Ko ka san kai ma kana nuna wariya?

Hakkin mallakar hoto Alamy

Mutane da dama ba sa ma sanin suna nuna bambanci a kan jinsin launin fata. Kuma ba za su yarda ma cewa suna yin wannan abin da suke yi din ba tare da sun sani ba na nuna wariya, har sai sun ga sheda ta kimiyya.

Ga nazarin Tom Stafford

A kasar da nake akwai dokoki da suka hana nuna wariya a bisa dalilai na bambancin kabila ko addini ko jinsi (mace ko namiji). Shekaru da dama rabanmu da wannan tsari da ya haramta luwadi da madigo, da kuma nuna bambanci ga mata wajen hana su zabe.

To amma wannan ba yana nufin an kawo karshen wadannan bambance-bambance ne ba. A wannan lokacin muna bukatar mayar da hankali domin yaki da wasu 'yan bambance-bambance da kusan ba a lura da su.

Wannan kuwa shi ne irin bambancin da muke nunawa bisa hasashe na rashin tabbas da kuma gazawa ta yin kokarin sanya mutanen da ke da wani bambanci da mu ko kuma wadanda muke ganin ba su kai yadda muke so ba cikin wani aiki ko wani abu na cigaba. Kalma daya da za a iya bayyana irin wannan bambanci ita ce dan karamin mamaye.

Wadannan abubuwa ne da suka hada da yawan tsokana, ko watsi da ra'ayin wani ba tare da wani hanzari ba, duk dai wani abu da bai dace ba, wanda kuma zai sa wani mutum ya ji an nuna masa wariya.

Mutanen da suke nuna irin wannan bambanci ba lalle ba ne sun san cewa suna da wannan ra'ayi na wariya. Masana tunani da halayyar dan adam sun bambance tsakanin dabi'unmu na fili, wadanda mun san muna yinsu da kuma dabi'unmu na boye, wadanda ayyukanmu ne ke bayyana su.

Misali za ka iya cewa kai ba mai nuna bambanci ba ne tsakanin mata ko maza, amma idan ya kasance kana yi wa mata katsalandan fiye da maza a taruka, to wannan kana nuna dabi'a ce ta nuna bambanci ga mata, wadda dabia'a ce da ta saba da halayyarka da kake bayyanawa.

Dabi'ar cutarwa

Wani abu da wannan dabi'a ta nuna bambanci da ba a fili take ba, shi ne, ita wariya ce da ta kunshi 'yan kananan abubuwa da muke renawa ko ba ma dauka da muhimmanci amma kuma a yayin da muka yi su muna nuna bambanci kan yadda muke daukar wasu mutanen idan muka kwatanta da wasu.

Wannan ne ya sa yake da wuya a iya auna ta ko a magance ta, ko kuma ma ka ga wasu mutanen sun dauke ta da muhimmanci.

Lalle wasu ba sa daukar wannan bambanci ko wariya da muhimmanci, wato idan mutane suka yi korafin ana nuna musu bambanci a 'yan wasu abubuwa da ake ganin ba su taka kara sun karya ba, sai a ga kamar sun zake cewa ana cutar da su.

Ana daukar 'yan kananan abubuwa a matsayin kanana kawai, ana ganin ba su da wani muhimmanci ko tasiri a rayuwa kuma bai kamata mu mayar da hankalinmu a kansu ba.

To zan iya cewa kai kana da ra'ayinka a kan haka, amma ni abin da nake so shi ne yadda za ka iya duba tasirin irin wadannan 'yan kananan abubuwa idan suka taru da yawa.

Babban misalin illar yadda launi ke shafar mu'amullarmu na nuna yadda bambancin launi ke sa mu nuna wariya a kan yadda muke daukar wasu mutane. Kuma hatta wasunmu da ke da matsayi idan suka samu kansu a irin wannan yanayi na nuna wariya ba sa jin dadi.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hatta mutum mai mutunci da ke tantance masu neman aiki ka iya nuna wariya ba tare da ya sani ba, kuma hakan zai iya shafar ƙoƙarin wanda yake tantancewa

A farkon shekarun 1970 wani ayari karkashin jagorancin Carl Word na jami'ar Princeton sun dauki wasu dalibai farar fata domin yin wani gwaji, na duba cancantar mutanen da za a dauka aiki.

