Ka san sirrin na'urorin cacar kalo-kalo?

Hakkin mallakar hoto Getty

Sirrin na'urorin kalo-kalo na caca haɗi da dabarun yaudara kan yadda ake sa farashin abubuwan da kuma yadda fasaha ta sa wasunmu yin kasada, waɗannan na daga abubuwan da jama'a da dama suka mayar da hankali wajen karantawa a wani rahoto da aka wallafa a watan Mayu na 2015.

Ga nazarin Robert Cottrell

Basira ta sanadin karuwar na'urori

Mutum-mutumi mai fasahar komai da ruwanka zai iya raba ka da aikinka, amma kuma abu ne mai wuya ya iya karbe ayyukan duniya baki daya, akalla dai daga irin fasahohin da ake iya hasashe a yanzu.

Zurfin bincike ya fargar da mu kan burinmu na samun fasaha ta na'urori; a kan hakan, bisa dan umarni ko sarrafawar mutanw, na'urori za su iya yin dokoki na ganewa da kuma rarraba abubuwan da ke kusa da su, a yawancin lokaci ma har sun fi mutane yin abin da kyau. Amma duk da haka na'urorin ba su da dalili (na yin abu) da kuma sha'awa kamar yadda dan adam yake da.(daga mujallar, The Economist).

Caca da masu tsara yadda abu ke zama jiki ga mutane

Fasahar tsara yadda abu ke zama jiki ga mutum kamar yadda aka yi nazarinta yayin ziyarce-ziyarce zuwa Las Vegas, babbar cibiyar kamfanin Bally wanda ya kirkiro na'urar cacar kalo-kalo da ta IGT, wadda ke gaba a fagen samar da na'urar cacar kwamfuta.

Injinan caca na'urorin ne masu sarrafa lambobi da fuska irin ta talabijin ko kwamfuta kawai , sauran abubuwan da ke tattare da su dabaru ne na tallace-tallace kawai.

''Sanya irin wannan wasa na caca a tsari irin na fasahar zamani ta akwatin talabijin irin na zamani ya kara wa mutane sha'awar yin cacar daga kashi 30 cikin dari zuwa kashi 80.'' Kuma ydda mutum zai iya samun nasarar cin kashi 45 na abin da ya sa ya shiga cacar wannan ya kawar masa da duk wata fargaba ta yin cacar. In ji Andrew Thompson mawallafin littafin Verge.

Lambobi. Yadda ake amfani da sanya farashi a ja hankalin mutane

Wannan ya kunshi tarin manyan dabaru. A takaice rubutu ne mai yawan gaske, wanda kuma aka yi shi cikin sauki, wanda ke nunawa karara dalilan da ke sa a sanya wa kaya ko wani abu farashin da ake sa masa, har zuwa abin da ya sa ake cire alamar dala a farashi ko kudin abinci a takardar kudin jerin abinci a wuraren sayar da abinci.

Har ma da farashin da masu manyan kantuna ke sanyawa wanda ke jan hankalin jama'a kisali na 0.99, wanda kawai dabara ce ta nuna alamar zaftare farashi. Ko da muna ganin mun fahimci dabarar ana yaudararmu cikin sauki da ita.

Tattaki zuwa duniyar sama. Dumokradiyyantar da samaniya.

Akwai bukatar sabbin dokoki na tafiye-tafiye zuwa duniyar sama jannati, ganin yadda jiragen sama jannati da tauraron dan adam ke shiga hannun kusan kowace kasa a duniya da ma mutane masu zaman kansu masu yawa.

A lokacin da aka sanya hannu a dokokin sama jannati na yanzu kusan shekara 50 da ta wuce, zuwa sama jannati abu ne da za a ce an ware shi kawai ga manyan kasasahen duniya.

Amma a yanzu kungiyar kimiyya ta wata makaranta da ta samu kudi sosai za ta iya tura tauraron dan adam samaniya. Cigaban fasahar kwamfuta ma da na na'urar samfura (3D) za su iya ma rage farashin yin hakan. Kamar yadda kasidar Dave Baiocchi da William Welser IV, mai taken Foreign Affairs, ta bayyana.

Falsafa. Za mu iya iko da rayuwarmu kuwa?

Tsohon babban limamin cocin Ingila ya yi talifin wasu littattafai a kan 'yanci da akidar rashin yadda da Ubangiji wadanda Julian Baggini da John Gray da Alfred Mele suka rubuta, inda ya ce, ''mun zama 'yan fursunar hoto, inda zama cikin 'yanci shi ne na iya aiyanawa gaba daya wanene ko menene ni.

Hadakar maganganu irin na akidar da ke cewa mutum ne ke da alhakin duk abin da ya faru da shi da kuma akidar tsananin kishin addini da aka dora a inda ba ta dace ba su ke karfafa mana guiwa a ra'ayin cewa dole ne mu yarda ba tare da wata tantama ba, cewa mu ne sanadin duk abin da muka yi kafin mu dauki alhakin ayyukanmu.''

Juyin halitta. Yadda na fahimci rayuwa

Tattaunawa a kan yadda halitta ta samu. Babu maganar kalmar 'Ubangiji' gaba daya a cikinta. ''Idan har muka taba samun wata halitta a wani wuri a duniya, zai kasance ne bisa dalilin wani abu kamar kwayoyin halitta (DNA), wadanda suke iya juyewa su zama wata halittar.

Motoci. Ka yi tunanin gwajin tukin mota mai amfani da fetur

Motoci masu aiki da fetur ba kara da datti kawai suke da su ba suna kuma da wahalar rikewa (tsada). ''Nawa za ka kashe ka zuba musu mai a gida, kuma gidajen man fetur na kyauta guda nawa ne?

Sai me sayar da motocin ya kalle mu cike da mamaki, ya ce ai ba ta yadda za a iya zuba wa mota fetur a gida kuma babu inda ake samun gidajen mai na kyauta. Sai dai a duk wata ka je da motarka gidan mai ka sayi fetur a farashi mai tsada.

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The secrets of slot machines