'Yar tsanar da ta fi mutum ƙashin-arziƙi

Wannan labarin wata 'yar tsana ce mai halayyar dan adam wadda ta zamo abin so ga kowa a kasar Japan. Neil Steinberg ya yi bincike kan amfani da abubuwa kanana da ke debewa mutane kewa kamar 'yar tsana, a kimiyyance da kuma a al'adance.

A ranar 14 ga watan Afrilu 2016, an samu girgizar kasa mai girman 6.2 wadda ta daidaita tsibirin da ke kudancin kasar Japan na Kyushu.

Girgizar kasar dai ta zubar da gidaje, al'amarin da yasa mutane suka rinka gudun ceton rai a kan titunan garin. Burbushin girgizar ya kuma cigaba har zuwa wasu 'yan kwanaki, a inda mutane 49 suka mutu kuma wasu 1,500 suka jikkata baya da dubban da suka yi kaura.

Daga nan ne kuma sai labari ya fantsama a duniya ta kafar sada zumunta. Wata mace mai suna Margie Tam ta wallafa a shafinta na sada zumunta cewa "An samu girgizar kasa," "Kumamon abin bai shafe ka ba?"

"Kumamon, da fatan kai da abokanka kuna cikin koshin lafiya?" Eric Tang, wani dalibin kwaleji yake tambaya.

Shi ma Ming Lee daga Thailand ya wallafa "ku yi wa Kumamato da Kumamon addu'ar tsira daga bala'i." An kuma ta wallafa wannan neman addu'a fiye da sau dubu.

Kumamato dai birni ne mai mutane da yawansu ya kai 700,000 a lardi mai albarkatun noma da ke kudu maso yammacin Japan.

To tambayar a nan ita ce, shin mene ne kuma Kumamon? Kuma me yasa girgizar kasa ta zama silar mayar da hankalin jama'a a kan Kumamon shi kadai?

Kumamon dai yana da kwarjini a idon mutane. "Ya kasance matsakaici abin sha'awa ga yara." in ji Tam, a lokacin da na tambaye ta me yasa ta damu da Kumamon a lokacin da aka yi girgizar kasa.

Al'amarin yana da dan rikitarwa.

Image caption Wata dattijuwa tare da Kumamato

A ranar 12 ga watan Maris 2016, wata daya kafin afkuwar girgizar kasa a Japan, Kumamon ya halarci wani shagali na tunawa da ranar haihuwarsa a Kumamato. Kimanin mutane 150 ne suka halarci shagalin da suka hada da mata kuma sun yi ta zuga shi tare da tafa masa da yin busar shauki a gare shi. Yana da bakin gashi mai sheki a jikinsa da manya kuma zagayayyun jajyen kumatu sannan kuma idanunsa sun kasance dara-dara. Tsawonsa ya kai kafa biyar. Ya sanya jaket mai launin azirfa tare jan laktai a wuyansa. Wata mace a wurin taron ta rikewa Kumamon 'yan tsanarsa da ke kwance a cikin makunshin jarirai. Wata macen ita ma ta sanyawa 'yar tsanar tata tufafi ruwan toka irin wanda ita ma ta sa. Ta ce ta kwashe kimanin wata guda wajen dinka kayan. 'Yan kallo da dama sun lika jar takarda a kumatunansu domin kwaikwayon Kumamo. Mutanen da suka samu sahun farko sun ce wurin shagalin ne tun karfe 3 dare saboda su samu wurin zama domin su yi taozali da Kumamo ba tare da shamaki ba.

"Gaskiya, ban san dalilin da yasa nake shaukinsa ba," in ji Milkinikio Mew, wata wadda ta yi tafiyayyiya tun daga Hong Kong. Ta yi barci saboda haka ta makara kuma ta zamo a sahun karshe. To amma fa ta zo ne da karfe shida na safe wurin taron da ya kamata a fara shi da karfe 10 na safen.

Shi dai wannan Kumamon ba za a ce kai tsaye mutum mutumi ba ne kuma ba mutum ba ne domin baya magana amma kuma hotonsa ya kauraye yankin.

Bugu da kari, Kumamon ba shi da sha'awa irin ta dan adam. To amma a lokacin Empress Michiko ta hadu da Kumamon a Kumamato a 2013, ta tambaye shi cewa "Ba ka da aure?"

To ke nan Kumamon wace irin halitta ce?

Shi dai Kumamon wani..... To shi ke nan bari mu ji kyautar da kamfanin Honda ya yi masa a lokacin shagalin bikin tunawa da ranar haihuwarsa. An fito da nakiyar da ake yankawa ranar shagalin tunawa da ranar haihuwa da aka fi sani da 'cake' a turance. Mahalarta taron suna ta faman rera wakar 'happy Birthday' wadda ke nufin muna taya ka murnar zagowar ranar haihuwa. Ana haka sai kuma aka fara ruwan mika kyautuka. Wani wakili daga kamfanin Honda wanda ke da masana'antar kirar babur a kusa da wurin da ake shagalin, ya mikawa Kumamon kyautar babur kirar Vespa mai suna 'scooter' wanda aka kera musamman domin shi.

Image caption Hoton Kumamato a kan jakunkuna.

Haka ma kamfani mai yin kekuna na Italiya, ya ba wa Kumamon kyautar keken tsere da aka kera na musamman saboda shi. An kuma ba shi kyautar faifan DVD mai dauke da salo daban-daban na motsa jiki.

