Gaskiya ne ƙasa za ta iya haɗiye mutum ya mutu?

Hakkin mallakar hoto AF ArchiveAlamy

Nuna mutum yana nutsewa a cikin kasa har ya mutu, abu ne da masu shirya fina-finai suke yawan yi a fim. To hakan abu ne mai yuwuwa a ce tabo ko kasa ta hadiye wani kasurgumin barawo ko macuci? BBC ta gudanar da bincike na kimiyya

Ga abin da Claudia Hammond ta binciko.

Dukkanninmu mun ga fina-finan. Za ka ga kasa ta kama mutum, yana ta kuka da kururuwa da rokon wadanda ke kusa su cece shi, amma yayin da yake kokarin neman tsira sai ya rika kara nutsewa, har sai ya nutse gaba daya.

Ba abin da za ka ga ya rage sai rerayi ko tabo da watakila hularsa. Akwai fina-finai da yawa da ake nuna irin wannan mutuwa ta hanyar nitsewa a kasa ko tabo, har ma dan jarida Daniel Engbar ya bi diddigin lokacin da wannan tsari ya yi tashe a fim.

A shekarun 1960, za ka ga fim daya a cikin guda uku yana da wannan bangare na irin wannan mutuwa a cikin rerayi ko tabo. Kusan duk wani fim da ka duba a wancan lokacin za ka ga wannan abu.

Amma kuma shedar da ke tabbatar da cewa kana ci gaba da kokarin tsira, kasar na kara hadiye ka ko kuma kana kara nitsewa a tabon, babu wata gaskiya game da ita.

Yawanci irin wannan kasa da za ka ga tana hadiye mutane, ta rerayi ne ko tabo da kuma gishiri wanda ruwa ya mamaye wurin da yake, musamman a yankunan bakin wutsiyar koguna.

Za ka ga kasar wurin tana da alamar karfi a ido, amma idan ka taka ta sai ta fara kwabewa (da ruwa). Amma kuma daga nan sai ruwan ya fara rabuwa da kasar.

Dankon da ke tsakanin kasar ya ragu sosai, abin da ke nufin kasar ba za ta iya daukar nauyinka ba kuma, sai ka fara nutsewa.

Gaskiya ne cewa duk wani motsi ko kokari da za ka yi na kada ka nutse zai sa ka kara nutsewa, amma kasar za ta ci gaba da hadiye ka har ka kai ga nutsewa gaba daya?

Hakkin mallakar hoto AF Archive Alamy

Daniel Bonn daga jami'ar Amsterdam yana Iran lokacin da ya ga wata sanarwa da ke gargadin masu ziyara a kusa da wani tafki kan hadarin cewa mutum zai iya nitsewa a wurin.

Daga nan sai ya debi kasar wurin ya je da ita dakin bincike na kimiyya, ya yi nazarin yawan tabon da ke cikinta da ruwan gishiri da kuma ainahin kasar da ke cikin, daga nan sai ya tsara wani yanayin yadda kasa ke rasa dankonta ta zama ba ta iya rike wani abu mai nauyi a kanta (kamar yadda take zama har mutum ya nutse a cikinta).

Maimakon ya yi amfani da mutane sai ya yi amfani da kwayoyin misali carbi na goran ruwa (aluminium), wadanda suke da kusan irin yanayin nauyin mutum.

Sai ya dora su a kan wannan kasa da ya sarrafa, sannan kuma ya kirkiri irin yanayin tsoro da rudewar da mutum yake shiga a lokacin da kasa ke tabo ke hadiye shi ko yake nitsewa a ciki, sai ya rika girgiza abin da ya zuba kasar ya dora kwayoyin, ya tsaya ya ga abin da zai faru. Ko kwayoyin goran ruwan za su nutse?

Amsar ita ce a'a ba su nitse ba. Da farko dai sun dan fara nutsewar kadan, amma yayin da kasar ta fara haduwa da ruwa kamar da sai dankonta ya karu, sai kwayoyin suka dawo sama inda suke.

Bonn da abokan bincikensa sun yi ta jarraba abubuwa da dama a kan wannan irin kasa ko tabo da mutum ka iya nuitsewa a cikinsa, da ya hada a dakin kimiyya, ya ga ko abubuwan za su nutse a ciki amma hakan bai faru ba.

Idan nauyi iri daya suke da shi da mutum za su nutse, amma kuma ba sa nutsewa sai dai su kai rabi kawai.

