Gaskiya ne abinci a kwano ya fi daɗi?

Hakkin mallakar hoto iStock

Wata sabuwar sara ta cin abinci a tangaran mai zurfi ko kwano ta kankama a gidajen abinci daga London har zuwa California. Masu wannan ra'ayi suna ikirarin abinci a kwano ya fi daɗi. Ina gaskiyar wannan magana?

Chris Baraniuk ya yi mana nazari

Wani dan birnin New York me wannan ra'ayi Lily Kunin ya sheda wa jaridar New York Post cewa ya ci abinci iri daya a tangaran mai zurfi da kuma wani ba a irin wannan tangaran din ba sai ya ji abincin ba shi da dadi sosai.

Haka ma wasu mutanen sun yi ikirarin cewa idan suka ci abinci a tangaran mai zurfi ko kwano abincin ya fi dadi. Wannan wani ikirari ne da wasu mutanen da yawa ke dauka shirme ne kawai, amma kuma abin zai iya kasancewa gaskiya.

Duka dai abu ne da ya dogara da yadda za mu ji dandano da kuma yadda za mu ji mun koshi bayan mun ci abincin. An yi nazari kan yadda launi da irin abinci yake iya tasiri a kan mutum, kamar yadda shi kansa amfanin irin kwanon da aka zuba abincin da cokulan da ka yi amfani da su wajen cin abincin za su yi.

Hakkin mallakar hoto iStock
Image caption Girma da siffar kwano da cokula kan iya tasiri sosai a kan daɗin abinci

Misali launin ja zai iya sa a ji alewar da ke da zaki kamar wata wadda ba ja ba, ta fi zaki. Haka kuma wani nazari da aka yi ya nuna cewa nauyin kwano da sauran kayan cin abinci suna sa mutum ya dauki abincin da aka zuba masa da daraja.

Sai dai sakamakon wannan nazari wani lokaci ya kan bambanta sosai- kamar yadda wani binciken ya gano cewa madarar nonon yogot da aka sha da cokalin roba maras nauyi kan sa mutum ya ji yogot din ta fi dadi da tsada.

Idan ana maganar abinci ne, abubuwa da dama za su iya yin tasiri, in ji Charles Spence, kwararre a kan yadda tunanin mutane yake a kan dandanon abinci a jami'ar Oxford.

Ya ce, ''na yarda cewa irin kwanon da muke cin abinci da shi yana taka muhimmiyar rawa kan yadda dandanon abubuwa suke.'' ya kara da cewa, ''komai kama daga irin kwanon (santsi ko kaushi ko nauyi ko rashin nauyi) da sanyi ko duminsa da sauransu na iya shiga cikin duka wannan.''

Idan masu ra'ayin cin abinci a cikin tangaran mai zurfi suna rike da tangaran din a hanunsu a lokacin da suke cin abincin, karin nauyin tangaran din zai iya yin tasiri kan gamsuwa ko koshinsu da abincin, har ma su fi jin dadin abincin.

Haka kuma idan tangaran din da kake rike da shi yana da dumi, za ka dauki sauran mutane da ke kusa da kai a matsayin masu dadin zama ko mu'amulla. In ji Spence, ''za ma ka ji cewa za ka iya biyan karin kudi a kan abincin.''

Tangaran din da ba shi da baki yawanci akan cika shi da abinci, abin da zai sa mutum ya dauka cewa abincin cikinsa yana da yawa sosai in ji Charles Spence

Spence ya gudanar da gwaji da wasu mutane domin sanin ko girman bakin tangaran din zai iya tasiri kan yawan abincin da ke cikin tangaran din.

Idan aka kara girman tangaran din duk da cewa yawan abincin daya ne za ka ga kamar yawan bai kai ba.

Hakkin mallakar hoto iStock

Masanin yana ganin za ka iya sauya tsarin ka ce kwanan tangaran din wanda ba shi da baki, ko da yaushe za a cika shi har baki ta yadda za a dauka cewa abincin cikinsa ya fi yawa.

Ba shakka yanzu gidajen sayar da abinci sun fara jarraba wannan tsari ta hanyar amfani da kwanukan abinci iri daban-daban a kwanan nan domin jawo hankalin masu sayen abincinsu.

Wannan ya sa yanzu za ka ga yawanci ana zuba wa mutane abinci a abubuwa iri daban-daban kamar wani fale-falen katako kamar allo.

''Zuba abinci a tangaran mai zurfi,'' in ji Spence, zai iya kasancewa wani martani ne na wannan al'ada ko salo, da kuma yarda cewa kwanon zuba abinci na da amfani kuma zuba wadansu nau'in abincin a wasu kwanukan abu ne da yake da muhimmanci.

Binciken da rahotannin duka dai suna nuna abu daya ne, abin shi ne a yau ba abincin da ka ci ba ne yake da muhimmanci, a'a yadda ka ci abincin ne.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Why 'bowl food' might be tricking your brain