai yi aiki ba.

Ta yi aure ta koma California da zama, kuma wani likita ya ce ya gano tana da wata cuta ne da ke sa kwayoyin halittarta su rika fitar da sinadarai da yawa.

Hakkin mallakar hoto iStock Olivia Howitt
Image caption Tunanin mutuwa kwatsam ya mamaye rayuwarmu ta yau da kullum

A yau, a karon farko a cikin shekaru, Hagberg Fisher tana rayuwa ba tare da tunanin cewa akwai wani gwajin cuta da za a yi mata ba. Tana bin tsari na kiyayewa da wasu dokoki na tabbatar da lafiyar kwayoyin halittarta, kuma ta ce hakan na yi mata aiki da kyau, domin tana jin sauki. Amma har yanzu tana rayuwa cikin rashin tabbas a kan lafiyar tata.

Ba ta da tabbas ko za a sake gano wata cuta, ko akwai wani abu da ke labe a cikinta da yake jiran bayyana kansa. Amma ta ce rashin tabbas na rayuwarta, da iya lokacin da za ta rayu, sun sauya ta gaba daya.

Ranar da za ka mutu

Ya za ka ji idan ka san ranar?

Shafukan kacici-kacici na intanet da yawa sukan bayyana ranar mutuwarka ta hanyar amfani da abubuwa da suka shafi rayuwarka, kamar jinsinka na mace ko namiji, bakar fata ko bature da shekarunka.

Misali kamar yadda shafin deathclock.com ya ce mutum mai shekara 28 wanda ba ya shan taba kamar ni, wanda awon yawan maikon jikinsa (BMI) yake kasa da 25, zai mutu ranar Litinin 26 ga watan Disamba na 2044.

Irin wadannan shafukan intanet suna zakewa wajen kafewa a kan ranakun da suke bayyanawa, amma dai ana samun inganci na kayan kimiyya na duba abin da zai iya kashe mutum, da kuma lokacin da zai mutu.

Misali wasu kamfanonin inshorar rai suna kokarin hasashen tsawon rayuwar mutanen da suke sayen inshorar tasu ta hanyar amfani da manyan hanyoyin dabarar tattara bayanai.

Kuma masu bincike suna kokarin gano hanyoyin kwayoyin halittar da za su rika nuna musu ranar mutuwar mutum. Wasu kwayoyin halittar ma ba ranar ba kadai hatta lokacin mutuwar ma za su iya taimaka wa likitoci su sani.

Wani bincike da aka yi a jami'ar Havard ya gano cewa mutanen da suke da wani sanfurin kwayoyin halittar jini (genotype) suna mutuwa kafin karfe 11 na safe, yawancin saura kuma suna mutuwa kafin karfe shida na yamma.

Zuwa yanzu dai duka wannan aiki ne na hasashe kawai bisa lissafin alkaluma, amma dai yadda ake samun cigaba a fannin kula da lafiya da binciken kwayoyin halitta, ka kwana da sanin cewa wata rana za a kai ga lokacin da za ka san ranar da za ka mutu.

Sanya mutuwa a ranka

Masana kimiyya sun san cewa sanya tunanin mutuwa a ranka zai iya shafar tunaninka ta hanyoyi da dama, yawancin lokaci ba ma tare da ka sani ba.

Wadansu bincike-binciken sun tabbatar da cewa a duk lokacin da abu ya yi karanci, misali lokacin da ya rage maka a rayuwa, to za ka ga mutane sun fi daukar wannan abu (da ya kusa karewa) da muhimmanci.

Wani mai binciken kimiyyar kuwa ya nuna cewa, idan dalibai suna rubutu a kan mutuwa zuwa wani tsawon lokaci, ana ganin suna rage damuwa su kuma nuna sanin muhimmanci da martabar kansu tare kuma da kwarin guiwa.

Wani nazari ya nuna cewa hatta tunanin mutuwarka zai iya sa ka sauya wasu ra'ayoyinka da siyasarka. Akwai wani fanni a ilimin tunanin dan adam (Terror Management Theory) , wanda ke cewa idan aka gabatar wa da mutane abin da ya shafi mutuwarsu ba tare da sun sani ba, sai su zama marassa hakuri da yawan fada.

Dukkanin wadannan maganganu suna nuna mana yuwuwar samun wani yanayi mai sarkakiya: idan har a nan gaba ilimin likitanci ya kai yadda za mu iya sanin ranar mutuwarmu sosai, to hakan zai iya sauya yanayinmu ta hanyoyi da yawa fiye da yadda za mu sani.

Hakkin mallakar hoto Getty Olivia Howitt
Image caption Ta yaya sanin ranar da za ka mutu zai iya sauya yanayinka

Har yanzu abu ne da ya sha bamban hasashe ko tunanin mutuwarka a can wani lokaci da kuma ganin lokacin a zahiri ya taho yau. Hagberg Fisher ta kwatanta hakan da mutuwar wani dan uwa ko aboki na kusa.

Za ka iya sanin cewa mutumin nan zai mutu nan ba da dadewa ba, sai ka shirya wa mutuwar, amma idan haka kwatsam ka samu labarin mutuwar, akwai yadda za ka ji (damuwa) yadda ba za ka iya shirya wa jin hakan ba ( misali kamar wutar lantarki ta ja ka kwatsam ba zato ba tsammani). Ba za ka taba sanin yadda abin yake ba sai ya faru.

Hagberg Fisher na cikin fargabar mutuwa kusa da shekara goma. Ba wanda zai iya gaya mata yadda wannan fargaba take, ko abin da yake tayar mata da hankali. Har ma ta kai yawancin lokaci likitoci ba sa ambatar kalmar sankara ko kurji (daji), idan suna duba ta.

A lokacin da aka sake ganowa tana da cutar zuciya (mai sa zuciya ta rika bugawa yadda bai dace ba), sai fargabar mutuwa farat daya ta mamaye ta.

Ta ji ta kame wuri daya ta kasa motsi, tana tsoron kada ta motsa ta jawo mutuwarta. Akwai maganganu na mutane da yawa da suka furta kan yadda rayuwa take, idan kana jin ranarka ta karshe a duniya kenan.

Steve Jobs ya taba cewa: ''Kullum safiya na kan duba mudubi na tambayi kaina: ''Idan yau ne ranata ta karshe a duniya, zan yi abin da nake gab da yi yanzu a yau?'' Kuma idan amsar ta kasance a'a a kwanaki da dama a jere, to na san cewa ina bukatar in sauya wani abu.''

Za a iya kallon wannan magana kamar ba wata ta a-zo-a-gani ba ko mai wani tayar da hankali, amma Hagberg Fisher ta ce rayuwa cikin yanayi na fargabar mutuwa tsawon lokaci ta sauya yadda take daukar rayuwa.

Ba ta damu da rayuwa a yanzu. Ba kasafai ma take yin wasu tsare-tsare da suka wuce na 'yan makonni ba. Kuma idan tana dariya ta ce tana tabbatar da cewa tana la'akari da dariyar da take yi.

Ta ce, '' a duk lokacin da na ji na kyalkyale da dariya ba kama hannun yaro, sai na yi tunani cewa ina dariya ne da jin dadi, kuma hakan yana da kyau, kuma zan yi ta in more, saboda na sani sosai cewa sabaninta ne(kuka).''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. How it feels to live with the possibility of 'sudden death'