Ko tauraron ɗan adam zai iya faɗowa kanka?

Hakkin mallakar hoto Getty

Ganin yadda ake ta samun ƙaruwar yawan tauraron ɗan adam da sauran jiragen bincike na 'yan sama jannati da ake harbawa samaniya, me zai faru idan wani tauraro ya faɗo duniya?

Masana kimiyya na Jamus na ƙoƙarin gano abin da zai iya faruwa.

Ricahrd Hollingham.

''Wannan ba shi ne abin tashin hankalin ba(tauraron dan adam) ,'' in ji Sebastian Willems yayin da masanin kimiyyar ya wuce da ni ta kusa da wani rufaffen gilashi da ke dauke da tarin wasu jiragen sama jannati na kwaikwayo, a wani ramin iska na hukumar kula da harkokin sama jannati ta Jamus (DLR), a birnin Cologne.

Daga nan sai muka shiga wani daki maras taga ta wata wagegiyar kofa, inda duk bangwayen dakin sun yi kaca-kaca, kuma ga iskar dakin na cike da warin abubuwan fashewa. A nan ne suke gwajin yadda jiragen sama jannati za su iya tashi.

Gwaje-gwajen da su Willems ke yi a nan sun kunshi amfani da wanna ramin katafaren ramuka na iska domin ganin irin abin da zai iya faruwa idan tauraron dan adam ya sulmuyo kasa daga sararin samaniya.

Ya ce, ''akwai tauraron dan dam da yawa a sama kuma ba dade ko bajima za su fado kasa. Watakila za su fashe amma tambayar ita ce, wace irin illa za su iya yi idan suka fado?''

Ma'ana wani bangare na tauraron dan adam din da ya gama aikinsa yake fadowa kasa zai iya fadawa kan wani abu ko ma a ce mutum?

Shi wannan ramin iska wanda Willems ke gwaji da shi, wata makekiyar na'ura ce da aka rirrefe da bututai da wayoyi, da aka jejjera a kan wani dabe.

Ramukan ko na'urar wadda ke iya samar da iska mai karfin gaske wadda gudunta ya linka na sauti sau 11, ana amfani da ita ne wajen gwajin tashi da shawagin jiragen sama masu dankaren gudu da kuma na 'yan sama jannati. A nan din akwai yadda Willens zai iya gwajin yadda tauraron dan adam zai iya fadowa daga sararin samaniya.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yawancin tauraron ɗan adam kan tarwatse idan zai faɗo doron duniya

Willensa ya ce, ''mu dabarar ita ce mu ga yadda abu zai fado cikin iska daga sararin samaniya. Muna son mu ga yadda yake fadowa ta cikin iska, cikin wani dan takaitaccen lokaci na dakika digo biyu (0.2), wanda kuma a cikin dan wanna lokaci za mu iya daukar hotuna da yawa kuma mu yi aune-aune.

Bayanan da aka samu a wannan gwaji za a sanya su ne a wani yanayi irin wanda aka yi gwajin amma wanna karon a kwanfuta domin a iya hasashen abin da zai faru idan tauraron dan dam ya rikito zuwa doron duniya.

Dunkulen tarkacen dubu 500 ko ma fiye da haka ya kama daga 'yan kananan karafuna zuwa tauraron dan adam da ya kai girman mota samfurin bas ko safa, kamar jirgin sama jannati na hukumar kula da samaniya ta Turai, Envisat, wanda salin-alin ya fado a watan Afrilu na 2012.

Hugh Lewis, babban malamin koyar da fasaha kan tashi da shawagin jiragen sama a jmai'ar Southampton a kudancin Ingila, ya ce, ''a tsari ya kamata mu bayyana cewa yawan abubuwan da muke turawa samaniya yana karuwa.''

Tun da tarkacen abubuwan fasaha na karuwa a samaniya, yuwuwar wani abu ya yi karo da wani tauraron dan adam ko jirgin 'yan sama jannati na karuwa.