Shi dai Kumamon ya kasance Yuru-Kyara da yaren 'yan Japan ko kuma yana da saukin kai. Keken da kamfanin Italiya ya ba shi ba yanzu za a sayar da shi ba. To amma sauran kyaututtukan guda biyu za su sahun sauran kayayyaki fiye da dubu dari da suke dauke da hotunan Kumamon wadanda kuma suka hada da motoci da jirage zuwa litattafai. Kamfani jirage na Japan ya sa hoton Kumamon a jikin jirgin samfirin 737. A lokacin da kamfanin Steiff mai kera kayan wasan yara ya fito da kayan wasan yaran masu dauke da hoton Kumamo guda 1,500 na musamman a kan Dala 300 kowanne, mutane sun saye su a cikin dakika biyar ta intanet, in kamfanin kayan wasan yara na Jamus.

Image caption Jirgi mai dauke da hotunan Kumamato

A bara ma kamfanin Leica ya yi wasu kamarori na daukar hoto masu dauke da Kumamon, a kan kudi Dala 3,300, farashin da ya yi dai-dai da na mutum-mutumin da kamfanin kera gwal na Tokyo ya yi na Kumamon da danyen gwal wanda aka saya Dala miliyan daya.

Har yanzu dai tambayar ita ce wane ne shi wannan Kumamon? Kumamon dai yana da saukin kai wajen mu'amala kuma wanda ke daya daga cikin abubuwan da al'ummar Japan suke matukar son gani saboda kasancewarsa na kowa, kama daga birane da kauyuka da gidaje har ma zuwa mutanen da ke gidan kaso. A wasu lokutan, ana fassara Kalmar Komamon a matsayin wani abu da kowa yake alakanta kansa da shi.

Image caption Kumamato yana da farin jini a tsakanin mutane.

Kumamato ya zama wata alama ta yankin Kumamato wanda ya kai girman jiha a Amurka. Yankin na amfani Kumamo wajen jawo hankalin masu yawon bude ido da kuma fitar da kayan amfani gona ga kasashen waje. A na matukar girmama Kumamo domin ana daukarsa a matsayin wani ubangiji da za ka iya samu a gidajen yankin Kumamato. Kumamo yana da tarin gemu. Labarinsa dai ya zamo kamar na gizo da koki da ake samu a irin tatsuniyoyin yara kanana. A wannan zamanin za mu iya cewa Kumamo dai-dai yake da 'yar tsana mai gashi.

Ba tim ba ce ita kadai ta nuna damuwarta akan halin Kumamo yake cikin lokacin girgizar kasar da aka yi a Japan, a watan Afrilu, saboda a lokacin aka tsaya da sanya bayanai a shafin Twitter na Kumamo wanda yake da mabiya 494,000, wanda kuma kafin nan ana zuba bayanai akalla sau uku a kowacce rana.

Image caption Hoton Kumamato akan gurji a wani shagon sayar da kayan marmari.

"Hakan ne ya janyo mutane suke ta faman tambayar me ya faru aka daina sanya bayanai a shafin Twitter na Kumamo, a dai-dai lokacin da ake bukatar bayanan nasa fiye da koyaushe," kamar dai yadda jaridar Japan Times ta wallafa a shafinta na Facebook, a ranar 19 ga Afrilu.

Kafin ka ce kwabo sai mutane, kama daga yara zuwa kwararru, suka fara aike da hotunan Kumamon ta shafukan sada zumunta. Tun suna dari sai suka koma dubbai. Ai ta aiko da hotunan daga kasashe daban-daban da suka hada da Thailand da Hong Kong da kuma China. Hakan ya sanya an zaburar da mutanen kan bukatar da ake da ita na taimakawa da kayan agaji domin tallafawa mutanen da girgizar kasar ta rutsa da su. Sakonnin dai suna dauke da hoton Kumamon, a inda kansa yake daure da tsimman bandeji, yana mai debo duwarwasun da za a aza damba na sake gina wani katafaren gida mai dadadden tarihi da ke Kumamato wanda ya ruguje sakamakon girgizar kasar.

Image caption Hotunan kananan abubuwa da mutane suke so musamman idan suna zaman kadaici.

Tarihi dai ya nuna cewa zamani daban-daban da suka shude, mutane suna da ubangiji a kowane gida, ba wai ana nufin ubangijin kowa da kowa ba a duniya, abin da ake nufi shi ne wani dan karamin abin kamun kafa kuma wani lokacin ma su kan debe kewa. ba kowa ne yake da abokai ko kuma jaririn da zai debe masa kewa ba. A mafi yawancin lokuta, mutane maza da mata suna zama a cikin halin kadaita.

Image caption Masana sun ce 'yar tsana tana debewa mutane kewa.

Ana dai yin 'yar tsana mai gashi saboda debe kewa musamman a lokacin da dare ya tsala ko ya yi duhu ko kuma idan iyayenka suka tafi suka kwanta cikin dare. Ana samun nutsuwa a kananan abubuwa kamar 'yar tsana. Kananan abubuwa irin su 'yar tsana na sanyawa mutum kwanciyar hankali, kamar yadda masanin ilimin dan adam, farfesaChristine R Yano na jami'ar Hawaii, ya rubuta. Idan kana son karanta na wannan labarin na turanci to za ka iya latsa wannan Meet Japan's Kumamon, the bear who earns billions.