Feyenoord za ta kara da Man United

Wasa Gasa Lokaci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan wasan Manchester United a lokacin atisaye

Manchester United za ta ziyarci Netherlands, domin karawa da Feyenoord a gasar cin kofin zakarun Turai ta Europa a ranar Alhamis.

Sai dai kuma Wayne Rooney baya cikin 'yan wasa 20 da za su buga wa Manchester United karawar da za su yi a Rotterdam.

Rooney mai shekara 30, wanda ya yi atisaye a kungiyar a ranar Laraba ba zai buga wasan farko da kungiyar za ta yi ba, haka ma Luke Shaw da Antonio Valencia da kuma Jesse Lingard.

Henrikh Mkhitaryan da Phil Jones wadan da ba su buga atisayen ba, su ma ba za su wakilci United a gasar ta Europa ba a ranar Alhamis.

United tana rukunin farko da ya kunshi Fenerbahce da Zorya Lugansk da kuma Feyenoord Rotterdam.

Ga wasu wasannin da za a buga a ranar Alhamis:

 • FC Viktoria Plzen vs AS Roma
 • Zorya Lugansk vs Fenerbahce
 • Apoel Nicosia vs FC Astana
 • BSC Young Boys vs Olympiacos
 • FSV Mainz 05 vs Saint Etienne
 • RSC Anderlecht vs FK Gabala
 • AZ Alkmaar vs Dundalk FC
 • Sassuolo vs Athletic de Bilbao
 • Panathinaikos vs Ajax Amsterdam
 • Standard de Liege vs Celta de Vigo
 • Nice vs Schalke 04
 • PAOK vs ACF Fiorentina
 • Internazionale vs Hapoel Beer Sheva
 • Southampton vs Sparta Prague
 • Villarreal CF vs FC Zurich
 • Sporting Braga vs KAA Gent