Nathan Dyer zai yi jinyar wata biyu

Kaka Wasa Kammala

Asalin hoton, Huw Evans picture agency

Bayanan hoto,

Nathan Dyer ya buga wa Leicester City wasanni aro a kakar da aka kammala da shi kuma aka ci kofin Premier

Dan wasan Swansea City, Nathan Dyer, zai yi jinya zuwa wata biyu.

Dan kwallon ya ce ya ji takaicin raunin da ya yi, wanda ya dunga jin radadi tun bayan da suka dawo daga atisaye a Amurka.

Dyer mai shekara 28, ya ci kofin Premier a bara a Leicester a lokacin da ya yi mata wasanni aro.

Dan wasan ya kulla yarjejeniyar ci gaba da buga tamaula a Swansea City zuwa shekara hudu a watan Agusta.