Rooney ba zai buga wa United wasan Europa ba

Atisaye Wasa Gasa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Rooney a lokacin da yake yin atisaye

Wayne Rooney baya cikin 'yan wasa 20 da za su buga wa Manchester United gasar cin kofin zakarun Turai ta Europa da za ta kara da Rotterdam a ranar Alhamis.

Rooney mai shekara 30, wanda ya yi atisaye a kungiyar a ranar Laraba ba zai buga wasan farko da kungiyar za ta yi ba, haka ma Luke Shaw da Antonio Valencia da kuma Jesse Lingard.

Henrikh Mkhitaryan da Phil Jones wadan da ba su buga atisayen ba, su ma ba za su wakilci United a gasar ta Europa ba a ranar Alhamis.

Kociyan Manchester United, Jose Mourinho, ya ce zai fara wasan da Marcus Rashford a karon farko a fafatawar da za su yi a rukunin farko.

Michael Carrick da Matteo Darmian da Timothy Fosu-Mensah da Marcos Rojo da kuma Memphis Depay za su buga wa United karawar, duk da cewar ba su buga fafatawar da Manchester City ta ci United a gasar Premier a ranar Asabar.