Me ke sa 'yan Burtaniya son shayi sosai?

'Yan Burtaniya suna shan shayi fiye da kofi miliyan dubu sittin a duk shekara- menene ke cikin shayi da har ya sa suke sha'awarsa haka ya kama su?

Veronique Greenwood

Ko da da madara ko sukari ko lemon tsami ko kuma tsura suka sha shayinsu, afili take cewa 'yan Burtaniya suna sha'awar dandanon shayi sosai.

Akwai wani abu tattare da wannan bauri da ya jawo wannan kauna, wadda ta sa 'yan Burtaniyar ke shan kofi miliyan dubu sittin a shekara kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Wato kowane namiji da mace da yaro a Burtaniya suna shan sama da kofi 900 a duk shekara.

Shayi ya shiga rayuwar 'yan Burtaniya, daga na karin kumallo zuwa na rana da ake sha sanye da kwat da lakataye da turoza, wanda manyan mutane ke sha a manyan otal-otal masu tsada na birnin London.

To wai shin wadanna sinadarai ne ke sa wannan ganye da ake matukar kauna wannan dandano? Kuma ko yanayin shan shayinka na bayyana wani abu game da kai?

Domin amsa wannan tambaya sai ka farao gano ainahin abin da ke sa ganyen wannan dandanon da yake da shi. Dandanon ganyen shayi ya dogara ne ga yadda aka noma shi, da sarrafa shi da kuma hada shi.

Ana noman ganyen shayi ne a yankuna masu zafi sosai da masu dan zafi-zafi. Amma kuma iadan ana son a yi koren ganyen shayi ne wanda ake kira 'green tea, sai manomi ya yi rufe shukar ya yi mata inuwa da raga ko tabarma, ta yadda rana ba za ta samu ganyen ba sosai.

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Ganyen shayi

Ba shakka wasu daga cikinmu za su so wannan dandano, kuma manoman ganyen za su iya kara sa ganyen ya yi wannan dandano daidai yadda ake so.

Bayan an debo ganyen daga gona sai a shanya shi ya bushe. A nan ma tsawon lokacin da ake barinsa a rana ya dogara ga irin dandanon da ake so ya yi.

Idan nau'in ganyen da ake yin green tea din ake so a yi, nan da nan da an shanya shi a rana ake kwashe shi a sa shi a kwano mai zafi ko tururi wato a dan tsorata shi, kamar yadda masu girki ke cewa.

Idan kuma ganyen bakin shayi kamar yadda muka sani ake so, sai a bar shi ya dan bushe a rana sannan a dafa shi, daga nan sai a samu ganyen shayin da ya kai kashi 78 cikin dari na shayin da ake sha a duniya.

Abin da ke faruwa a duk wannan lokaci da aka shanya ganyen shayin shi ne, kwayoyin halitta ko sinadaran wannan ganye suna harhaduwa ne su sauya yanayin haduwarsu.

Yawan tsawon lokacin da ganyen ya dade a rana, shi ne yawan irin sauyin da za su yi, Bisa la'akari da yawan yadda mutane ke shan shayi, akwai bukatar a san ko wannan hanya ta hada shi tana da wani tasiri a fannin lafiya.

Akwai dai shakku game da amfanin da shayi yake yi a jikin mutum, bayan dumama masa hannu da kuma sanya mutum ya kasance cikin hayyacinsa ba barci a tare da shi.

Duk da sinadaran da ke cikin ganyen shayi masu sa kuzari, tasirinsu ba wani mai yawa ba ne, amma dai za ka ji garau.

To amma me ya sa mtanen Burtaniya suke son wadannan sinadarai? Kuma me ya sa kake zaben wani ganyen a kan wani, da yawan yadda kake shan shi da kuma muhimmancinsa a wurinka?

Masaniyar halayyar dan adam Kate Fox ta rubuta a littafinta Watching the English, cewa akwai sakonni da dama da ake bayarwa a duk lokacin da dan Burtaniya ya hada shayi. Ta ce idan ka ga an hada bakin shayi ya hadu sosai , to wannan galibi ma'aikata ne ke shanshi.Mutum yana kara matsayi a cikin al'umma yana rage karfin shayin da yake sha.

Shan shayi da madara da sukari su ma suna da manufarsu. Ta ce, ''yawancin mutane a Burtaniya suna daukar sa sukari a shayi a matsayin wata manuniya ta rashin matsayi a cikin al'umma wato talakawa ne ke yin haka.

Ko da cokali daya ne ka zuba za a iya daukarka a matsayin talaka, sai dai idan kana daga cikin wadanda aka haifa kafin shekara ta 1955. Idan ka zuba cokali fiye da daya ana daukarka a matsayin na talaka na tsaka-tsaki, idan kuwa sukarin ya wuce cokali biyu to ba shakka kana daga cikin rukunin ma'aikata. In ji marubuciyar.

Sauran dabi'un sun hada da lokacin da kuma yadda ka sa madara, idan ma har ka sa a shayin. Fox tana ganin idan ka ga mutum ya hada bakin shayi irin na China (Lapsang Souchong), ba sukari ba madara, to hakan wata alama ce ta damuwa ga mutumin da yake matsayin tsaka-tsaki. Irin wannan shayin daidai yake da hadadden shayi da ya sha sukari da madara.

Mutum zai iya kawo dalilai da yawa da yake ganin suka sa mutanen Burtaniya suke son shayi, daya daga ciki dai zai iya kasancewa shayi ba abu ne da zai kawo maka wata tsutsar ciki ba.

Wani masanin kimiyyar abinci da na taba tattaunawa da shi ya gaya min cewa a ganinsa, muhalli na da tasiri wajen irin abincin da mutum yake so. Ya ce kana son abin da kake so ba lalle domin komai, ko da yake mutum zai iya samun sha'awar kusan komai.

Muhimmancin abinci ko wani abin sha a rayuwarka zai iya kasancewa ne saboda duk wani abu da ke tattare da shi, wato al'adar abin.

Asalin hoton, Alamy

Bayanan hoto,

Wasu na ganin sanya sukari a shayinka na iya nuna matsayinka a cikin al'umma

Fox ta rubuta cewa bayan sinadaransa shayi wani abu ne da yake sa mutum ya ji daidai, saboda idan dan Burtaniya ya shiga wani yanayi na rashin jin dadi ko damuwa a tsakaninsa sda jama'a, sai kawai ya hada shayi.

Haka kuma ya kamata ka sani cewa wasu daga cikin sinadaran da ke cikin ganyen shayi na hana tsuntsaye ko kwari da sauran halittu cinye ganyen ne.

Wannan abin mamaki ne sosai ganin yadda mu mutane kuma muke neman ganyen matuka da kuma irin muhimmanci da ma'anar da muke ba shi.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Why do the British love the taste of tea so much?