Menene ke rayuwa a ƙarkashin farcenka?

Hakkin mallakar hoto Getty

Wanke hannuwanku shi ne matakin farko na kare kanka daga duk wasu ƙwayoyin halitta masu cutarwa. To amma kana ma wanke ƙasan farcenka?

Ya dai kamata a ce kana yi...

Jason Goldman ya yi mana nazari kan wannan

Watakila ka san cewa wanke hannu na daya daga cikin hanyoyin da suka fi dacewa na kariya daga watsuwar kwayoyin cuta.

A wurare da dama akwai dokokin da aka yi na musamman domin tabbatar da ganin cewa wadanda suke aiki a wuraren abinci suna tsaftace hannuwansu a ko da yaushe.

To sai dai kuma babu irin wankin da za ka yi da zai taba raba hannuwanka da duk kwayoyin bakteriyar da suka kama zango a hannuwan naka.

Wannan shi ne ya sa likitoci da ma'aikatan jiyya suke sanya safar hannu a duk lokacin da suke duba maras lafiya musamman ma kan cewa dafa kayan aiki da ake yi shi ma ba zai iya ba da kariya ga kamuwa da dukkanin kwayoyin cuta ba.

Tun kusan shekara dari da ta gabata likitoci suka fara gano cewa duk irin wankin da aka yi ko da sau nawa ne sai an samu wasu kwayoyin cuta na bakteriya.

Amma sai a shekarun 1970 ne masu bincike suka fara gano dalilin da kwayoyin cuta na bakteriya ke ci gaba da makalewa a hannun mutum ko da ya wanke.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Farcen ado ya fi na ainahi tara ƙwayoyin cuta

An gano cewa rufe bakin dan yatsa zai iya sa hannunka ya kasance cikin tsafta tsawon lokaci ko da yake ba bakin dan yatsa din ba ne yake tara kwayoyin cutar, farce ne ya ke ba su mafaka.

Sai a shekarun 1980 ne masana kimiyya suka fara gudanar da bincike domin gano su wanene ke rayuwa a karkashin farcenmu.

A shekarar 1988 wasu masu bincike guda uku daga jami'ar Pennsylvania suka yi nazari a kan hannuwan wasu ma'aikatan shashen koyon aikin likita na jami'ar su wadanda ba su yi wata mu'amulla da marassa lafiya ba. A binciken sun gano cewa karkashin farce wata matattara ce ta kwayoyin bakteriya haka kuma sauran sassan hannun ma'aikatan ma na bayar da mafaka ga daruruwan kwayoyin cutar, amma kuma karkashin farcen shi ya fi tara dubban kwayoyin a duk yatsa daya.

Kwayoyin cutar da akae samu a karkashin farcen daya suke da wadanda ke sauran sassan hannun illa dai karkashin farcen ya fi tara su.

Dan filin da ke tsakanin farcenka da yatsa wuri ne da ya fi tara kwayoyin saboda kariyar da yake ba su da kuma lemar da ke wurin, saboda haka ne ake samun dubbansu na rayuwa a nan, su girma su kuma hayayyafa.

Masu binciken sun rubuta cewa, abin da aka gano tun kafin nazarin nasu da ke nuna cewa yawan wankin da ake yi wa hannu ba ya kawar da dukkanin kwayoyin cuta a hannu, da kuma abin da suka gano su ma cewa wannan karkashin farce matattara ce ta dubban kwayoyin cuta, zai iya tabbatar da maganar da ake yi cewa maganin kashe kwayoyin cuta da ake amfani da shi a yayin wanke hannu ba ya kaiwa wurin.

Wannan wuri wato karkashin farce wuri ne da hatta ingantattun matakan kariya daga kwayoyin cuta ba kasafai suke yin tasiri a wurin ba. Wani sabon fagen bincike ma na ci gaba da kokarin tabbatar da irin kwayoyin halitta na cuta da ke rayuwa a faratan ma'aikatan jiyya. Kuma ba wai faratansu na asali ba, hatta na gayu da suke sanyawa kwayoyin cutar kan makale a jikinsu, ko ma faratan da aka sa wa jan farce.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kowane kan ɗan yatsa zai iya zama matattarar dubun dubatar ƙwayoyin bacteriya

A shekarar 1989, shekara daya bayan binciken na jami'ar Pennsylvania , wasu ma'aikatan jiyya sun rubuta cewa, ''ko da yake ba a yi wasu bayanai game da rashin hadarin tara cutuka da farata na ado suke yi ko za su iya yi ba, ma'aikatan lafiya da dama sun karkata ga amfani da farata na ado".

