Kyaftin din Chelsea John Terry zai yi hutun kwana 10

Asalin hoton, AP/Kirsty Wigglesworth
Ranar Lahadi John Terry ya yi rauni yayin wasan da Chelsea ta buga da Swansea
Kyaftin din Chelsea, John Terry, zai yi hutun buga wasa na kusan kwana 10 bayan da ya yi rauni a kafarsa yayin wasan da suka buga da Swansea ranar Lahadi.
Hakan na nufin dan wasan mai shekara 35 da haihuwa ba zai buga wasan Premier League da Chelsea za ta kara da Liverpool ba ranar Juma'a da ma wasan Cin Kofin League wanda za ta kara da Leicester ranar 20 ga watan Satumba.
Mai yiwuwa daya daga cikin sababbin 'yan wasan kungiyar, David Luiz ko Marcos Alonso, ya hau matsayinsa.