Leicester City ta doke Club Brugge

Asalin hoton, Getty Images
Leicester ta fara gasar zakarun Turai da kafar dama
A wasan farko da Leicester ta fara buga gasar cin kofin zakarun Turai, ta doke Club Brugge da ci 3-0 a karawar da suka yi a ranar Laraba a Belgium.
Marc Albrighton ne ya fara cin kwallon farko, sai kuma Riyad Mahrez da ya ci guda biyu a karawar., daya a bugun tazara, dayar kuwa a bugun fenariti.
Lesta wadda ta lashe kofin Premier da aka kammala a karon farko a tarihin kungiyar sama da shekara dari, tana rukuni na bakwai da ya kunshi Copenhagen da Porto da kuma Club Brugge.
Leicester za ta karbi bakuncin FC Porto a wasa na biyu na cikin rukuni a gasar ta cin kofin zakarun Turai ranar 27 ga watan Satumba.