Ba za mu lashe Kofin Zakarun Turai ba - Ranieri

Gasa zakaru Turai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Leicester City za ta fara yin wasan farko a gasar cin kofin zakarun Tura ta bana

Kociyan Leicester City, Claudio Ranieri, ya ce da kyar ne idan za su iya lashe Kofin Zakarun Turai na bana.

Ranieri ya kara da cewar abu ne mai wuya domin akwai manyan kungiyoyi da suke cikin gasar; sannan ya ce daukar kofin a wurinsu kamar sake rubuta labarin almara ne.

Leicester, wadda ta lashe kofin Premier na bara a karon farko, za ta buga Gasar Zakarun Turai a ranar Laraba da Club Brugge.

Sai dai kuma kyaftin din Leicester City, Wes Morgan, ya ce za su iya daukar kofin, ya kuma ja kunnen kungiyoyi da kada su raina su.

Leicester tana rukuni na bakwai da ya kunshi Copenhagen da Porto da kuma Club Brugge.