Manchester City ta ci Manchester United a gida

Guardiola dai yana samun nasara a wannan kakar wasannin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jose Mourinho da Guardiola suna tafawa kan nasarar Man City

Manchester City ta samu nasara a kan Manchester United da ci 2-1, a wasan da suka buga ranar Asabar, a Old Trafford.

Dan wasan Man City, Kevin de Bruyne ne ya fara jefa kwallon farko a ragar Man United.

Kelechi Iheanacho ne kuma ya sanya kwallo ta biyu, a inda shi kuma Zlatan Ibrahimovic ya ci wa Man United kwallo daya.

Yanzu dai Manchester City tana da maki 12 kuma ita ce a saman teburin gasar Premier, bayan da ta samu nasara a wasanninta dari bisa dari.