Me ke sa mutane cin farar ƙasa?

Hakkin mallakar hoto Josh Gabbatiss

Al'adar nan ta cin farar ƙasa da ake kira kalaba abin mamaki ta zama ruwan dare, kuma yayin da ake ɗaukarta a wasu ƙasashen duniya a matsayin cuta, a wasu kuwa ƙarfafa wa mutane guiwa ake yi su yi ta.

To amma me zai sa a ce mutane suna son cin abin da a takaice za a ce datti ne kawai?

Josh Gabbatiss ya bincika lamarin

Sheila tana 'yar karamar yarinya a Kamaru a lokacin da ta saba da cin farar kasa( kaolin) ko kalba.

''Ina makarantar furamare,'' in ji ta. ''Gwaggona tana cinta, kuma a mafi yawan lokaci ni ce zan je in sayo mata.'' A yanzu Sheila tana karantu ne a jami'ar Faransa.

Ta ce mutane da yawa a kasarsu suna cin kasar kullum. wasu ma ta zamar musu jiki, ba za su iya zama ba tare da ita ba. Farar kasa ba aba ce da ke da wuyar samu ba, za ka iya samunta a yawancin kasuwannin Kamaru, amma ba ta daga cikin abubuwan da aka haramta ci.

Ita kalaba ba wata muguwar kwaya ko wani abu ne me sa maye ba. Datti ne kawai.

Al'adar cin datti tana da dadadden tarihi a Kamaru. Rubuce-rubucen lokacin mulkin mallaka na yankin sun bayyana dabi'ar soai. Wani marubuci da abin ya ba shi mamaki sosai ya ce, ''an gaya min cewa kusan duk yara suna cinta,'' a rubutun da ya yi a kan mutanen Batanga .

Ya kara da cewa , ''hatta wadanda ke hannun 'yan mishan ma suna cinta duk da cewa ba sa daga cikin wadanda za a ce sun san wata aba yunwa.''

Hakkin mallakar hoto Sera Young
Image caption A yawancin kasuwannin ƙasashen Afrika za ka ga farar ƙasa ta ci ta sayarwa

Kamar yadda Sera Young, kwararriyar a kan nazarin al'adar cin datti wadda take a jami'ar Cornell da ke Amurka, ta ce dabia ce da take da dadadden tarihi a duniya.

Young ta yi kusan shekara 20 tana bincike a kan wannan al'ada, kuma a rubutun da ta yi, inda ta yi nazari a kan kusan bayanai na tarihi 500 na da, da na yanzu a fadin duniya, ita da abokan bincikenta sun tattara bayanai kan yadda al'adar kusan za a ce ta bazu a duniya.

Al'ada ce da ake da ita a kasashe irin su Ajentina da Iran da Namibiya kuma kusan akwai dabi'u a kanta da suke kusan daya a wasu kasashen.

Wannan kuwa shi ne kusn an gano cewa an fi yinta a kasashe masu zafi, kuma rukunin mutane biyu sun fi yinta, musamman yara da kuma mata masu juna biyu.

Bayanin rashin yinta sosai a wasu wuraren ko kasashen zai iya kasancewa sakamakon kin bayar da rahotanninta ne bis dalilai na saba al'ada.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Don muna sha'awar abu hakan ba ya nufin yana da kyau ga lafiyarmu

Wannan al'ada ta cin abin da ba abinci ba na faruwa ne a gabanmu in ji Sera Young, tana mai bayar da misalin wata fitacciyar mawakiya a birnin New York na Amurka wadda wani sirri nata shi ne son cin wannan kasa idan tana da juna biyu.

Young' ta samu wannan sha'awa ne ta yin nazari a kan wannan al'ada ta cin kasa a lokacin da take wani bincike a wata karkara a Tanzania . "Ina yi wa mata masu juna biyu tambayoyi ne a kan larurar karancin jini a jiki a sanadin rashin sinadarin da ake kira ayon (iron) ne,'' ta ce.

"Ina zaune ne a dandamalin gidan wata mata mai juna biyu ne ina tambayarta abin da ta fi son ci idan tana da ciki, sai matar tace min:'A duk rana ina banbarar kasar bangon dakina ne in ci.'"

Wannan magana ba kada Young. ''Cin kasa ya saba wa duk wani abu da aka koyar da mu mu yi,'' in ji ta.

Tsarin likitanci na kasashen Turawa ya dauki al'adar cin datti a matsayin al'adar da ta zama jiki a wurin mutum, wadda zai aikta ta ya cutar da kansa da niyya kamar shan ruwan bilichi ko hadiyar gilashi

A kasar Kamaru babu wata alkunya ko laifi a kan al'adar. Young ta kara shan mamaki,a lokacin da take aiki aKenya, inda ta ga ana sayar da farar kasar wadda aka kawata a fakiti-fakiti da dandano iri daban-daban.

A jihar Georgia wadda ta yi fice saboda nau'ukan farar kasar masu kyau, har ma da shafin intanet na tallarta, wadda kuma duk da cewa an yi ta fakiti-fakiti inda aka rubuta ba abin ci ba ne, kowa ya san abin da ake yi da ita.

Hakkin mallakar hoto Josh Gabbatiss
Image caption Cin kalaba zai iya samar da sinadaran da muka rasa a jiki?