Ko da yake wannan kasa maras karfi ba za ta iya janka ta nutsar da kai ba, to me kuma ya sa tun da har kimiyya ta yi hasashen ba za ka yi ta nutsewa a ciki ba, me ke sa a wani lokaci ake samun hadarin da za a ce mutum ya nitse, kamar yadda wata mata me 'ya'ya biyu ta nitse a 2012 lokacin tana hutu a Antigua ?

Dalilin shi ne idan har ba za ka iya fita daga irin wannan kasa ko yumbu ba idan ka fara nutsewa to ambaliyarta ka iya rufe ka. To a wannan lokacin za a iya cewa wannan kasa tana da hadari.

Saboda haka a ce kai daya ka yi kokarin tsirar da kanka, hakan ba zai sa ka nitse ba, amma duk da haka sai mu yi hankali.

Domin idan kana son cetar kan naka ba tare da wani ya taimaka maka ba, kafin kasar ko tabon ya yi sako-sako, to binciken Bonn ya nuna cewa kafin ka iya fitar da kafarka daya kawai kana bukatar karfin da ya kai na daga mota mai matsakaicin girma (100,000 newtons) .

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nitsewa a rumbun hatsi ka iya zama babban haɗari

A binciken Bonn da abokansa sun gano cewa gishiri yana da muhimmanci a cikin kasar ko yumbun domin yana kara rage dankon kasar wanda hakan ke sa yumbun ko kasar ba ta iya daukar abu mai nauyi.

Amma kuma wasu masu binciken wannan karon daga Switzerland da Brazil, sun gano cewa akwai irin wannan kasar da ba sai da gishiri take iya zama haka ba.

Sun gudanar da binciken ne a wani tabo ko kasa da suka diba daga wani bangare na wutsiyar teku a gabashin Brazil, inda suka gano cewa akwai wata kwayar bakteriya da take haifar da irin wannan hadin kasa ko yumbu, wanda za ka ga kamar yana da karfi daga sama amma da ka taka da kafa sai tabon ya dare.

Amma kuma ko da ma tabon yana hadiye mutum, muhimmin abu shi ne irin wannan tabo ba shi da zur fi ko yawan da zai shanye tsawon mutum gaba daya.

Amma kuma busasshiyar kasa ko tabo kuma yanayin daban yake da wanda yake jikakke. Nitsewa a cikin misali rumbu cike da hatsi zai iya kasancewa matukar hadari, domin a nan kana bukatar taimakon gaggawa.

A shekara ta 2002 an samu rahoton wani mutum wanda ya fada rubun hatsi da alamuru a wata gona a Jamus.

Kafin masu ceto 'yan kwana-kwana su gane rumbun da ya fada daga cikin guda takwas da ke wurin, ya nitse har zuwa hammata, kuma kokarin da yake yi na fita da kanshine yake sa yana kara nutsewa

A duk lokacin da ya fitar da numfashi sai girman kirjinsa ya ragu, abin da ke sa hatsi ya maye gurgin da ya ragu, kuma hakan na kara sa shi wuyar samun yin numfashi.

Daga nan sai aka yi dabarar tura likita inda yake ta hanyar amfani da igiya, ya sanya mishi abin da zai rika shakar iska yana samu ya yi numfashi (irin na asibiti), kuma aka sa wata ragama a kewayen kirjin mutumin domin ta hana shi kara tsukewa.

Amma kuma bayan wani dan lokaci sai kirjinsa ya fara ciwo, shi kuma likitan cutar matsalar numfashi ta asma ta same shi saboda kurar rumbun

Sai 'yan kwana-kwanar suka yi wata dabara, inda suka kai wata garwa, suka sa ta a kewayen mutumin, daga nan sai suka yi amfani da wata na'ura suna zuke hatsin da ke kewayen mutumin, wanda hakan ya sa hatsin ba ya matse shi kuma, ta hakan aka samu aka ceto shi.

Idan ka fada cikin tarin kasa ko rerayi maras karfi da za ka iya nitsewa, kana bukatar taimakon wani da gaggawa. Amma kuma idan tabo ne fa (jikakke), ba ka nitse ba amma dai ya rike ka?

To abin da za ka yi a nan idan kai daya ne sai ka rika motsa kafarka domin tabon da ya rike ma kafa ya ja ruwa sai ya yi sako-sako.

Dabarar ita ce ka da ka tayar da hankalinka (wanda abu ne mai wuya), ka kwanta baya ka buda kada ka sa wani bangare na jikinka ya rinjaya, har sai ka ji kana yi sako-sako kana iya tasowa sama.

Kuma fa kada ka manta da malafarka.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa na. Can quicksand really suck you to your death?