Tsohon dan wasan Arsenal Flamini ya koma Palace

Dan wasa Kwallon Kafa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Tsohon dan wasan Arsenal Mathieu Flamini

Crystal Palace ta dauki tsohon dan wasan Arsenal, Mathieu Flamini, kan yarjejeniyar zai buga mata tamaula zuwa karshen kakar bana.

Flamini mai shekara 32, ya bar Arsenal a karshen kakar badi, bayan da ya yi mata wasanni 246 tsawon shekara biyu, ya kuma ci kofin kalubale uku a kungiyar.

Dan wasan ya kuma lashe kofin Serie A a shekarar 2011 a lokacin da ya buga wa AC Milan tamaula shekara biyar, kuma shi ne na biyar da Palace ta dauka a bana.

Palace din ta dauki Andros Townsend da Steve Mandanda da James Tomkins da Christian Benteke da kuma Loic Remy wanda zai yi mata wasanni aro.