Young ta tambaye ni ko a unguwarmu yankin kudancin Landan (South London) akwai wani kantin da ake sayar da kayan abinci da sauran kayan gida na Afrika. Na ce e akwai. Sai ta ce min, ''to ki je kawai ki shiga ki ce a ba ki kasar masu ciki. Za ki samu ba wata tantama.''

Bayan sa'a daya na je wani kantin sayar da kayan abinci irin na Afrika, sai ga shi na fito da wata mulmulalliyar kasa a hannuna wadda na saya kusan fan daya.

Ko da na sanya ta a baki na tsaya ina kokarin in gano abin da dandanonta ke kama da shi, inda da farko na ji kamr kifi banga, kafin daga karshe na ce, kai kamar datti kawai take

Hakkin mallakar hoto Josh Gabbatiss
Image caption Wannan ƙasar za ta iya kasancewa da ƙwayoyin cuta

Na yi mamakin abin da ke sa mutane cin wannan kasa, har su saba da ita. ''Kowa yana da dalilinsa,'' in ji Monique, wata dalibar Kamaru. ''Sha'awa ce kawai, ko maganin amai ko ciwon ciki.'' To kenan maimakon a ce al'adar cuta ce, wato magani ce kenan?

An bayar da misalai ko dalilai uku na abubuwan da ake gani suna sa mutane cin kalba, kuma amsar da Monique ta bayar ta tabo guda daya daga ciki.

Datti ba su taru sun zama daya ba. Kalba tana wani rukuni ne na farar kasa, kuma ita ce wadda mutane suka fi so idan suna sha'awar cin kasa. Farar kasa za ta iya ba wa mutum sinadarin da ba zai samu ba a abinci na sosai.

Kalba na da amfani sosai wurin hada abubuwa, wannan ne ya sa ma lokacin da Monique ta yi maganar cewa tana maganin ciwon ciki, ake ganin tana yin hakan ne ta yadda take hana wasu abubuwa masu guba walwala a cikin mutum.

Gwajin da aka yi da beraye da kuma birai ya nuna cewa hatta dabbobi sukan nemi yin amfani da wasu abubuwan da ba abinci ba domin mgance gubar da suka hadiya.

Kuma hanyoyin hada abinci na gargajiya daban-daban sun kunshi hadi abinci da farar kasa ko tabo ta yadda maganin zai fi dadin ci ko sha.

Akwai 'ya'yan itatuwa masu kwaya wadanda gaba daya ba su da dadin ci amma kuma yadda ake hada su shi a California da Sardinia ya hada da nike kwayar da ke cikinsu da farar kasa domin rage dacin kwayar cikin 'yan itacen.

Dalili na biyu kuma da ya sa ake ganin kila shi ya sa ake cin farar kasar shi ne, kalabar za ta iya samar da sinadaran da babu su a cikin kayan abinci. Yawanci ana danganta cin abu mai datti kamar kasar da cewa za ta iya karawa mutum sinarin ayon (iron) na jini.

Hakkin mallakar hoto Sera Young
Image caption Farar ƙasa wadda ake kira kalaba a wasu wuraren na jiran masu saye

Akwai kuma masu ganin cewa cin irin wanna abu mai datti ya samo yana faruwa ne saboda tsananin yunwa, ko rashin sinadaran gina jiki, abin da ke kai mutane ga sha'awar kasar.

Dalilan farko guda biyu suna nuna alamu da dalilin yin wannan dabi'a. Young ta ce, ''mun yi hasashen cewa yawanci al'ada ce da ake yi a yankin kasashe masu zafi, saboda nan ne ake da yawan kwayoyin cuta.

'' Ta kuma kara da cewa Yara da mata masu juna biyu sune rukunin mutanen da suka fi bukatar kwayoyin kariya daga cuta, saboda garkuwarsu tana da rauni.

Shakka babu akwai matsala a tattare da cin datti, domin akwai yuwuwar cewa sinadaran da babu su a jikin ake kokarin samar da su ta hakan, zai iya kasancewa hakan ne ma ke haifar da rashin nasu.

Za ka iya watsi da wannan al'ada ta cin farar kasa da cewa dabi'a ce kawai ta yara da kuma kwadayin mace mai ciki, ko kuma wata dabi'a ta can wasu kasashen nesa, to amma babu daya daga cikin wadannan dalilai da za ce sun yi wa maganar adalci.

Musamman ma ganin cewa danganta duk wadannan dalilai da al'adar kamar nuna wariya ne ga mutanen da suke cin kasar, kuma abin ya zamar musu jiki, amma kuma su kansu ba za su iya gaya ma dalilin da ya sa suke cinta ba.

Kafin a fahinci wannan dabi'a da kyau a san ko tana da amfani ko illa ko ta hada duka biyun, sai masu bincike sun yi cikakken nazari mai zurfi da zai yi la'akari da abubuwan da suka shafi fannin lafiya da kuma na al'ada.

''Ba wai fa a nan ina cewa 'kowa ya rika cin cokali uku na farar kasar (kalaba) bane a kowace rana ba''', in ji Young. ''Amma dai a gaskiya zuwa yanzu ba mu da dalilin da zai sa mu ce al'adar ba ta da kyau gaba daya.''

Idan kana son karanta wannan a harshen Ingilishi latsa nan. The people who can't stop eating dirt