Nigeria ce ta 14 a iya kwallo a Afirka

Asalin hoton, Getty Images
Nigeria ce ta 67 a jadawalin da Fifa ta fitar a watan Agusta
Tawagar kwallon kafa ta Najeriya ta matsa sama zuwa mataki na 14 a jerin kasashen da suke kan gaba a iya taka-leda a Afirka.
A jerin kasashen da suka fi iya kwallo a duniya da Fifa ta fitar a ranar 15 ga watan Satumba, Najeriya ce ta 64 a duniya a fagen tamaula.
A jadawalin da hukumar kwallon kafa ta duniya ta fitar a watan Agusta, Najeriya ce ta 67 a iya tamaula a duniya, kuma ta 16 a Afirka.
Kasashen da suke saman Najeriya a Afirka sun hada da Côte d'Ivoire da Algeria da Senegal da Tunisia da Ghana da Jamhuriyar Congo da Masar da Congo da Mali da Morocco da Kamaru da Guinea da Afirka ta Kudu.
Argentina ce ke kan gaba a iya kwallo a duniya, sai Belgium a mataki na biyu da Jamus a matsayi na uku.
Tawagar Super Eagles, wadda ba za ta buga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a 2017 ba, tana matsayi na 64 a iya murza-leda a duniya.