Masu binciken suna son ganin ko wasu ma'aikatan jiyya 56 da suka sanya farce na ado, wanda ya fi nasu na ainahi tsawo, kuma kusan an rufe shi da jan farce, ko sun fi faratan wasu ma'aikatan jiyyar 56 masu farce na ainahi tara kwayoyin bakteriya (cuta).

Haka kuma suna son sanin ko wanke hannu ya fi tasiri ko rashin amfani a hannun masu faratan ado.

Masanan sun gano cewa masu faratan ado sun fi masu farata na ainahi yawan kwayoyin cuta a faratan kafin wanke hannu da kuma bayan wanke hannun.

Wannan ba yana nufin sun fi yada kwayoyin bakteriya ga marassa lafiyar da suke yi wa magan ba fa kenan, illa dai cewa kwayoyin bakteriyar da ke faratan nasu suna da yawa sosai.

Wasu bincike-binciken da aka wallafa irin wadannan a 2000 da 2002 ysun bayar da sakamako iri daya. Amma zuwa wannan lokacin masu bincike na aikin jiyya sun samu shedar da ke nuna cewa farcen ado na tabbatar da dabi'ar rashin wanke hannu da kyau, wadda ke kara matsalar.

Kuma sun gano cewa faratan ado za su iya huda safar hannun da ma'aikatan jiyya ke sanyawa.

Shi kuwa farcen ainahi da aka sanya wa jan-farce, wata matsala daban ya nuna, matsalar kuwa ita ce 'yan mitsi-mitsin abubuwan da ke cikin fentin ko 'yan wuraren da fentin bai rufe ba da kyau za su iya bayar da mafaka ga kwayoyin bakteriya.

A shekarar 1993,ma'aikatan jiyya a asibitin Johns Hopkins da ke Baltimore a Amurka sun duba faratan wasu manyan mata 26 wadanda asibitin ya dauke su aiki, amma kuma ba sa mu'amulla da marassa lafiya. Dukkaninsu ba su da faratansu gajeru ne, kuma an bincia su kafin da kuma bayan kwana hudu da sanya wa faratansu jan-farce

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wanke hannu ba zai isa ba dole ne sai ka tabbatar da tsaftar faratanka

Abin da binciken ya nuna shi ne sanyawa farce na ainahi jan-farce, ba ya nuna wata alama ta kara yawan kwayoyin bakteriyar da ke farcen, kamar yadda farce na ado da aka sanyawa jan-farcen yake yi. Sai dai barin farce ba tsawo kuma cikin tsafta, ga alama ya fi muhimmanci a kan ko an yi wa farce jan-farce ko ba a yi masa ba, in ji masu binciken.

Wani binciken da ka yi shi ma shekara daya bayan wannan na fari ya tabbatar da irin wannan sakamako, inda aka ga farcen da aka sanya wa jan-farce sama da kwana hudu ya fi yawan kwayoyin bakteriya, kuma wanda aka sa mi shi jan-farcen ba jimawa ba ya dauke da kwayoyin cuta.

Kusan mutane miliyan biyu zuwa uku ne suke mutuwa a duk shekara a sanadiyyar kamuwa da cutar amai da gudawa, wadda kazanta ke haddasawa. Kuma ana ganin wanke hannu da sabulu zai iya kare kusan miliyan daya a cikinsu.

Amma kuma bayan wanke hannu da sabulu, abin da yafi dacewa mutum ya yi kusan a zahiri yake, wanda shi ne lura sosai da sakon karkashin farcenka lokacin da kake wanke hannu, kuma idan kana son samar da yanayin da ba za a samu kwayoyin halitta na bakteriya masu yawa a yatsunka ba, ka rika yanke faratanka da kyau, kada su yi tsawo sannan ka tsaftace su.

Dukkanin wadannan matakai za su sa ka yi tunani kafin ka gaigayi faratanka.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. What lives under your fingernails?