An hukunta LeRoy saboda cogen 'yan kwallo

Tarko Kotu Cinikayya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

LeRoy ya ce kotun ta fahimci cewar an dana mashi tarko ne ya kuma kama shi.

An ci tarar kociyan Togo, Claude LeRoy, bayan da wata kotu ta same shi da laifin yin coge a cinikayyar 'yan kwallo lokacin da yake Racing Club de Strasbourg.

Babbar kotun Strasbourg ta ce LeRoy, wanda ya horar da Racing Club de Strasbourg daga shekarar 1998 zuwa 2008, zai biya tarar fam 12,790.

Kotun ta ce ta samu kociyan da laifin yin takardun jabu da kuma amfani da mukamai na karya har sau hudu a lokacin da ya yi cinikin 'yan wasan tamaula.

Kotun ta yanke hukuncin ne kan sayar da Jose Luis Chilavert, da Peguy Luyindula, da Henri Camara, da kuma Per Pedersen.

Bayan da aka yanke masa hukuncin LeRoy ya ce kotun ta fahimci cewar an dana mashi tarko ne ya kuma kama shi.