Murray zai kara da Del Potro a Davis Cup

Kwallo Tennis Kofi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Birtaniya ce ke rike da Davis Cup

Andy Murray zai kara da Juan Martin del Potro a gasar kwallon tennis ta Davis Cup a karawar da Birtaniya za ta yi da Argentina ranar Juma'a.

Birtaniya, mai rike da kambun na Davis Cup, za ta fafata da Argentina a wasan daf da na karshe a Glasgow.

Bayan wasan Murray da Del Potro sai karawa tsakanin Kyle Edmund na Birtaniya da Guido Pelle na Argentina.

Haka kuma Andy da Jamie za su kece raini da Federico Delbonis da kuma Leonardo Mayer a gumurzun 'yan wasa bibbiyu.