A gaskiya ma ya kamata a rika sauya wurin da aka girke tashar sararin samaniya akai-akai domin kauce wa hadarin karo.

Lewis ya ce, ''Mun ga yadda abubuwa suke fadowa kasa daga sararin samaniya tun lokacin da aka samu fasahar zuwa samaniya, hasali ma duk kwana uku ko hudu wani babban abu na fadowa, kuma wannan abu ne da zai dau lokaci yana ci gaba da faruwa.''

Lewis ya kara da cewa, ''wadanna abubuwa da suke fadowa na tarkacen tauraron dan adam za su iya kasancewa kusan girman karamar mota.''

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Yawanci ana karkatar da tauraron ɗan adam da zai faɗo ya faɗa yankin tekun da ba wani abu

A gwajin da yake yi a ma'aikata ko raminsa na iska Willems ba yana sako kananan motoci ba ne daga sama su fado, amma yana duba yadda abu mai girma zai tarwatse ya fado daga sararin samaniya , domin ya san wanne ne daga tarkacen abin zai iso doron duniya.

To ganin yadda wadannan tarkace na taurarin dan adam da sauran abubuwa ke fadowa daga sararin samaniya akai akai, me ya sa tarkacen wadannan abubuwa ba sa cika mana filaye, suna fadowa a kan rufin dakunanmu ko kuma ma su rika fada mana a ka?

Amsar wannan tambaya ita ce, yawanci masu harba tauraron dan adam zuwa sararin samaniya suna tsara yadda tauraron nasu idan ya kare aiki zai fado doron duniya, a can wani sashe na teku.

Sai dai abin damuwar shi ne, yadda wani tauraron dan adam din wanda ya mutu ba tsammani zai fado. Daya daga cikin faduwar da aka samu a baya bayan nan ta tauraron dan adam daga sararin samaniya ita ce ta tauraron bincike na hukumar kula da sararin samaniyar Amurka (UARS) a shekarar 2011.

Duk da cewa kashi 70 cikin dari na duniya ruwa ne ya mamaye shi, kuma yawancin yakunan tudu na duniya babu mutane da yawa, Lewis ya ce duk da haka akwai yuwuwar a cikin kashi 1 cikin 2,500 hadarin wannan tauraro na Amurka da ya fado cikin jama'a a wani wuri a doron duniya.

Bisa la'akari da cewa sama da mutane miliyan daya ne suke mutuwa a hadarin mota a kowace shekara, hadarin wani bangare na wani tauraron dan adam da ya gama aiki yake fadowa kasa ya bige ka dan kadan ne.

Amma duk da haka abin damuwa ne domin kamar yadda majalisar dinkin duniya ta zartar duk akasr da tauraronta ya haddasa haka to ita ce za ta dau alhakin abin da ya faru.

Hukumomin kula da sararin samaniya a kan haka ne suke kokarin rage yuwuwar aukuwar duk wani hadari da ya danganci fadowar tauraron dan adam ko wani jirgin sama jannati da makamantansu.

Wannan gwaji da ake yi a Jamus za a yi amfani da shi wajen ganewa da kuma bin diddigin duk wasu tarkace da za su fado daga sararin samaniya, ta yadda hatta tauraron dan adam din da ba a san zai fado ba za a iya sa ido a kansa sosai idan ya subuto.

Yadda tsadar harba tauraron dan adam samaniya ke raguwa da kuma yadda ci gaban fasaha ke sa a rage girmansa, a shekaru gommai masu zuwa za a yi ta harba karin tauraron dan adam da yawa.

Lewis ya ce, ''amfanin da muke samu daga harba tauraron dan adam samaniya na karuwa amma kuma hadarin fadowar tarkacensa duniya na karuwa.''

Duk da cewa abu ne mai wuya wasu tarkace ko wani bangare na wani tauraron dan adam ya fado maka, yawan abubuwan da ke fadowar daga sama zai karu. Ba abin da za a harba sama ya tabbata a can har abada.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. Could a satellite fall on your head?