Abin shi ne su wadannan dalibai da aka sa aikin ba su san cewa, an shirya aikin ne domin gwada su kan yadda za su rika yi wa masu neman aikin ne ba a lokacin tantance su bisa launin fatarsu.

Duk da cewa sun yi amanna aikinsu shi ne su zabi mutanen da suka fi cancanta da aikin, amma sai suka nuna 'yan wasu alamun bambanci ga bakaken fata a yayin tantancewar,(kamar ta hanyar murmushi ko ta ido da motsi da jiki ko ishara) duk da cewa masu neman aikin suna can nesa da su.

Karin binciken da aka yi a baya-bayan nan a kan wannan nazari ya kara tabbatar da hakan, kuma wadannan alamu na nuna kauna ga farar fata 'yan uwansu ba sa cikin dabi'a ko halayyarsu ta zahiri.

Bambancin da aka nuna wa bakaken fatar a lokacin ya hada hadda yawan lokacin ganawar da aka ba kowanne, an gano cewa masu daukar aikin sun rage musu lokaci kashi 25 cikin dari. Wannan kadai rashin adalci ne, to amma ya za a fuskanci matsala kamar wannan?

Bayan tattara wadannan bayanai a kan wadannan alamu na nuna wariya a boye, sai masu gudanar da binciken suka dauki wasu mutanen kuma na daban suka ba su horo kan yadda za su yi kamar yadda wadancan masu daukar aiki farar fata suka yi wa masu neman aikin bisa bambancin launin fatarsu.

Wato an horar da su, kan su rika yi wa farar fata murmushi da fara'a da kusantarsu da kuma ba su wadataccen lokaci yayin ganawar, kuma su yi wa bakaken fata sabanin wadannan abubuwa, amma kuma a magana kada su nuna wa kowa bambanci, wato su mutunta kowa ba bambanci.

A gaba kuma sai masu binciken suka sake dauko wasu daliban wannan jami'a ta Princeton fararen fata su yi aiki a matsayin masu neman aiki, kuma aka sa su yi wa wasu daga cikinsu wannan karba ta nuna fifiko, a kan farar fata, wasu kuma su yi musu kamar yadda aka nuna wa bakar fata wariya.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wani nazari ya yi kokarin sa farar fata cikin irin yanayin wariyar boye da ake nuna wa bakaken fata

Sakamakon ya bamu damar ganin irin tasirin wariya, domin masu neman aikin da aka yi musu wannan wariya ta boye ta bakaken fata, ba su yi kokari ba a tantancewar, kamar yadda wasu masu duba jarrabawa masu zaman kansu suka gani.

Mutanen sun rika yin kura-kurai masu yawa, har ma sukan dan matsa baya daga mai tantance a lokacin ganawar maimakon matsawa kusa da shi, idan da an ba su fuska.

Ba abu ne mai wuya ka ga wannan a yanayi irin na daukar aiki ba, kuma abu ne da zai iya sa ka rasa damarka ta samun wani aiki.

Kuma abin shi ne alamarin da ya haifar da wannan illa shi ne halayyarmu wadda ba da baki muke furta ta ba, wadda ma yawancinmu muna yi ba tare da niyya ba ko kuma sanin muna yi.

Kuma wani abu ma shi ne yadda aka samu wannan wariya daga daliban jami'ar Princeton, wadda jami'a ce a duniya ta 'ya'yan masu hali. To idan har farar fata masu hali za su gamu da wannan matsala ta nuna wariya, to sai mu yi tsammanin mummunan tasiri ko illar wannan bambanci idan a kan mutanen da ba wasu masu hali ba ne.

Gwaji ko nazari irin wannan ba ya bayar da gaba dayan gaskiyar da ke tattare da nuna wariya. Matsaloli kamar wariyar launin fata abubuwa daban-daban ne ke haddasa su wadanda ba su tsaya a kan dabi'ar mutum ba kadai, yawanci kuma wariyar da muke nunawa a zahiri da kuma ta boye su ke kara karfafa su

Wariyar launin fata za ta shafi (mutane) masu neman aiki kafin tantancewa, da lokacin tantance su da kuma bayan tantancewar ta hanyoyi da dama fiye da wadanda na bayyana.

Abin da wannan binciken ya nuna hanya daya ce wadda ko da da kyakkyawar niyya, dabi'ar mutane ga wadanda ba su da rinjaye ka iya yin babban tasiri. Dan bambanci kadan zai iya taruwa ya girma.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Prejudice is not always overt. It's called 'microaggression'