Attajiran China sun sayi kulod din West Brom

Karkashi Gasa Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Karkashin Peace Albion ta yi shekara 11 a gasar Premier

Kulob din West Bromwich Albion mai buga gasar Premier ta Ingila, ya sanar da cewa attajiran China sun kammala sayensa.

Tsohon shugaban kulob din Jeremy Peace ne ya amince da cinikin karkashin jagorancin Guochuan Lai.

Tun a cikin watan Yuni suka cimma matsaya a tsakaninsu, amma suka tsaya jiran amincewar sashin kula da huldar kudade na hukumar Premier.

Albion shi ne kulob na uku da rukunan attajiran China suka saya daga yankin yammacin Ingila da suka hada da Aston Villa da Wolves.