Kone zai ci gaba da wasa a Sunderland

Asalin hoton, Getty Images
A watan Janairu ne Sunderland ta dauki Kone daga kungiyar Lorient mai buga gasar Ligue 1 ta Faransa.
Mai tsaron baya na Sunderland, Lamine Kone, ya sabunta yarjejeniyar ci gaba da taka-leda a kungiyar zuwa shekara biyar.
Dan kwallon tawagar Ivory Coast, mai shekara 27, ya nemi izinin barin kungiyar a cikin watan Agusta a lokacin Everton na zawarcinsa.
A watan Janairu ne Sunderland ta dauki Kone daga kungiyar Lorient mai buga gasar Ligue 1 ta Faransa.
Sunderland za ta ziyarci Tottenham a gasar Premier wasan mako na biyar a ranar Lahadi.