Ronaldo zai buga wasan da za su yi Osasuna

Ya samu rauni a kafa bayan karo da Dmitri Fayet
Bayanan hoto,

Christiano Ronaldo ya warke

Dan wasan Real Madrid, Christiano Ronaldo zai taka ledar farko tun bayan raunin da ya samu a gwiwarsa, a wasan karshe na gasar Euro 2016.

Ya dai samu raunin ne sakamakon taho-mu-gama da ya yi da dan wasan Faransa, Dimitri Payet, a lokacin wasan da Portugal ta ci Fransa 1-0.

Dan wasan na gaba, mai shekara 31, bai buga wa kulob dinsa wasanni ukun farko na wannan kakar wasannin ba.

A ranar Asabar ne Real Madrid za ta kara da Osasuna a cigaba da wasannin gasar La Liga, kuma Ronaldo zai taka wasan.

Kocin Real Madrid, Zinedine Zidane ya ce "muna murna da dawowar sa".